𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Malam. wace
sallah ce ta fi yawan lada?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
(1) Dukkan ayyukan ibada da
Allaah ya yi umurni da su suna da falala da lada idan aka yi su a bisa ƙa’idojinsu da sharuɗɗansu. Amma a bayan
Tawheed da kyautata Aqeedah, sallah ita ce mafificiya daga cikin dukkan ayyukan
da ake yi da gaɓoɓi. Shiyasa aka fara
ambaton ta a cikin Hadisin Rukunnan Musulunci.
(2) Sallah ita ce kaɗai aikin da malaman Salaf
suka yi ittifaƙi a kan cewa: Duk wanda ya bar yin ta haka nan kawai da gangar
saboda lalaci, ko da ba tare da jayayya ko musu a kan wajibcin ta ba, ya
kafirta. Domin ita ce bambanci a tsakanin musulunci da kafirci da mushirikanci.
(3) Sallolin Farillar nan guda biyar
da Allaah ya ɗora wa
bayinsa a cikin kowane yini da dare sun fi falala da lada a kan duk waɗanda ba su ba daga cikin
sallolin nafiloli na ‘rawaatib’ da waɗanda
ba ‘rawaatib’ ɗin
ba, kuma daga cikin waɗanda
akwai dalilin da ya sa ake yin su da waɗanda
ba su ba.
(4) A cikin sallolin farilla guda
biyar kuma Sallolin Asubah da La’asar sun fi sauran alkhairi da falala, saboda
Hadisai da suka zo musamman a kan su. Sannan kuma Sallar La’asar tana da fifiko
na musamman ita ma saboda ya tabbata a cikin Hadisai Sahihai cewa ita ce
‘As-Salaatul-Wustaa.’
(5) Ita ma Sallar Jumma’ah da ake
yi a ranar Jumma’a tare jama’a a bayan kammala sauraron huɗubobi guda biyu daga
liman tana da falala a matsayinta da falalarta na idin mako-mako. Musamman kuma
ga wanda ya kula da ƙa’idoji
da ladubbanta, bai tozarta komai daga cikin hakan ba.
(6) Sallar Farilla a masallaci
tare da jama’a a bayan liman ta fi falala a kan wacce aka yi ta a inda ba
masallacin ba, ko da kuwa tare da jama’a ne. Kuma sallar da jama’a suka fi yawa
a cikinta ta fi wacce jama’a suka yi kaɗan
a cikinta. Haka ma wacce aka yi ta a masallacin da ya ke nesa ta fi wacce aka
yi a masallaci na-kusa, sai in da wani dalili.
(7) A cikin Nafiloli kuwa
Sallolin Nafila na ‘Rawaatib’ sun fi waɗanda
ba su ba, saboda Hadisai da suka zo masu yawa a kan bayanin falalarsu cewa:
Suna zama dalilin samun ginin gida na musamman a cikin Aljannah. Baya da
kasantuwar suna da alaƙa da Sallolin Farilla ko dai kafin su, ko kuma a bayan su.
(8) Ta wata fuskar kuma Salloli
irinsu Sallar Janaza ko Sallar Idi ko Sallar Khusufi ko Sallar Roƙon
Ruwa da makamantansu suna da falala da lada fiye da waɗanda ba su ba. Domin yadda aka keɓance su da wani yanayi ko
hali na musamman, baya ga zuwan Hadisai Sahihai da suke nuna wajibcin waɗansu daga cikinsu.
(9) Amma sauran Nafiloli na
ganin-dama da neman ƙarin lada kuwa, sallolin da aka yi a cikin gida sun fi waɗanda aka yi su a cikin masallaci
nesa ba kusa ba. In ban da Sallar Tarawihi ko Asham da ake yi a dararen watan
Azumin Ramadan mai albarka, saboda riwayoyin Hadisai Sahihai da suka zo a kan
ta.
(10) Haka nan dai Sallolin Nafila
na dare sun fi na rana falala, saboda an fi samun natsuwar zuciya da kwanciyar
hankali da nisantar sharrori irin na riya a cikin su. Kuma waɗanda aka yi su a ƙarshen
dare sun fi waɗanda
aka yi su a farkon daren falala, saboda dacewar su da lokacin saukowar Ubangiji
Ta’aala zuwa saman duniya, da kuma dacewa da lokacin halartowan Mala’iku.
(11) Sannan kuma Sallar Wutri da
mutum yake cike adadin raka’o’in sallar darensa da ita ta fi dukkan sallolin
falala, musamman dayake Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
ya damu da ita sosai, kuma bai taɓa
barin yin ta ba, ko a halin tafiya ma balle a halin saman gida. Shiyasa waɗansu malamai suke ganin
ita ma farilla ce!
(12) Ta wata fuskar kuma, sallar
da aka daɗe a tsaye
ana karatu a cikinta ta fi falala a kan wacce ba haka ba. Shiyasa Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yake daɗewa
a tsaye a cikin sallarsa da dare har ƙafafunsa su kumbura, domin kawai ya nuna
godiya ga Ubangijinsa (Tabaaraka Wa Ta’aala)
da ya yi masa gafarar dukkan zunubansa na-gaba da na-baya!
Amma kuma bai ɗora wa sauran musulmi yin
hakan ba. Sai dai ya umurce su da yin iya abin da suke iyawa kawai daga cikin
waɗannan ayyukan.
Saboda kasantuwar shi kamar yadda Allaah Maɗaukakin
Sarki ya siffata shi ne
لَقَدۡ جَاۤءَكُمۡ
رَسُولࣱ مِّنۡ أَنفُسِكُمۡ عَزِیزٌ عَلَیۡهِ مَا عَنِتُّمۡ حَرِیصٌ عَلَیۡكُم بِٱلۡمُؤۡمِنِینَ رَءُوفࣱ رَّحِیمࣱ
Duk abin da ke ƙuntata
muku yana yi masa tsananin wahala, mai kwaɗayin
alkhairi ne gare ku, kuma ga muminai mai tsananin tausasawa ne mai tausayawa.
(Surah At-Taubah: 128).
Allaah ya ƙara mana ƙoƙari
da kafewa a kan ɗa’a.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.