𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaykum Warahmatullahi, Da
fatan malam yana lafiya, Malam ya halatta namiji ya yi kunshi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikum assalam, Ya halatta
namiji ya yi kunshi a gemunsa da kansa, da launin da yake ba baki ba, kamar
yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi umarni a yiwa Abu-Khuhafa
mahaifin sayyadi Abubakar R. A lokacin da ya musulunta ranar buɗe Makka a hadisin Ibnu
Hibban mai lamba: 5472 Wanda Shuaibu Al'ar'na'u'd ya inganta.
Ya wajaba namiji ya nisanci duk
wani kunshi da zai zama kamanceceniya da mata, saboda Allah ya la'anci namijin
da yake kamanceceniya da mata kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi mai
lamba ta: 2784.
Yana daga cikin ka'diojin da ya
kamata a sani cewa: Kamanceceniya da mata yana iya banbanta daga wuri zuwa wuri,
yana saɓawa daga
al'ada zuwa wata.
Allah ne mafi sani
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat. whatsapp. com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.