Namiji Zai Iya Yin Kitso A Kansa?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Allah shigafarta malam naji wata magana ne yau kuma ina shakku akai, wai Namiji zai iya yin kitso a kansa ba haramun bane?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Dangane da yin kitso ga mazaje ko kuma barin gashinsu haka, abu ne wanda addini bai tsananta akai ba.

    Domin kuwa an ruwaito cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yakan bar gashin kansa ne asake ba tare da kitso ba.

    Sannan kuma an ruwaito cewa ya taɓa raba Sumar kansa kashi huɗu, sai ya kitsesu daban daban.

    Sayyiduna Abu Huraira (ra) ya ruwaito Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana cewa: "Duk wanda yake da Gashi, to ya kula (ya tsaftace) abinsa". (Abu Dawud hadisi na 4163).

    Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam shi kansa yana da gashi mai tsawo har zuwa kan kafadunsa. (Kamar yadda Imam Bukhary ya ruwaito daga Anas bn Malik, ahadisi mai lamba 5563 da kuma Sahihu Muslim hadisi mai lamba 2338.

    Har ma wani lokacin matarsa Sayyida A'isha takan taje masa gashin kamar yadda Imamul Bukhary ya ruwaito a hadisi na 219.

    Imam Tirmizy da Abu Dawud da Ibnu Maajah sun ruwaito hadisi daga Sayyidah Ummuhani (ra) tana cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya shigo garin Makkah alhali akwai kitso guda huɗu akansa".

    Da yake shin Sharhi akan wannan hadisin, Ibnu Hajr Al-askalani yace : Wannan hadisin na Sayyidah Ummuhani za a daukeshi ne amatsayin cewa ba wai ko yaushe yake yin kitson ba.

    Yakan yi ne a lokacin da bai samu damar Tajewa ko kula da gashin sosai ba, saboda halin tafiya, ko yaki. Ba wai abu ne na yau da kullum ba.

    (FATHUL BAAREE, mujalladi na 10 shafi na 360).

    Awancan lokacin nasu, ba abun mamaki bane don mutum namiji ya yi kitso. Amma a lokutan da suka biyo bayan wannan, sai abun ya zama ba al'adar Mazaje ba.

    Don haka idan mutum ya tsinci kansa agarin da maza masu mutunci suna yin kitso shikenan babu laifi yayi.

    Amma idan ka tsinki kanka agarin da Mazaje masu Mutunci ba su yin kitso, to bai kamata kayi ba.

    Mu dai anan yankin Nigeria bamu saba ganin Maza manya masu mutunci suna yin kitso ba. Sai dai Mawakan turai, ko 'yan Kwallo da dai sauransu.

    Bai kamata mutum ya yi koyi dasu ba. Domin kuwa duk wanda ya yi kama da wasu mutane to za a tasheshi tare dasu aranar Alkiyama.

    WALLAHU A'ALAM.

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.