Ticker

Robon Kwana Tsakanin Uwargida Da Amarya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Miji ne shekara guda da watanni biyu rabonsa da iyalinsa saboda yana karatu a wani garin. A bayan tafiyarsa sai aka ɗaura masa aure da wata amarya a garin nasu. To, yanzu da zai komo gida daga makaranta shi ne yake tambaya: Wai a wurin wace matar zai fara sauka? Yana son a ba shi dalili a kan duk abin da aka zaɓa masa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

A wurin uwargidansa zai fara sauka kamar yadda ya saba: Su gaisa da ita, kuma ya zauna a wurinta, kamar yadda yake yi a wurin iyayensa idan ya komo daga tafiya. Ya ci abinci a wurin uwargidansa, ya rungume ta, ya sumbance ta, amma ba tare da saduwar aure ba, domin ba kwananta ba ne.

Yin wannan ya halatta saboda hadisin A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) ta ce

كَانَ رَسُولُ اللهِ  - صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَآلِهِ وَسَلَّمَ - لَا يُفَضِّلُ بَعْضَنَا عَلَى بَعْضٍ فِي الْقَسْمِ مِنْ مُكْثِهِ عِنْدَنَا ، وَكَانَ قَلَّ يَوْمٌ إِلَّا وَهُوَ يَطُوفُ عَلَيْنَا جَمِيعاً ، فَيَدْنُو مِنْ كُلِّ امْرَأَةٍ مِنْ غَيْرِ مَسِيسٍ ، حَتَّى يَبْلُغَ الَّتِي هُوَ يَوْمُهَا ، فَيَبِيتُ عِنْدَهَا

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance a iya zamansa a cikinmu, ba ya fifita sashenmu akan sashe a wurin rabon kwana, kuma da ƙyar wuni guda ke wucewa har sai ya kewaya a cikinmu gaba-ɗaya, sai ya kusanta ga kowace mace amma ba tare da saduwa ba, har sai ya kai ga wacce ya ke yininta ne, sai ya kwana a wurinta.

(Ahmad: 6/107-108, da Abu-Daawud: 2135, da Al-Haakim: 2/186 suka riwaito shi, kuma As-Shaikh Sameer Bn Ameen Az-Zuhairiy (Hafizahul Laah) a cikin ta’aliqinsa ga Bulughul Maraam, shafi: 323-324, ya bayyana cewa: Hasan ne).

Wannan ya nuna

1. Miji yana iya shiga ɗakin wacce ba kwananta ba kuma ya yi komai da ita in ban da saduwa kawai.

2. Yin wannan ɗin bai shiga cikin karkatar da Allaah ya hana ba, shi ya sa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yake yin sa.

3. In ba da izini ba, miji ba shi da ikon kwana sai a ɗakin wacce ya ke kwananta ne, idan kuwa ya yi gangancin yin haka to ya aikata karkatar da aka hana.

A ranar da sabuwar amarya ta tare, to ita ce da miji ba uwargida ko sauran matansa ba. Haka hadisai suka nuna daga ayyukan Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam):

A cikin Sahih Al-Bukhaariy (4794) daga hadisin Anas Bn Maalik ya kawo ƙissar tarewar auren Ummul-Mumineen Zainab Bint Jahshin (Radiyal Laahu Anhaa), ya ce

أَوْلَمَ رَسُولُ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - حِينَ بَنَى بِزَيْنَبَ ابْنَةِ جَحْشٍ فَأَشْبَعَ النَّاسَ خُبْزًا وَلَحْمًا ثُمَّ خَرَجَ إِلَى حُجَرِ أُمَّهَاتِ الْمُؤْمِنِينَ كَمَا كَانَ يَصْنَعُ صَبِيحَةَ بِنَائِهِ فَيُسَلِّمُ عَلَيْهِنَّ وَيَدْعُو لَهُنَّ وَيُسَلِّمْنَ عَلَيْهِ وَيَدْعُونَ لَهُ

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi walima a lokacin da ya tare da Zainab Bint Jahshin, ya ƙosar da mutane da gurasa da nama. Sai kuma ya fita zuwa ɗakunan uwayen muminai, kamar dai yadda ya saba yi a wayewan garin tarewarsa. Sai ya yi musu sallama kuma ya yi musu addu’ar alkhairi. Su ma suka yi masa sallama, suka yi masa addu’ar alkhairi.

A cikin hadisin da yake saman wannan a cikin Sahih Al-Bukhaariy (4793) ya ambaci lafuzzan da suka yi amfani da su, ya ce

فَخَرَجَ النَّبِىُّ - صلى الله عليه وسلم - فَانْطَلَقَ إِلَى حُجْرَةِ عَائِشَةَ فَقَالَ « السَّلاَمُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الْبَيْتِ وَرَحْمَةُ اللَّهِ » . فَقَالَتْ وَعَلَيْكَ السَّلاَمُ وَرَحْمَةُ اللَّهِ ، كَيْفَ وَجَدْتَ أَهْلَكَ بَارَكَ اللَّهُ لَكَ فَتَقَرَّى حُجَرَ نِسَائِهِ كُلِّهِنَّ ، يَقُولُ لَهُنَّ كَمَا يَقُولُ لِعَائِشَةَ ، وَيَقُلْنَ لَهُ كَمَا قَالَتْ عَائِشَةُ

Sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya fita, ya tafi zuwa ɗakin A’ishah, ya ce: Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah, mutanen gidan nan. Sai ta ce: Wa Alaikas Salaam Wa Rahmatul Laah. Yaya ka samu iyalinka (amaryarka)? Allaah ya yi maka albarka. Sai kuma ya riƙa ƙwanƙwasa ɗakunan sauran matansa dukkansu, yana faɗa musu yadda ya faɗa wa A’ishah, su kuma suna faɗa masa irin yadda A’ishah ta faɗa masa.

Wannan ya nuna: A ɗakin amaryarsa ya kwana a daren da ya gabata, ba a ɗakunan sauran matan ba.

Sannan har a cikin halin tafiya bai bar bin wannan ƙaidar ba. Domin a cikin ƙissar auren Ummul Mumineen Safiyyah (Radiyal Laahu Anhaa) wadda aka yi a lokacin yaƙin Khaibar haka abin ya auku, kamar yadda ya zo a cikin Sahih Al-Bukhaariy: (371) daga Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu), ya ce

فَأَعْتَقَهَا النَّبِىُّ - صلى الله عليه وسلم - وَتَزَوَّجَهَا . حَتَّى إِذَا كَانَ بِالطَّرِيقِ جَهَّزَتْهَا لَهُ أُمُّ سُلَيْمٍ فَأَهْدَتْهَا لَهُ مِنَ اللَّيْلِ ، فَأَصْبَحَ النَّبِىُّ - صلى الله عليه وسلم - عَرُوسًا

Sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ’yanta ta kuma ya aure ta. Har sai da suka kasance a kan hanya (sun yi zango a cikin tafiya) sai Ummu Sulaim ta gyara ta (ta yi wa amaryar kwalliya) kuma ta raka ta zuwa wurinsa a cikin dare. Sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya wayi gari yana matsayin ango.

 

Wannan ya nuna: Ana tarewar aure da amarya a cikin halin tafiya, ba sai an kai gari ba.

Sai dai kuma a nan larurar da ta hana amarya tarewa da mijinta ita ce rashin samun angon a cikin garin da ta ke. Don haka tun da yau ya komo sai ya cika mata haƙƙinta na kwanaki uku ko bakwai, sannan daga baya ya raba musu kwana, kamar yadda Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu Anhu) ya ce

مِنَ السُّنَّةِ إِذَا تَزَوَّجَ الرَّجُلُ الْبِكْرَ عَلَى الثَّيِّبِ أَقَامَ عِنْدَهَا سَبْعاً ثُمَّ قَسَّمَ، وَإِذَا تَزَوَّجَ الثَّيِّبَ أَقَامَ عِنْدَهَا ثَلَاثاً ثُمَّ قَسَّمَ

Yana daga cikin Sunnah: Idan mutum ya auri budurwa akan bazawara ya zauna a wurinta har kwana bakwai sannan ya raba. Idan kuma ya auri bazawara sai ya zauna a wurinta har kwana uku sannan ya raba. (Sahih Al-Bukhaariy: 5214; Sahih Muslim: 1461).

Malamai sun ce

1. Wannan ya nuna: Haƙƙin budurwa ce a fifita ta da kwana bakwai lokacin tarewa, bazawara kuma da kwana uku kafin a yi rabon-kwana.

2. Kuma abin nufi da: ‘ya zauna a wurinta’ shi ne: Kwana tare da ita a wuri ɗaya, da yin barcin rana a ɗakinta, da zama a ɗakinta a cikin yini ko darenta, idan buƙatar hakan ta taso.

3. Jerantawa a cikin waɗannan kwanakin wajibi ne, don haka in da wani miji zai koma ga wata daga cikin matansa kafin ya kammala su, to dole sai ya maimaita su daga farko bayan ya rama wa sauran matansa abin da ya gabata.

4. Idan aka kawo masa sabuwar amarya a cikin waɗannan kwanakin uku ko bakwai, to dole sai ya kammala adadinsu tukuna sannan ya koma ga sabuwar amaryar.

Wannan ita ce fahimtarmu a kan wannan fatawar a yanzu. Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments