TAMBAYA (100)❓
Mene ne gaskiya akan cewar Shehu
Ahmad Tijjani ya buga kudin jabu. Muna buqatar amsa amman da hujjoji pls
AMSA❗
Bismillahir Rahmanir Rahim
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah SWT. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga cikamakon Annabawa, Annabi Muhammad SAW
Kowanne musulmi na gaskiya yasan
cewar addinin musulunci addini ne wanda yake komai akan tsari, na koyarwar
Qur'ani da hadisi, tareda ruguza bidi'a da tsayar da sunnah
Yanzu haka wasu sunyi nutso a
cikin tekun bidi'a ta hanyar fifita shehunnai da kuma allantar da wasunsu. Buri
na wannan amsar ta fargar da wasu yan bidi'a akan tarihin abinda ya faru ga
shehun da suke bi alhalin sun gafala da abinda mutane masu binciken tarihi suka
sani
Littafin Prof. Dahiru Maigari
(Daga Islamic Dept. BUK, mawallafin littafin "Shaikh Inyass as-Singali da
kuma littafin "ad-Dariqatut Tijjaniyya"), zai taimaka sosai wajen
fito da hujjojin
Kamar yanda marigayi Shaikh
Albany Zariya ya binciko, yace musamman Prof. Maigari yayi thesis din sa na PhD
a wannan bangaren ma'ana shi a gidansu ya dingire. To amman abin mamakin shine,
a lokacin da yayi wannan littafin saida yan dariqa suka so su kashe shi, saboda
a cikin littafin yayi bayani da hujja cewar Shaikh Ahmad Tijjani ya taba buga
kudaden jabu (forgery), hukumar kasar su ta kama shi, aka yi masa dukan tsiya,
aka daure shi a kotu a karshe aka koreshi daga kasarsa
Yan dariqa sukai musun wannan
labarin, (suka ce karya ne) nan da nan sai hukuma ta bincika kuma ta tabbatar
da cewar anyi hakan (kuma yan kasar su Shehu Ahmad Tijjani din shaidu ne akan
hakan). A karshe aka qarqare cewar indai aka kashe Prof. Dahiru Maigari to da
sa hannunsu (yan dariqa) indai ba mutuwace irin ta Allah ba, dukkan yan dariqa
suka sa hannu, Professors na BUK ma suka sa hannu. To ammanfa wai a hakan shi
wannan Ahmad Tijjani din yake da mabiya miliyoyi a kasar da take da EFCC!
Shaikh Albany Zariya yace "Da ni dan majalisar (tarayya) ne da sai na taso
da wannan zancen wataran". Ku kula cewar Prof. Dahiru Maigari fa a gidan
kaulaha ya girma, don haka babu kokwanto akan abinda ya faru tunda su ganau ne
ba jiyau ba
~ inji Shaikh Albany Zariya
(Rahimahullah)
Na tambayi Ambassador Muhammad
Arab akan hukuncin dan Nigeria wanda ya buga kudin jabun, sai ya bani amsa
kamar haka;
Toh, Shidai jabun kudi a tsarin
dokokin kasa da Sharia ana masa laqabi da "Counterfeit" Wanda yake
haramun ne a cikin dokokin Nigeria Wanda kowacce hukuma zata Kama mutum ta
gurfanar dashi a ganaban Court domin hukunci.
A cikin kundin dokokin wato
"CBN Act (2007)" Sashi na 20 hudu cikin baka wato (4) tayi magana a
takaice kan cewa dukkan wanda aka Kama da Buga kudin bogi ko Amfani dashi ya
zama wajibi a hukuntashi ta hanyar turashi zuwa gidan gyaran, Kuma kada yayi
kasa da Shekara Biyar cikin wa'adin zaman da zaiyi acan.
Ga Yanda turancin yake a CBN Act
20027 👇
“For the avoidance of doubt, Section 20(4)
of the CBN Act (2007) as amended, states that: “It shall be an offence
punishable by a term of imprisonment of not less than five years for any person
to falsify, make or counterfeit any bank note or coin issued by the Bank which
is legal tender in Nigeria.”
GA WASU KADAN DAGA HUKUNCE
HUKUNCEN DA AKAYI BADA JIMAWA BA DA YADDA SUKA KASACE👇
21
August 2021
Wata Babbar Kotu dake zamanta a
karamar hukumar Birnin Kudu ta nan Jihar Jigawa ta yankewa Farfesa Steve
Uchella da Bonafice Afifa Oru hukuncin daurin shekaru 5 a gidan Yari bisa
zargin su da laifin yin Jabun kudade.
An gurfanar da masu laifin a
gaban alkali mai shari’a Musa Ubale, bisa laifuka guda uku da suka hada da hada
baki da aikata laifuka da cin amana da buga jabun kudi.
kuma Kotun ta yanke musu hukuncin
daurin shekaru 5 bisa Laifin hada baki da aikata laifuka da cin amana da buga
jabun kudi, ko kuma su biya tarar Naira dubu 500,000 kowannen su.
23 February 2020
Wata kotun tarayya da ke zamanta
a Yola, babban birnin jihar Adamawa, ta yanke wa wasu mutane hudu hukuncin
daurin shekara 60 a gidan yari bayan an gurfanar da su bisa tuhumarsu da
mallakar jabun kudi.
Jastis Abdulazeez Anka ne ya
yanke wa mutanen hudu, da suka hada da mace guda daya, hukuncin bayan hukumar
ICPC mai yaki da cin hanci da rasha wa ta gurfanar da su. Alkalin ya bayyana
cewa zasu shafe shekaru 10 a gidan yari a kan kowanne laifi da suka aikata,
kuma kotun ta same su da aikata guda shidda.
