Saduwa A Gaban Yaro

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Na ji audio clip na wani malami da yake karatun Iziyya yana cewa, haram ne miji ya sadu da matarsa idan akwai wani a tare da su a ɗakin, ko da kuwa ɗansu ne ƙarami, kuma ko da yana barci. To, waɗanda ɗakin na su ƙarami ne kuma shi kenan musu, yaya za su kauce wa aikata wannan haram ɗin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah:

Gaskiya ne, haka As-Shaikh Abul-Hasan Aliy Al-Maalikiy ya faɗa a cikin Iziyyah, ya ce

وَلَا يُصِيبُ الرَّجُلُ زَوْجَتَهُ أَوْ أَمَتَهُ وَمَعَهُ أَحَدٌ فِي الْبَيْتِ صَغِيرًا كَانَ أَوْ كَبِيرًا يَقْظَانَ أَوْ نَائِماً

Kuma kar namiji ya sadu da matarsa ko kuyangarsa alhali akwai wani tare da shi a cikin ɗakin, ƙaramin yaro ne ko babban mutum, kuma a farke ya ke ko yana barci.

A nan bai faɗi matsayin wannan hanin ba.

Amma Al-Abbiy Al-Mutee’ Saalih Abdussamee’ mai sharhin littafin shi ne ya bayyana hukuncin hanin, inda ya faɗa a sharhi, ya ce

فَيُكْرَهُ مَعَ النَّائِمِ وَالصَّغيرِ، وَيُمْنَعُ مَعَ الْيَقْظَانِ الْكَبِيرِ

Don haka, an karhanta shi tare da mai barci da ƙaramin yaro, kuma an hana shi tare da babban da ya ke a farke. (Al-Muqaddimatul Iziyyah Lil Jamaaatil Azhariyyah, shafi: 206).

Wato, ya raba wannan mas’alar gida biyu ne:

1. Idan akwai yaro ƙarami a farke a cikin ɗakin, ko babban mutum mai barci, to saduwar makaruhiya ce.

2. Idan kuma akwai babba ne wanda ya ke a farke, to sai kawai ya ce: ‘An hana.’

Bai bayyana nau’in hanin ba: Na haramci yake nufi, ko kuwa na karhanci ne? Amma ganin yadda ya raba mas’alar gida biyu, ya rabe magana ta-biyu daga ta-farko, kuma har ya ba waccan ɗin hukuncin karhanci, wannan kamar ishara ce ga cewa hani na haramci yake nufi da maganarsa ta-biyu. Domin idan ba haka ba, to da rarrabewar ba ta da wata fa’ida kenan. Wallahu A'alam.

Ɗaukar hanin a matsayin na haramci shi ya fi natsar da zuciya, domin dalilai daga nassoshin shari’a abin da suka nuna kenan, kamar maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

 »احْفَظْ عَوْرَتَكَ إِلاَّ مِنْ زَوْجَتِكَ أَوْ مَا مَلَكَتْ يَمِينُكَ  «

Ka tsare al’aurarka sai dai daga matarka ko kuyangarka. (Sahih Abi-Daawud: 4017, Sahih At-Tirmiziy: 2794, Sahih  Ibn Maajah: 1920).

Sannan kuma da maganarsa cewa

 »لاَ يَنْظُرُ الرَّجُلُ إِلَى عَوْرَةِ الرَّجُلِ وَلاَ تَنْظُرُ الْمَرْأَةُ إِلَى عَوْرَةِ الْمَرْأَةِ   «

Kar wani namiji ya kalli al’aurar wani namiji, kuma kar wata mace ta kalli al’aurar wata mace. (Sahih Muslim: 338, Sahih Abi-Daawud: 4018, Sahih At-Tirmiziy: 2793).

Malamai sun haɗu a kan cewa: Wannan hanin na haramaci ne. Wato, haram ne a wurin dukkan malamai: Namiji ya kalli al’aurar wani namiji, ko mace ta kalli al’aurar wata mace. Kuma wanda ya fi tsanani shi ne: Namiji ya kalli al’aurar wacce ba matar aurensa ta Sunnah ba, ko mace ta kalli al’aurar wani namijin da ba mijin aurenta na Sunnah ba. (Al-Imaam Abu-Zakariyya Yahya Bn Sharf An-Nawawiy a cikin Sharhu Muslim: (4/30), da Abut-Tayyib Muhammad Shamsulhaqqil Azeem Abaadiy a cikin Aunul Ma’buud: (11/40) sun ambato wannan ijma’in).

