1. Kwanaki na mana gwalo,
Wasu na shagali da murna.
2. Ga ƙasa na ambatonmu,
Mun shagalta da cin amana.
3. Ga shi ba ta ma sanarwa,
4. Kuma ba ta ƙara loto,
In ta zo balle mu zauna.
5. Kwanaki na yaudararmu,
Ga shi babu zaman lumana.
6. Duniyar duka babu tabbas,
Ko da me ja kan batuna?
7. Sai ka wayi gari cikinmu,
Yamma ba kai in ka auna.
8. Wasu sai ko a tashi ba su,
Haihuwarsu ta zo da ƙuna.
9. Daga nan sun ɗauki layi,
Kwanakinsu a nan ya zana.
10. Tun ana ɗan baka mama,
Har ka girma ka je Madina.
11. Sai batun aure ya taso,
Sai ka auri ɗiyar Amina.
12. Shekara kafin ta dawo,
Haihuwa ce har da suna.
13. Daga nan ka zam ma Baba,
Sai iyalai duk su baina.
14. Sai ko tsufa ta rufe ka,
Daga nan mutuwa ka auna.
15. Kwanaki sun baka dama,
Sai abin da kayo a duna.
16. Wanda yai khari a duniya,
Zai tarar har yai yi murna.
17. Wanda yai akasi na khari,
Za ya girbi duhu da ƙuna.
18. Ihiwani ƙwarai mu farka,
Kan ta zo mana 'yan uwana.
19. Rabbi ba mu sa'a gaba ɗai,
Duk mu ɗunguma can a aljanna.
20. Ɗanbala yai yo kasidar,
Daga Borno gidan lumana.
©
Mohammed Bala Garba
23/7/2022.
5:55 pm.
Sabuntawa
10/11/2023.
8:27am
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.