𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu Alaikum Malam Khamis. Mijina
ya sakeni saki ɗaya,
ina da ciki wata 6 a jikina, sai daga baya kafin na haihu sai yace ya dawo dani,
ni Kuma naki komawa tunda Daman hakuri nakeyi dashi yazo ya sakeni batare da
nace yasakeni ba, Kuma Malam har cikin Raina banason sake komawa gidansa sabida
gaba ɗaya yafita a
raina, Babu sonsa azuciyana, meye matsayina donshi yanacewa ni matarsace nikuma
inacewa ba matarsa bace, don yana ikirarin zaiga ubanda zai dauramin aure, ataimakamin
da amsa, bissalam🙏🙏
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam Warahmatullah
Wabarkatuhu
To 'yar'uwa tabbas miji yana da
damar da zai yiwa matarsa kome mutukar tana cikin idda. Duk Mutumin da ya saki
matarsa. Matukar dai Iddarsa bata Cika Akanta ba. Sai kuma Yace ya Maidata. To
ba Makawa ta Maidu. Ko tana so ko bata so. kuma iyayen matar ko ita kanta ba su
da damar da za su ja masa birki Sabida Faɗin
Allah da Yake Cewa
وَبُعُوْلَتُهُنَّ اَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِىْ ذٰلِكَ اِنْ اَرَادُوْۤا اِصْلَاحًاۗ
Kuma mazan aurensu su ne mafiya
haƙƙi
ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin Maslaha. (Surah: Al-Baqara, Ayat:
228)
Amma mutukar bai yi mata kome ba
har ta kammala idda to ba shi da dama akan ta, amma zai iya shiga cikin manema.
Yadda ake Yiwa Irin Waɗannan Mazajen Waɗanda Basa Son Zaman
Lafiya. Domin Suna Maida Mace ne dan Su Azabtar da Ita. Ba don Su cigaba da
zama don Maslaha ba, Sabida Sun San Allah ya ba su wannan Damar.
Idan har Akwai Cutarwa da
Wulakanci da Sauransu. Wanda Wannan Halayen Nasa ne ma yasa Kika ji ya Fita a
Ranki. Har ta kai da son sa baya Zuciyarki. Kuma baki da Ra'ayin Komawa Gidansa.
To babu laifi ki nemi khul'i daga gareshi. Wato ki bashi sadaqin da zai isheshi
ya auri wata matar, (Amma wannan agaban alqali ake warwarewa) a ɓata auren a Kasheshi
yazama ke da mijinki babu wani ƙulli tsakaninku, dan haka baze yiwuba a
gyara Auren ko ya maida ki ba sai in ya sake biya sabon Sadaki an sake ƙulla
Sabon Aure, domin shi khul'i ba Saki bane, Asali Faskhune shi.
Allah Yace
اَلطَّلَاقُ مَرَّتٰنِۖ فَاِمْسَاكٌ بِۢمَعْرُوْفٍ اَوْ تَسْرِيْحٌ بِۢاِحْسَانٍۗ وَلَا يَحِلُّ لَـکُمْ اَنْ تَأْخُذُوْا مِمَّاۤ اٰتَيْتُمُوْهُنَّ شَيْـــًٔا اِلَّاۤ اَنْ يَّخَافَاۤ اَ لَّا يُقِيْمَا
حُدُوْدَ اللّٰهِۗ فَاِنْ خِفْتُمْ اَ لَّا يُقِيْمَا
حُدُوْدَ اللّٰهِۙ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا فِيْمَا افْتَدَتْ بِهٖۗ تِلْكَ حُدُوْدُ اللّٰهِ فَلَا تَعْتَدُوْهَاۚوَمَنْ يَّتَعَدَّ حُدُوْدَ اللّٰهِ فَاُولٰۤٮِٕكَ هُمُ الظّٰلِمُوْنَ
Saki sau biyu yake, sai a riƙa da
alhẽri,
ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da
kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin
Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to,
bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne
sabõda haka kada ku kẽtare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai. (Surah:
Al-Baqara, Ayat: 229)
Mallamai ma'abota ilimi sunyi
bayanin ya halasta ga mace idan tana fuskantar zalunci da cutarwa daga mijinta
babu laifi ta nemi saki daga gareshi, wasu suna ganin wajibi ne ma ya sake ta
in dai ta nemi sakin, sannan bayan ya sake ta kuma aladabtar da shi, Idan kuma
ya ki sakin ta to zata iya yin khul'i ta fanshi kanta daga wajan mijinta ta
hanyar ba shi sadakin da ya ba ta lokacin auranta kamar yadda matar Thabit Bn
Kais bn Shammas ta yiwa mijinta a hadisin da ya tabbata a manyan Kundayan
musulunci.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.