𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul
Laah. Shin ya halatta yaron da bai balaga ba ya yi limancin sallah. Wata ce ɗanta mai shekaru biyar
yake jan ta sallah da yar'uwarsa. Ko hakan ya yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah Wa Barakaatuh.
Malamai suna da mabambantan ra’ayoyi a kan wannan
mas’alar: A lokacin da wasu ke ganin ba zai yiwu yaron da bai balaga ba ya yi
limancin sallah, wasu suna ganin ya halatta ya yi. Matuƙar dai yaron ya waye,
kuma ya san abin da ake nufi da sallar, kuma ya iya kawo ta daidai gwargwado,
tare da rukunnanta da sharuɗɗanta
har zuwa sallama, shikenan.
Dalilinsu kuwa shi ne hadisin da
Al-Bukhaariy (4302) ya riwaito cewa Sahabi Amru Bn Salamah (Radiyal Laahu Anhu)
ya zama limamin mutanen ƙauyensu saboda shi ne ya fi su karatun Alqur’ani, a lokacin yana ɗan shekaru shida zuwa
bakwai. Kuma ba a ji Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya
yi musun hakan ba.
Faɗin
cewa: Ai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai san sun yi
hakan ba, don ba a tare da shi su ke ba a lokacin, malaman sun bayar da martani
ga hakan da cewa: Ko da a ƙaddara cewa Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) bai san hakan ba, ai kowa ya san Ubangijinsa (Subhaanahu Wa
Ta’aala) ya san da
aukuwar hakan. In da kuwa ba daidai suka aikata ba, ai da ya saukar da wahayi
domin faɗakar da shi
hakan, irin yadda ya faɗakar
da shi a lokacin da ya fara yin sallah da takalmin da ke ɗauke da najasa. Kuma da
ma Allaah Ta’aala ya ce:
وَإِن تَسۡـَٔلُوا۟
عَنۡهَا حِینَ یُنَزَّلُ ٱلۡقُرۡءَانُ تُبۡدَ لَكُمۡ
Kuma idan kuka yi tambaya a kan
al’amari a lokacin da ake saukar da Alqur’ani sai a yi muku bayani. (Surah
Al-Maa’idah: 101).
Amma game da wannan mas’alar, me
ya sa ita mahaifiyar yaran ba za ta shugabance su ba kawai, a wuce wurin? Ko
yaron ya fi ta sanin Alqur’ani ne? Meye laifi idan ita ta yi musu limanci? Ba
ga Sahabiya Ummu-Waraqah (Radiyal Laahu Anhaa) ta kasance tana yi wa mutanen
gidanta limanci ba?! (Sahih Abi-Daawud: 553).
Daga baya idan yaron ya ƙara
girma, kamar idan ya kai shekaru shida zuwa bakwai sai ta fara sakam masa
ragamar limancin, kamar yadda hadisin Amr Bn Salamah ya nuna. Tare da cewa, in
dai ba da wata larura ba, kamata ya yi a lokacin ya riƙa tafiya masallaci ne
tare da mahaifinsa yana yin sallolinsa na farilla a bayan liman.
Allaah ya datar da mu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Cnf26Q8MPqz9yUYU1nxqRq
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.