Idan Saduwa Tana Cutarwa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Idan saduwa da miji yana haifar da cutarwa ga mace za a iya cewa: Allaah yana fushi da ita idan ba ta amsa wa mijin ga buƙatarsa ba?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

    Kodayake dokokin musulunci sun ɗora wa mace ta amsa wa mijinta a duk lokacin da ya buƙace ta. Kuma har akwai munanan alƙawura na azaba gare ta idan ta taurare ba ta je ga biyan buƙatar mijin ba. Amma addinin yana lura da halin ƙunci ko rashin natsuwa ko tsananin gajiya da rashin shaawar buƙatar ma.

    Shi kansa miji bai zama mutumin kirki na-gari ba idan dai ya nace ga neman ta biya masa buƙatarsa a lokacin rashin lafiyarta ko tsananin yunwa ko baƙin ciki kamar saboda rasuwar wani daga cikin iyaye ko wani ɗa ko dan ’yan uwa da makamancin haka.

    Amma kuma idan mace tana cikin matsalar rashin iya biya wa miji buƙata, to sai ta sanar da shi wannan halin da take cikin kuma ta ba shi hakuri, ta rarrashe shi. Sannan kuma ta kwantar masa da hankali irin yadda take yi masa a lokacin haila ko biki. Idan har ta samu ya yarda ya amince shikenan. Da ma abin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fada a cikin hadisin shi ne

    وَالَّذِى نَفْسِى بِيَدِهِ! مَا مِنْ رَجُلٍ يَدْعُو امْرَأَتَهُ إِلَى فِرَاشِهَا فَتَأْبَى عَلَيْهِ ، إِلاَّ كَانَ الَّذِى فِى السَّمَاءِ سَاخِطًا عَلَيْهَا ، حَتَّى يَرْضَى عَنْهَا  «

    Na rantse da Wanda raina ke hannunsa! Babu wani namijin da zai kira matarsa don saduwa da ita, sannan kuma ta ƙi yarda gare shi, face Wanda ke sama ya kasance mai fushi da ita, har sai lokacin da ya yarda da ita. (Sahih Muslim: 3613).

    Wannan ita ce mafita mai janyo alheri. Amma ba ta fuskance shi da izza da tsiwa da sauran munanan abubuwa irin waɗannan ba.

    Allaah ya ƙara mana fahimta da ƙarin kafewa a kan bin dokokin addininmu.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.