𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salamu Alaikum, Malam, wata
matsala ce da ta zama kamar ruwan-dare a wasu sassa ko yankunan ƙasar
nan: Mutum ya ce ya raba-ƙafa a cikin addini, watau yana zuwa masallaci kuma yana zuwa
coci, wai yana gudun kar ya zo wanda ya bi a nan ba shi ne zai haye ba a
lahira! Wai shin yaya matsayin irin waɗannan
mutanen?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Irin waɗannan in dai ba masu taɓin-hankali ba ne, to
manyan jahilai ne. Ba su fahimci komai ba a cikin addinin musulunci. Domin
Kalmar shahada wacce da ita ake shiga addinin Musulunci ta fayyace komai.
Shaidawar da bawan Allaah ya yi cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai dai
Allaah shi kaɗai, ba
shi da abokin tarayya, wannan abin da yake nufi shi ne: Mutum ya amince ne tun
daga zuciyarsa har bakinsa zuwa ga gaɓoɓinsa cewa: Allaah Ta’aala
Maƙagin
halittar sammai da ƙasa, da duk abin da ke cikinsu, da abin da ke a tsakaninsu,
wanda kuma yake gudanar da al’amuransu,
guda ɗaya ne, shi ne
Allaah Tabaaraka Wa Ta’aala: Ba shi da farko, ba shi da ƙarshe, kuma ba shi da
iyaye, ko mata, ko ɗa,
ko wani abokin tarayya. Don haka, shi kaɗai
ne kaɗai abin bauta,
ban da duk wanda ba shi ba daga cikin Mala’iku da Annabawa da Manzannin Allaah.
Ballantana sauran halittun da ba su kai su daraja ba, daga cikin itatuwa da
duwatsu da dabbobi da tsuntsaye da sauran shaiɗanun
mutane da aljanu da sauransu!
Amma a cikin addinin kirista
kuwa, sun ɗauki
Allaah a wurinsu guda ɗaya
ne amma a cikin alloli guda uku: Uba da Ɗa Ruhi mai Tsarki! Wannan kuwa wani
babban zunubi ne mai Girma a mahangar addinin Musulunci. Domin Allaah bai yarda
da wannan gamayyar ko haɗin-gwiwar
ba, ya ƙyamace
shi, kuma ya kafirta duk mai amincewa da wannan aƙidar. Allaah ya ce
لَقَدْ كَفَرَ الَّذِيْنَ قَالُوْۤا اِنَّ اللّٰهَ هُوَ الْمَسِيْحُ ابْنُ مَرْيَمَۗ وَقَالَ الْمَسِيْحُ يٰبَنِىْۤ اِسْرَاۤءِيْلَ اعْبُدُوا اللّٰهَ رَبِّىْ وَرَبَّكُمْۗ اِنَّهٗ مَنْ يُّشْرِكْ بِاللّٰهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللّٰهُ عَلَيْهِ الْجَـنَّةَ وَمَأْوٰٮهُ النَّارُۗوَمَا لِلظّٰلِمِيْنَ مِنْ اَنْصَارٍ ٢٧ لَـقَدْ كَفَرَ الَّذِيْنَ قَالُوْۤا اِنَّ اللّٰهَ ثَالِثُ ثَلٰثَةٍۘوَمَا مِنْ اِلٰهٍ اِلَّاۤ اِلٰـهٌ وَّاحِدٌۗوَاِنْ لَّمْ يَنْتَهُوْا عَمَّا يَقُوْلُوْنَ لَيَمَسَّنَّ الَّذِيْنَ كَفَرُوْا مِنْهُمْ عَذَابٌ اَ لِيْمٌ ٣٧
Haƙiƙa! Waɗanda
suka ce: Allaah shi ne Masihu Ɗan Maryam sun kafirta, kuma Masihun cewa
ya yi: Ya ku Bani-Isra’ila!
Ku bauta wa Allaah Ubangijina kuma Ubangijinku. Kuma lallai duk wanda ya yi
tarayya da Allaah, to tabbas! Allaah ya haramta masa Aljannah, kuma makomarsa
ita ce Wuta, kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka!
