Mata Za Su Iya Ziyartar Makabarta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam, ina da tambaya akan ko ya halatta mata su ziyarci makabarta, don suyi addu’a ga magabatansu ??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. Ya halatta mata su ziyarci Makabarta, amma kar su yawaita, saboda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya la’anci mata masu yawan ziyarar Makabarta, kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi !!

Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya wuce wata mace tana kuka a jikin Kabari, sai ya ce mata “Ki ji tsoran Allah, ki yi hakuri” kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (1283), a cikin hadisin Manzon Allah bai hana ta ziyarar Kabari ba, kawai ya yi mata WA’AZI ne akan ruri da koke-koken da take yi, sannan Nana A’isha ta tambayi Annabi Sallallahu alaihi Wasallam game da addu’ar da za ta yi in ta je Makabarta sai ya koya mata, kamar yadda ya zo a Sahihi Muslim a hadisi mai lamba ta (974), hakan sai ya nuna mustahabbancin zuwan mata Makabarta ba tare da yawaitawa ba.

Addu’ar ita ce kamar haka

اَلسَّلامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ المؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وَإِنّا إِنْ شَاءَ اللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، وَيَرْحَمُ اللهُ الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنَّا وَالْمُسْتَأْخِرِينَ أَسْأَلُ اللهَ لَنَا وَلَكُمْ الْعَافِيَةَ.

Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku ma'abota waɗannan gidaje daga muminai da musulmi, kuma mu in Allah ya so masu riskuwa ne da ku. Kuma Allah ya ji kan waɗanda suka gabata daga cikinmu da waɗanda suka yi saura. Ina rokon Allah aminci daga bala'i gare mu da gare ku.

Hadisin da aka rawaito cewa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya la’anci mata masu ziyartar Makabarta bai inganta ba, saboda a cikin sanadinsa akwai Salih Baazaam, shi kuma yana da rauni a wajan malaman Hadisi, kamar yadda Ibnu Abdulbarr ya ambata a Tamheed 3/234.

Don haka ya halatta mata su ziyarci Makabarta, saidai su kiyayi yawaitawa, saboda hadisin Farko da na ambata, da kuma ruri da koke-koke, saboda hadisin Bukhari da ya gabata

Don neman karin bayani duba: Almuhallaa 3/388 da kuma Almajmu’u 5/310.

SHIN YA HALATTA MATA SU ZIYARCI MAKABARTA

TAMBAYA (190)

Assalamu alaikum malan ina muku Fatan alkhari Allah yasaka muku dagidan aljannatul firdau Malnan ina da tambaya Akan ziyararar mamaci a maqa'barta mace zata Iya zuwa

Idan kaje malan kamai addu'a yasan kaje kuma yana jinka Shi mamaci

AMSA

Waalaikumus Salam Warahmatullahi Wabarakatuhu

Ziyartar Maqabarta ga Maza koyine da Sunnah saboda hakan zai sa ka tuna da gidan ka na Gaskiya (Kabari)

Annabi (Sallallahu alaihi wasallam) yace (ma'ana): Da na haneku da Ziyartar Maqabarta Amman yanzu na umarce ku da kun dinga Ziyartar domin kuwa hakan zai sa Ku tuna Mutuwa)

Muslim ne ya rawaito hadisin da waninsa

A riwayar Hakim kuma:

"Yin hakan zai sanyaya zuciyarku, zai sa Ku zubda hawaye, Kuma zai sa Ku tuna Lahira saidai Ku kula kada ku fadi abinda yake na haramun yayinda Kuka ziyarci mamatan

(Sahih al-Jaami' 4584)

Gameda Mata su ziyarci maqabarta Kuma wannan kam Makaruhi ne bisa jumhoor ul-'ulemaa'

A wata riwayar Kuma Haramun ne Dogaro da hadisin da Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace (ma'ana): "Allaah ya la'anci Matan da suke yawaita Ziyartar Maqabarta"

(Ahmed, Tirmidhi da Ibn Majah)

"Allaah ya la'anci Matan da suke Ziyartar Maqabarta da Kuma wadanda suke ginin masallachi akan Kabari da wadanda suke saka Haske akai"

(Abu Dawud, Tirmidhi, Nasaa'i da al-Hakim)

Dalilan da yasa aka hana Mata Ziyartar Maqabarta shine: saboda sun kasance suna da naqasu Wanda silar zuwan zaisa ta fashe da Kuka a bakin kabarin mamacin musamman ma idan tanada alaqa dashi Wanda Kuma munsan cewar Kukan Mutuwa shabe shabe Haramun ne domin kuwa zai iya taba addininta da Kuma lafiyarta

Dalilin na biyu shine: Maqabarta waje ne kebantacce Wanda zai zamo barazana ga Rayuwar Namiji ballantana Kuma Rayuwar mace domin kuwa ana gudun kada ta fada hannun miyagun mutane lalatattu akan hanyar ta ta zuwa ko a dawowa zata iya haduwa da marasa tarbiyya

Saidai Malamai sunce ba laifi bane idan wani Malami Mai tsoron Allaah ya jagorance su sun tafi tare don yayi musu waazi ya nuna musu nan shine makomar kowannenmu

Dangane da Kuma Addu'ar da ake Yayin shiga Maqabarta

Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyarda Addu'ar Ziyarar Makabarta Kamar haka:

اَلسَّلامُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الدِّيَارِ مِنَ المؤْمِنِينَ وَالْمُسْلِمِينَ، وَإِنّا إِنْ شَاءَ اللهُ بِكُمْ لاَحِقُونَ، وَيَرْحَمُ اللهُ الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنَّا وَالْمُسْتَأْخِرِينَ أَسْأَلُ اللهَ لَنَا وَلَكُمْ الْعَافِيَةَ.

Assalamu 'alaykum ahlad-diyari minal-mu'mineena walmuslimeen, wa-inna in shaal-lahu bikum lahikoon,{wa yarhamu l-lahu-l- mustaqdimina minna wa-l-musta'khrina} nas-alul-laha lana walakumul-'afiyah.

Aminci ya tabbata a gare ku, ya ku ma'abota wadannan gidaje daga muminai da musulmi, kuma mu in Allah ya so masu riskuwa ne da ku. Kuma Allah ya ji kan wadanda suka gabata daga cikinmu da wadanda suka yi saura. Ina rokon Allah aminci daga bala'i gare mu da gare ku

Dangane da Kuma mamaci yaji addu'ar ka wannan banada ilimi akai domin kuwa wannan Gaibhu ne Kuma Allaah Azzawajallah shi kadai ne yasan Gaibhu

Abinda ya tabbata daga Sahihayn shine: mamata suna Jin Sautin takalman mutane yayinda suke komawa gida

Anan zaa bar mutum da halayensa ne

Ya Allaah ka sa mu tabbata wajen aikata ayyuka nagari ka rabamu da Bidi'ah da Shirka

Wallahu taala aalam

Muna muku tallar sabuwar makarantar USMANNOOR ONLINE ACADEMY inda muke karatuttukan: GYARAN SALLAH, SUNNONI 1,000 da Kuma KIMIYYA DA AL'AJABAN QUR'ANI, duk Wanda yake da ra'ayi shiga, yayimin magana ta Private zaa turo masa link din, in Sha Allaah

Subhanakallahumma wabi hamdika ash-hadu anla'ilaha illa anta astaghfiruka wa'atubi ilayk

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments