𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Malam mace ce
da mijinta bayan aukuwar wata matsala a tsakaninsu sai matar ta kwashe kayanta
ta bar gidan mijin, sai bayan watanni tara take son ta dawo. To wai akwai auren,
ko sai an sake ɗaura
Sabon Aure?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laahi Wa Barakaatuh.
Da zaran an ɗaura aure da ƙa’idojinsa da sharuɗɗansa to yana nan a ƙulle,
babu abin da yake warware shi sai in mijin da zaɓin
ransa ya warware shi ta hanyar aukar da saki. Ko kuma da umurnin alƙali
kamar idan ya gano cewa mijin yana cutar da ita, ba ya sauke haƙƙoƙinta
da suke a kansa.
Kuma a bayan ɗaura aure ba ya halatta
mace ta kwashe kayanta haka nan kawai ta bar gidan mijin domin ɓacin rai. Sannan bai
kamata su kansu iyayenta ko waliyyanta su bar ta a gabansu na tsawon lokaci
haka nan ba tare da binciken mijin ba. Allaah Ta’aala ya ce
وَإِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوا حَكَمًا مِنْ أَهْلِهِ وَحَكَمًا مِنْ أَهْلِهَا، إِنْ يُرِيدَا إِصْلَاحًا يُوَفِّقِ اللَّهُ بَيْنَهُمَا، إِنَّ اللَّهَ كَانَ عَلِيمًا خَبِيرًا
Idan kuma kuka ji tsoron aukuwar
saɓani a tsakaninsu
to sai ku aika da mai hukunci a cikin danginsa da mai hukunci a cikin danginta.
Idan dai suna nufin gyara ne to Allaah zai datar a tsakaninsu. Haƙiƙa
Allaah ya kasance masani ne mai ba da labari. (Surah An-Nisaa’: 35).
A ƙarƙashin wannan matar da ta dawo bayan
watanni tara ko fiye ko ƙasa da haka tana nan a matsayin matarsa, tun da dai bai sake
ta ba, kuma ba ta kai ƙara kotu don neman rabuwa da shi, kamar ta hanyar khul’i ko makamantan hakan ba.
Amma a wannan zamanin da gaskiya
da riƙon
amana da tsoron Allaah suka yi ƙaranci a cikin mutane bai kamata su
amince kawai ta shiga ta zauna haka nan ba tare da sake binciken lafiyarsu ba. Haka
kuma lallai kafin ya kusance ta ya tabbatar babu komai a cikin mahaifarta, don
kar a ɗauko zuriyar
wani gida a haɗa da
na gidan wannan mijin.
Allaah ya ƙara mana shiriya.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat. whatsapp. com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.