Haƙiƙa! Waɗanda
suka ce: Allaah shi na-ukun alloli uku ne sun kafirta! Kuma babu wani abin
bautawa sai dai abin bauta guda ɗaya
(shi ne: Allaah). Kuma idan ba su ciru daga abin da suke faɗi ba, to lallai azaba mai
raɗaɗi za ta shafi waɗanda suka yi kafircin
daga cikinsu!
(Surah Al-Maa’idah: 72-73)
Sannan kuma jingina wa Allaah ɗa shi ne mafi munin zagi
gare shi Subhaanahu Wa Ta’aala. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya faɗa a
cikin hadisin da Al-Imaam Al-Bukhaariy (4482) ya fitar daga riwayar Ibn Abbaas
(Radiyal Laahu Anhumaa) cewa
قَالَ
اللَّهُ : كَذَّبَنِى ابْنُ آدَمَ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ ، وَشَتَمَنِى وَلَمْ
يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ ، فَأَمَّا تَكْذِيبُهُ
إِيَّاىَ فَزَعَمَ أَنِّى لاَ أَقْدِرُ أَنْ أُعِيدَهُ كَمَا كَانَ ، وَأَمَّا شَتْمُهُ
إِيَّاىَ فَقَوْلُهُ لِى وَلَدٌ ، فَسُبْحَانِى أَنْ
أَتَّخِذَ صَاحِبَةً أَوْ وَلَدًا
Allaah ya ce: ‘Ɗan
Adam yana ƙaryata
ni, kuma hakan bai kamace shi ba. Sannan kuma yana zagi na, hakan kuma bai
kamace shi ba. Amma ƙaryata ni shi ne: Riyawarsa cewa wai ba ni da ikon sake mayar
da halittarsa kamar yadda ya kasance kafin mutuwarsa. Zaginsa gare ni kuwa shi
ne: Cewa da ya yi wai ina da ɗa!
Na tsarkaka daga in riƙi mata ko kuma ɗa!’
Kai! Faɗin cewa Allaah Ta’aala yana da ɗa wata mummunar magana ce
da ta kusa ta ruguza rayuwar duniyar nan! Allaah Ta’aala ya ce
تَكَادُ السَّمٰوٰتُ يَتَفَطَّرْنَ مِنْهُ وَتَـنْشَقُّ الْاَرْضُ وَتَخِرُّ الْجِبَالُ هَدًّاۙ ٠٩ وَمَا يَنْۢبَـغِىْ لِلرَّحْمٰنِ اَنْ يَّتَّخِذَ وَلَدًاۗ ١٩
Sama ta yi kusa ta kekkece saboda
shi, kuma ƙasa
ta tsattsage, kuma duwatsu su rididdige; saboda sun jingina ɗa ga Allaah Mai Rahama
(Surah Maryam: 90-91)
To, ta yaya wanda ya san wannan a
Musulunci zai taɓa
yin tunanin samun tsira a hanyar masu faɗin
irin waɗannan
munanan maganganun ga Allaah Tabaaraka Wa Ta’aala?!!
Don haka, abin da ya wajaba ga
duk wanda ya sani shi ne: Ya karantar da irin waɗannan
mutanen sahihin addinin musulunci. Kuma kar a kuskura a mayar da maganganunsu
abin dariya ko raha. Domin ko kusa abin ba na dariya ko annashuwa ba ne. Laifin
kan iya shafar waɗanda
suka yi sakaci wurin karantar da su ma. Allaah ya kyauta.
Amma game da matsayinsu a lahira,
wannan kam yana wurin Allaah Ta’aala ne Masanin ɓoye
da bayyane na dukkan al’amura. Idan a haƙiƙa iyakan ilimin mai irin wannan ra’ayin kenan, kuma tsoron
Allaah ne manufarsa ga hakan, to zai iya yiwuwa Allaah ya yafe masa, kamar
yadda ya yafe wa wanda ya yi wasiyya ga ’ya’yansa cewa: Bayan mutuwarsa
su ƙona
gawarsa, kuma su sheƙe tokar a cikin iska, don gudun kar Allaah ya kama shi!
Idan kuma shegantaka ce da sakaci
wurin neman gaskiya, to wannan al’amarinsa a fili ya ke.
Allaah ya kiyaye!
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.
com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook.
com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.