𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Shin ko laifi ne idan na nemi saki daga mijina sakamakon ba ya min adalci, don ba ya so na?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah Wa Barakaatuh.
Asali dai ya halatta mace ta nemi
mijinta ya sake ta, idan ba ta son shi, saboda hadisin da Al-Imaam Al-Bukhaariy
(5273) ya riwaito daga Sahabi Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa: Matar
auren Thaabit Bn Qaisin (Radiyal Laahu Anhumaa) ta zo wurin Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ta ce: Ni dai ba na zargin Thaabit Bn Qaisin
da wani mummunan abu a cikin ɗabi’a
ko addini, sai dai kaɗai
ina ƙyamar
kafirci ne a cikin musulunci! Sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya ce
« أَتَرُدِّينَ عَلَيْهِ حَدِيقَتَهُ » .
Za ki mayar masa da lambunsa
kenan?
Ta ce: E. Sai Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce masa
« اقْبَلِ الْحَدِيقَةَ وَطَلِّقْهَا تَطْلِيقَةً »
Karɓi
lambunka, kuma ka sake ta saki guda.
Amma kuma in ba da dalili ƙwaƙƙwara
ba haram ne mace ta nemi mijinta ya sake ta, saboda hadisin da Al-Imaam
Abu-Daawud (2226) da At-Tirmiziy (1187) suka riwaito daga Thaubaan (Radiyal
Laahu Anhu) daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
« أَيُّمَا امْرَأَةٍ سَأَلَتْ زَوْجَهَا طَلاَقًا فِى غَيْرِ مَا
بَأْسٍ فَحَرَامٌ عَلَيْهَا رَائِحَةُ الْجَنَّةِ »
Duk wata matar da ta nemi saki
daga wurin mijinta ba da wani dalili muhimmi ba, to kuwa ƙamshin
Aljannah haram ne a gare ta.
Sannan kuma ba ki yi bayanin me
kike nufi da cewa: ‘ba ya miki adalci’ ba. Idan kina nufin adalci a wurin
soyayyar zuci da sha’awar saduwa da sauran makamantan haka, to wannan ba abu ne
mai yiwuwa ba tun daga nassin Alqur’ani
وَلَنْ تَسْتَطِيْعُوْۤا اَنْ تَعْدِلُوْا بَيْنَ
النِّسَاۤءِ وَلَوْ حَرَصْتُمْ فَلَا تَمِيْلُوْا كُلَّ الْمَيْلِ فَتَذَرُوْهَا كَالْمُعَلَّقَةِۗوَاِنْ تُصْلِحُوْا وَتَتَّقُوْا فَاِنَّ اللّٰهَ كَانَ غَفُوْرًا رَّحِيْمً
Kuma bã zã ku iya yin ãdalci ba a
tsakanin mãtã kõ dã kun yi kwaɗayin
yi. Sabõda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka
rãtaye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
(Surah: An-Nisaa, Ayat: 129)
Idan kuwa kina nufin ba ya yin
adalci a cikin abubuwan da su ke a fili ne a bayyane, kamar a wurin rabon kwana
da abinci da tufafi da makamantan haka, to a nan ya janyo wa kansa wani babban
zunubi ne. Kuma neman ya sake ki ba ita ce hanyar warware matsalar ba. Kamata
ya yi ki tsaya ki cigaba da janyo hankalinsa, ko ki sanar da wanda zai iya
janyo hankalinsa cikin hikima da kyakkyawan wa’azi. Me yiwuwa Allaah ya sa ya
gane ya dawo kan hanya, ke kuma ki samu ladan da ya fi jajayen raƙumma,
kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa game da wanda Allaah ya
shiryar da wani mutum ta hanyarsa.
Idan kuma, kamar yadda kika ce,
ba ya son ki ne, to ai shi ya kamata ya ɗauki
duk matakin da ya dace kamar ya sake ki, ba wai ke ki nemi sakin ba. Tun tuni
dai Allaah Ta’aala ya ja kunnen mazaje
وَاِذَا طَلَّقْتُمُ النِّسَاۤءَ فَبَلَغْنَ اَجَلَهُنَّ فَاَمْسِكُوْهُنَّ بِمَعْرُوْفٍ اَوْ سَرِّحُوْهُنَّ بِمَعْرُوْفٍۗ
وَلَا تُمْسِكُوْهُنَّ ضِرَارًا لِّتَعْتَدُوْاۚوَمَنْ يَّفْعَلْ ذٰلِكَ فَقَدْ ظَلَمَ نَفْسَهٗۗ وَلَا تَتَّخِذُوْۤا اٰيٰتِ اللّٰهِ هُزُوًا وَّاذْكُرُوْا نِعْمَتَ اللّٰهِ عَلَيْكُمْ وَمَاۤ اَنْزَلَ عَلَيْكُمْ مِّنَ الْكِتٰبِ وَالْحِكْمَةِ يَعِظُكُمْ بِهٖۗ وَاتَّقُوا اللّٰهَ وَاعْلَمُوْۤا اَنَّ اللّٰهَ بِكُلِّ شَىْءٍ عَلِيْمٌ
Kuma idan kun saki mãta, sa'annan
suka isa ga ajalinsu (iddarsu), sai ku riƙe su da alhẽri ko ku sallame su da alhẽri,
kuma kada ku riƙe su a kan cũtarwa
dõmin ta tsawaita
idda. Kuma wanda ya aikata wancan, to, haƙĩƙa, yã zãlunci kansa. Kuma kada ku riƙi ãyõyin
Allah da izgili. Kuma ku tuna ni'imar Allah da abin da Ya saukar a kanku na
Littãfi da hikima.
Yana yi muku wa'azi da shi. Kuma ku bi Allah da takawa kuma ku sani cewa lalle
ne Allah ga dukan kõme
Masani ne. (Surah: Al-Baqara, Ayat: 231)
Amma idan a bayan duk waɗannan bayanan kin ga ba za
ki iya yin haƙurin jurewa ba, to kamata ya yi ki fara sanar da manyansa,
kafin manyanki waɗanda
suka ɗaura muku auren,
domin su zauna su binciki al’amarin, kuma su samar da mafita. Allaah Ta’aala
dai cewa ya yi
Surah: An-Nisaa, Ayat: 35
وَاِنْ خِفْتُمْ شِقَاقَ بَيْنِهِمَا فَابْعَثُوْا حَكَمًا مِّنْ اَهْلِهٖ وَحَكَمًا مِّنْ اَهْلِهَاۚاِنْ يُّرِيْدَاۤ اِصْلَاحًا يُّوَفِّـقِ اللّٰهُ بَيْنَهُمَاۗاِنَّ اللّٰهَ كَانَ عَلِيْمًا خَبِيْرًا
Kuma idan kun ji tsõron sãɓãwar tsakãninsu to ku aika
da wani mai sulhu daga mutãnensa da wani mai sulhu daga mutãnenta. Idan sun yi
nufin gyãrãwa, Allah zai daidaita tsakãninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Yã
kasance Masani Mai jarrabãwa.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Turo tambayar ka ta WhatsApp
number, banda kira: 08164363661
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.