Idan Ka Saki Matarka, Ban Yafe Maka Ba

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum. Idan uba ya ce wa Ɗan shi kar ya sake matar sa, in ya sake ta bai yafe ba. Toh idan yaron ya sake ta yana da laifi ne a wurin Allah? Yaron auren dole aka masa da matar, kuma matar ta ki zama a gidan. ba su ma taɓa haɗa shinfida ba, gashi baban shi ya gargaɗe shi kar ya sake ta ?.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam, matukar Manufofin zamantakewar ba za su tabbata ba in su ka cigaba da zama tare ya halatta ya sake ta,  saboda cigaba da rike ta saɓon Allah ne, biyayya ga Allah tana gaba da biyayya ga Iyaye.

    Allah yana cewa a suratul Bakara aya ta 229

    اَلطَّلَاقُ مَرَّتٰنِۖفَاِمْسَاكٌ بِۢمَعْرُوْفٍ اَوْ تَسْرِيْحٌ بِۢاِحْسَانٍۗوَ

     "Saki karo biyu ne,  bayan haka kuma sai a rike ta da kyautatawa ko kuma a rabu cikin lalama"

    A aya ta (230) Allah ya halattawa mace ta fanshi kanta in ta ga ba za ta iya tsayawa da hakkokin aure ba, Idan suka rabu Allah zai azurta kowa daga falalarsa kamar yadda ya zo a Suratun Nisa'i .

    Daga cikin Manufofin aure akwai samun Zuriyya da nutsuwa da kuma debe-kewa, rintse ido daga kallon Haram, mutukar Manufofin suka goce saki yana halatta.

    Ba duk mummunar addu'ar iyaye Allah yake amsawa ba, in da Allah yana amsa duka munanan addu'o'in mutane da sun mutu Miris, kamar yadda Allah ya yi bayani a Suratu Yunus aya ta (11)

    وَلَوْ يُعَجِّلُ اللّٰهُ لِلنَّاسِ الشَّرَّ اسْتِعْجَالَهُمْ بِالْخَيْرِ لَـقُضِىَ اِلَيْهِمْ اَجَلُهُمْۗفَنَذَرُ الَّذِيْنَ لَا يَرْجُوْنَ لِقَاۤءَنَا فِىْ طُغْيَانِهِمْ يَعْمَهُوْنَ

    Kuma dã Allah Yana gaggãwa ga mutãne da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da alhri, haƙĩƙa dã an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Sabõda haka Munã barin waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu sunã ta ɗimuwa.

    Allah ne mafi sani

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.