A taƙaice dai tun da kallon alaura haramun ne, wannan ya nuna kallo ko sauraron yadda maaurata - ko waɗanda ba su ba - suke aikata saduwar, shi ne yafi tsanani wurin haramci. Ko da kuwa yara ƙanana ne suke ji da ganin hakan, balle kuma manya.

Dole ne iyaye su san cewa: Yana da matuƙar hatsari su riƙa bari yaransu ƙanana suna ji ko ganin yadda ake aikata hakan, ko daga koina ne ma ba wai daga gare su kaɗai ba. Kuma ba wai sai a lokacin da yaran suke tare da su a cikin ɗaki ba. A’a, ko da ba a cikin ɗakin su ke ba, kamar ta hanyar leƙe daga nesa, ko ta hanyar naurar ɗaukan hoto da makamantan hakan! Domin sakaci a kan wannan na iya haifar wa yaran da mummunan sakamako a cikin rayuwarsu.

Kwanan baya a cikin social media an tattauna da wani wanda masifar aikata fyaɗe ta yawaita daga gare shi. A cikin maganganunsa ya bayyana cewa, matsalarsa ta fara ne daga yadda mahaifiyarsa take barin tsiraicinta a buɗe a gabansa a lokacin da take wanka ko kwalliya tun yana ƙaramin yaro! Wai daga nan ne ya zama yana shaawar ganin tsiraicin mace a lokacin da ya girma!

Mu kuwa - Alhamdu Lil Laah - an kare mu daga irin waɗannan masifun tun tuni. Domin Manzon Allaah Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya koyar da mu kyawawan ladubba na musulunci, kamar waɗannan

 »مُرُوا أَوْلاَدَكُمْ بِالصَّلاَةِ وَهُمْ أَبْنَاءُ سَبْعِ سِنِينَ وَاضْرِبُوهُمْ عَلَيْهَا وَهُمْ أَبْنَاءُ عَشْرِ سِنِينَ وَفَرِّقُوا بَيْنَهُمْ فِى الْمَضَاجِعِ «

Ku umurci ’ya’yanku da yin sallah a lokacin suna ’yan shekaru bakwai, kuma ku buge su a kan ta a lokacin da su ke ’yan shekaru goma, kuma ku rarrabe a tsakaninsu a wurin kwanciya. (Sahih Abi-Daawud: 495).

Malamai sun ce: An ɗauki wannan mataki mai tsanani ne a kan yaran da ba su kai lokacin balaga ba, duk kuma da kasantuwar su ’yan uwa ne, domin a kare su daga sharrin muguwar sha’awar jima’i tun suna ƙanana. (Aunul Mabuud: 2/115).

Tun da kuwa haka abin ya ke, ashe ya zama dole iyaye su ɗauki dukkan matakan kare ’ya’yansu daga wannan masifar, kamar ta hana su ganin hakan daga ko’ina ma, balle kuma daga gare su su da kansu.

Kamar yadda wani malami ya taɓa cewa ne: Duk wanda ya tashi a wannan yankin na Arewa a cikin gidaje irin na musulmi kuma har ya kai kamar shekaru arba’in a yau, abu ne mawuyaci ya iya shedar cewa ya taɓa ganin lokacin da ɗaya daga cikin iyayensa ya ɗauki buta ya kewaya domin yin wankan janaba, balle kuma ya ce ya taɓa ganin lokacin da suke aikata saduwar! Duk kuwa da kasantuwa a tare da su yake rayuwa, kuma - a galibi - tare da sauran yayyi da baffanni da ’ya’yansu a cikin gidan. Ga kuma irin ƙuncin rayuwar da kowa ya san ya fi na yau nesa ba kusa ba.

To, meyasa a lokacin suka iya kare waɗannan abubuwan daga idanu da kunnuwan ’ya’yansu, mu kuma a yau muka kasa?

Me yake hana mu iya koyi da irin waɗannan kyawawan halayen na musulunci daga iyayenmu da magabatanmu?

Allaah ya faɗakar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments