𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Mene ne hukuncin korar yaro daga
masallaci, ko daga sahun farko don babba ya maye gurbinsa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan yaro ba ya cutar da kowa –
da aikinsa ko maganarsa to bai halarta a fitar da shi daga masallaci, ko a dawo
da shi sahun da yake baya da wanda yake tsaye a cikinsa ba, koda kuwa a bayan
liman yake kai tsaye; saboda a sunna wanda ya fara zuwa wuri shi ya fi cancanta
da shi, kuma Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya hana mutum ya tashi dan'wansa
daga wurinsa shi don ya zauna a wurin, masallatai kuma gidajen Allah ne, bayin
Allah (baba da yaro) daya suke a cikinsu.
Hadisin da Annabi Sallallahu
alaihi Wasallam yake cewa “Masu hankalin cikinku ya zama su suke biye da ni a
sahu” kuwa ba ya nuna a rika korar yara daga sahun farko koda daga su sai liman
kamar yadda wasu malamai suka ɗauka.
Wannan hadisi yana kwadaitar da manyan ne kan su je masallaci da wuri don su
samu tsayawa a bayan liman. Sannan korar su daga sahun da suke zuwa na baya zai
haifar da matsaloli kamar: Taruwarsu a wuri guda wanda wannan zai sa su yi ta
wasa da hayaniya lokacin sallah Za su rika kin Masallaci Za su rika kin
masallata, musamman mai korar su.
WALLAHU A'ALAM
Shiekh Ibn Uthaimin
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.