Ticker

    Loading......

Limancin Mai Naƙasa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

 As-Salaamu Alaikum. Maigida ne yake da naƙasar da take hana shi yin sallah a tsaye, to yaya limancinsa ga iyalinsa da waɗanda ba su kai shi ƙwarewa ko zurfi a cikin karatun Alqurani ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Malamai sun sha bamban a kan limancin mara lafiya ko mai wata naƙasa a jikinsa ga masu lafiya, waɗanda ba su da irin wannan naƙasar.

Waɗansu sun ce makaruhi ne, waɗansu kuma sun ce ya halatta.

As-Shaikh Al-Mujaddid Al-Albaaniy (Rahimahul Laah) ya ce

Babu yadda za a ce yin hakan makaruhi ne, balle ma har a ce wai sallar ba ta inganta ba saboda hakan, matuƙar dai sharuɗɗan Limancin da aka shimfiɗa sun cika a kansa. Ba mu ganin wani bambanci a tsakanin limancinsa da limancin makaho wanda ba ya iya tsare kansa daga najasa irin yadda mai gani yake iya tsarewa. Haka kuma mai sallah a zaune wanda ya kasa miƙewa tsaye. Domin dai kowannensu ya aikata irin abin da yake iyawa ne da gwargwadon ikonsa kawai, kuma da ma:

لَا یُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ

Allaah ba ya ɗora wa wani rai komai face dai iyawarsa.

 Surah Al-Baqarah: 286 .

Daga cikin sharuɗɗan da malamin yake nufi a nan akwai abin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ambata a cikin hadisin Muslim: 673 , cewa:

يؤمُّ القومَ أقرؤُهمْ لِكتابِ اللَّهِ وَإن كانوا فrي القراءةِ سواءً فأعلمُهمْ بالسُّنَّةِ فإن كانوا في السُّنَّةِ سواءً فأقدمُهمْ هجرَةٍ فإن كانوا في الهجرة سواءً فأكبرُهم سِنًّا ولا يُؤَمُّ الرجلُّ في سلطانِهِ ولا يُجلَسُ على تَكرِمَتِهِ إلا بإِذنِه

Wanda zai yi wa mutane limanci shi ne wanda ya fi su karatun littafin Allaah. Idan kuma sun zama daidai a karatun sai wanda ya fi su sanin Sunnah. Idan kuma sun yi daidai a Sunnah sai wanda ya riga su yin hijira. Idan kuma sun zama daidai a hijira to sai wanda ya fi su girma a shekaru. Kuma ba a yi wa wani mutum limanci a cikin gidansa, ko a cikin mulkinsa, kuma ba a zama a kan karagarsa sai da izininsa.

A wata riwaya kuma ya ce

مَكانَ سِلْمًا سِنًّا

Wanda ya fi su a shekaru, maimakon: Wanda ya riga su musulunta.

Sannan kuma ƙaidar da malamai suka shimfiɗa a wurin limanci ita ce: Duk wanda sallarsa ta inganta ga kansa in yana shi kaɗai, to limancinsa ta inganta ga waninsa .

Idan limamin ya yi sallarsa a zaune, a nan ma malamai sun sake shan bamban game da mamu masu yin sallah a bayansa. Shin ko su ma a zaunen za su yi ko kuwa a tsaye tun da ba su da uzuri ko larura irin ta sa?

Sahihiyar maganar da muka fi natsuwa da ita ita ce

Idan tun farko limamin ya fara sallar a zaune ne, to wajibi ne masu sallah a bayansa su ma su yi sallar a zaune tun daga farko har ƙarshe, saboda umurnin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da ya ce

ائتمُّوا بأئمَّتِكُم فإن صلَّوا قيامًا، فصلُّوا قيامًا، وإن صلَّوا جلوسًا فصلُّوا جلوسًا

Ku yi koyi da limamanku: Idan ya yi sallah a tsaye to ku yi sallar a tsaye ku ma; idan kuma ya yi sallah a zaune sai ku ma ku yi sallar a zaune. (Muslim: 417)

Amma idan ya fara sallar a tsaye ne sai kuma daga baya wata larura ta sanya shi ya zauna, to a nan ba sai mamu sun zauna ba. Suna iya cigaba da sallarsu a bayansa a tsaye.

Domin a lokacin da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fito a cikin rashin lafiyarsa na ajali ya tarar Abubakar yana cikin sallah tare da sahabbai, sai ya zauna a gefensa na hagu a matsayin liman kuma Abubakar ya koma mamu tare da sauran sahabbai. A wannan lokacin shi Abubakar da sauran mutane sun cigaba da yin sallah a tsaye ne a bayan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), wanda yake yin sallah a zaune, kuma bai umurce su da su zauna ba. (Al-Bukhaariy: 198; Muslim: 418).

Sannan kuma malamai sun nuna cewa: Idan limamin ya yi sallarsa da nuni ( imaa’i ko ishara) a wurin ruku’u ko sujada saboda larura, to su mamu sai dai su cika su daidai, ba za su yi nuni irin na limamin ba. (Tamaamul Minnah: 1/340).

Allaah ya ƙara mana fahimta a cikin addininmu.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaahi Assalafiy

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments