TAMBAYA (52)❓
Dan Allah malam ayimin Karin
bayani game da idan mace zatayi wankan haila sai ta tsefe gashin kanta
AMSA❗
Alhamdulillah
Bai wajabta ga macen da take
wankan janaba ta warware gashinta gaba daya ba to amman ya zama wajibi ruwa ya
ratsa ko wanne lungu da saqo na jikinta, har gashin kanta
An tambayi Shaikh Abd al-Azeez
ibn Baaz (Rahimahullah), wasu matan suna tufke gashin kansu kuma idan sunzo
wankan janaba basa warwarewa. Shin wankansu yayi ? A kula cewar ruwan bai ratsa
ko ina a cikin gashinta ba. Don Allah a bamu shawara. Allah ya saka da alkhairi
Sai ya bada amsa kamar haka;
"Idan har mace ta zuba ruwa a gashin kanta ya wadatar mata, saboda hadisin
Umm Salama (RA) cewar ta tambayi Annabi SAW akan hakan. Tace: Ni mace ce mai
yalwar gashi akaina, shin zan warware gashi na a lokacin da nake wankan janabah
?
Sai Annabi SAW ya ce: "A'a,
ya isar miki ki zuba ruwa sau uku a kanki, bayan haka sai ki kwara ruwa
ajikinki, silar haka kin tsarkaka" Muslim ne ya rawaito shi a cikin Sahih
Muslim
Don haka idan mace ta zuba ruwa a
kanta sau uku ya wadatar mata kamar yanda wannan sahihin hadisin ya nuna
Majmoo' Fataawa al-Shaykh Ibn
Baaz 10/182
Shaykh Bin Baaz ya ce: A bangaren
wankan janabah (ghusl) anfi son a zuba ruwa sau uku akai, amman shafar gashin
bazai wadatar ba saboda wancan hadisin dake cikin Sahih Muslim
Majmoo' Fataawa al-Shaykh Ibn
Baaz 10/161
Ibn al-Qayyim a cikin Tahdheeb
al-Sunan:
Wannan hadisin na Umm Salamah ya
nuna cewar bai wajaba mace ta warware gashin kanta ba bayan janabah. Malamai
sun yarda da wannan riwayar saidai akwai hadisin da aka rawaito daga Abdullahi
ibn Amr da kuma Ibrahim al-Nakha'i wanda ya ce: zata warware gashin. Saidai
bamu ji wani wanda ya goyi bayan wadannan malaman ba
Shaykh al-Uthaymeen ya ce: mafi
karancin abinda zatayi shi ne ta tabbatarda ruwa ya ratsa ko'ina a jikinta, har
karkashin gashinta. Zaifi kyau mace tayi hakan kamardai yanda aka rawaito daga
Annabi SAW cewar lokacin da Asma' bint Shakl tayi tambaya akan wanka bayan
janabah
Annabi SAW ya ce: "Dayanku
zata dauki ruwanta tareda ganyen lotus ta tsarkake kanta ta tsarkake jikinta
sosai. Sai ta zuba ruwa akanta ta cuda sosai ta yanda zai ratsa koina akanta
daganan saita kwarara ruwan a jikinta. Sai ta dauki kaya (ko towel) wanda
yakeda almuski ta tsane jikinta" Asma' tace: "Ta yaya zata tsarkake
kanta da shi ?" Sai Annabi SAW ya ce: "Subhanallah, ta tsarkake
jikinta da shi"
Sai Nana Aisha (RA) ta kara da
cewar: "Ta bi duk inda jini ya bata a jikinta ta goge"
Bukhari da Muslim ne suka rawaito
hadisin
Ba wai dolene sai mace ta kwance
gashinta ba har saidai indai ya zamana ta daureshi ne tamau-tamau saboda gudun
kada ruwa ya qi shiga gashin gaba daya, saboda wancan hadisin na Umm Salamah
Sai Shaykh al-Uthaymeen ya kawo
hujjar wancan hadisin wanda muka kawo a baya
Majmoo' Fataawa Ibn 'Uthaymeen,
11/318, 319
Domin karin bayani sai a duba
amsar tambaya ta: 34,776 da 27,065 da 9,755 da kuma tambayata 2,648
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa
Usman D. Mato
(Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfqds
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.