Allah swt ya karemu ya tsare mu
daga mugunji da mugun gani tareda Mummunan Aiki.
Fatan Alkhairi
Bissalaam
©Boss Mohammed Arab (Saturday
23.12.2023)
Sannan kuma munsan a musulunce
wannan laifin zamba ne kuma aikata zamba haramun ne
A bangaren littafin
"Jawahirul Ma'ani" da yan Tijjaniyya suke kafa hujja kuma, Prof. Dauda
Ojobi yayi bayani sosai akan asalin littafin. Kafin karanta bayanansa yakamata
a fara sanin wanene Prof. Dauda Ojobi
Ya kasance Bishop ne kuma shine
Former Secretary of Northern Christian of Nigeria (CAN) wato tsohon sakataren
kiristocin arewacin Nigeria. Retired Professor Faculty din Law dake Jami'ar
jihar Benue. Haka kuma shine Third Reverend Father daga arewacin Nigeria bayan
Paul Gindri da GG Ganaka. Shine tsohon Commissioner of Justice a jihar Bauchi
kuma tsohon shugaban Baptist Church na farko a Kaduna. A karshe Allah
Azzawajalla ya shiryar dashi bisa tafarkin musulunci, daganan ya koma
makarantar allo, a hankali a hankali ya samu ilimin addinin musulunci kuma ya
zama silar musuluntar da dubunnan Christians ta hanyar amfani da Qur'ani,
hadisai da kuma Bible. Professor Dauda Ojobi yana da PhD dai dai har guda 4.
Ma'ana yanada BSc guda 6, MSc guda 6, PhD guda 4. Gaba daya Degree dinsa 16
kenan
Prof. Dauda Ojobi tsohon dan
Tijjaniyya ne domin kuwa saida yayi shekaru 19 a dariqar Tijjaniyya, a karshe
ya fita daga dariqar bayan ya gano illolinta ya koma Ahlus Sunnah, kamar yanda
ya shaidawa al'umma a wani karatu da sukai tare da marigayi Shaikh Albany
Zariya mai taken: "A INA GASKIYAR TAKE?". A karatun ne yayi bayanin
cewar shi (Prof.) da kansa yake yiwa Ibrahim Kaulaha tausa idan yana hutawa, a
lokacin da ya zauna a gidan Kaulaha, sannan kuma yayi bayani akan "Wanene
Reverand Peter Jatau" da kuma "Wanene Mai Tatsine" sannan kuma
yayi tsokaci akan "Salatil Fatih" da yan Tijjaniyya suke yi
Prof. Dauda Ojobi yace
"Akwai wani littafi mai suna
Jawahiril Ma'ani wanda jahilai suke ta kashe kansu akansa, wanda ya wallafa
wannan littafin Bishop ne kamar ni wato ba musulmi bane ba, dan kasar Misra ne
(Egypt)"
Ya ci gaba da cewa: "Emperor
Habacus na Rome, shi ya bashi ijara yaje ya fitarda abinda zai batar da
musulmai ta hanyar tusa musu wani ra'ayin a zuciyarsu. Sunansa Bishop Salvan
Gregory. An wallafa littafin Jawahiril Ma'ani a shekarar 1892 A.D wanda yayi
daidai da 1260 A.H a karkashin censorship na Emperor Habacus dake kasar Rome.
Idan zaka tabbatar da wannan zance sai kaje ka duba littafin Roman Catholic
Encyclopedia 1940 Volume 8, page 109"
"Littafin Jawahiril Ma'ani
sashin Antagonism ne, sannan kuma (duk dalibin ilimi yasan) Annabi SAW baiyi
maulidi ba, hakama sahabbansa da tabi'ai da atba'ut tabi'in duk ba wanda yayi,
amman wanda yayi Maulidin Naby da farko a shekarar 597 A.H (Anno Hegira) wanda
yayi daidai da 1211 A.D (Anno Domini) shine Bishop Hezakaya Volak ya qirqiro
Maulidin Naby a karon farko, mutumin kasar Turkey ne. Don haka idan kana son ka
kara nazari sannan ka tabbatar da hakan saika duba cikin littafin Roman
Catholic Encyclopedia 1940 Volume 8, page 18,112"
"Idan maulidi musulunci ne
to me zai kai asalinsa cikin littafin Roman Catholic Encyclopedia, har ma ya
samu fassararsa daga wajen?"
Anan maganar Prof. Dauda Ojobi ta
tiqe
(Ka duba kaset din marigayi
Albany mai taken: "A INA GASKIYAR TAKE?")
Wancan "Jawahirul Ma'ani
kenan to ina kuma ga idan ka duba littafin "Jawahirul Masa'id"
wallafar Ibrahim Inyas?
Ni dai a iya dan karamin sani na,
idan mutum ya buga kudin jabu (forgery) babban laifi ne, wasu kasashen ma kashe
mutum suke yi.
To yanzu tambaya ta farko anan
itace; su yan dariqa me yasa basa binciken asalin abu saidai kawai su dinga
aiwatarwa ba tare da neman ilimi akan abin ba. Sannan kuma tambaya ta biyu
itace; me yasa shehunnansu suka boye musu wannan al'amari na jabun kudi da
Shehu Ahmad Tijjani ya taba bugawa har aka koresa amman a haka miliyoyin mutane
suke bin dariqarsa ta Tijjaniyya?
Muna roqon Allah ya rabamu da
bidi'a ya tabbatar damu akan musulunci bisa sunnar Annabi SAW kan fahimtar
Salaf (Magabatan farko)
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa
Usman Danliti Mato
(Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.