𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam
Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya ce wa matarsa: ‘In kin samu miji ki yi
aure!’ ta saku? Kuma sun yi wata shida yanzu ba su a tare da juna, ko za ta iya
yin auren?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Malamai sun kasa
Lafazin Saki gida biyu ne: Akwai Saki Sarihi wanda ba a iya fahimtar komai daga
cikinsa sai dai sakin kawai, kamar idan mijin ya ce wa matarsa: Na sake ki!
Akwai kuma
Saki na Kinaya, wanda ke iya ɗaukar
ma’anar saki, kuma a lokaci guda ya ɗauki
wata ma’anar da ba sakin ba. Kamar miji ya ce wa matarsa: Tafi gidanku!
Ma’anarsa za
ta iya zama saki ne yake nufi, ko kuma ya zama manufarsa: Tafi gidanku sai
al’amura sun gyaru. Ko: Tafi gidanku kafin in dawo daga tafiya. Ko kuma: Tafi
gidanku a koya miki abinci ko ladabi da biyayya. Da sauransu.
Kamar haka,
wannan kalmar: In kin samu miji ki yi aure, a fahimtata ta fi kama da nau’in
saki na kinaya. Domin ma’anarta kan iya kasancewa: ‘In kin samu miji ki yi
aure, in gani!’ Domin ƙarancin maza masu son yin auren da ake da su! Ko kuma: ‘In kin samu miji ki yi
aure, in kin isa!’
Watau saboda tsananin soyayyar da ya san tana yi masa!
Don haka,
kafin a yanke hukunci a kan irin wannan sakin na kinaya sai dole an ji daga
bakin mijin: Shin sakin yake nufi, ko kuwa wani abin daban yake nufi?!
Matar da aka ɗaura mata sahihin aure ba
za ta sake yin aure da wani mijin ba sai a bayan aurenta na farko ya mutu: Ko
dai ta hanyar mutuwan mijin ko mutuwar auren. Kuma ko a bayan mutuwar auren ba
za ta iya sake yin wani auren ba, sai a bayan ta gama idda. Ita kuma Idda tana
bambanta da gwargwadon matsayin macen da
aurenta ya mutu
1. Idan ya
kasance saboda mutuwar mijinta ne, to iddarta watanni huɗu ne da kwanaki goma.
2. Idan kuma
saboda saki ne, to iddarta tsawon haila uku ne, idan matar tana daga cikin waɗanda suke cikin shekarun
yin hailar ce.
3. Idan kuwa
ba ta daga cikin masu yin hailar saboda tsufa ko yaranta, to tsawon iddarta
watanni uku ne.
4. Idan kuwa
matar mai ciki ce a lokacin da aka sake ta, to iddarta shi ne ta haife cikinta.
Don haka, waɗannan matar ba za ta iya
yin aure ba, har sai an tabbatar da cewa mijin sakinta ya yi. Sannan kuma ko a
bayan hakan sai kuma bayan ta gama yin idda.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.