TAMBAYA (53)❓
Asalamu
alaikum warahamatulahi wabarkatuhu mallam ni dalibinkane inada tambaya allah
yakara daukaka allah yabiyaku allah yasa kamuku da gidan aljana mallam tambayata
shine idan mace tanada ciki tanayin jinin al ada sai tambaya nabiyu idan nasadu da matata
akwai wani ruwa fari yana fituwa agabanta nagode
AMSA❗
Waalaikumussalam,
Warahmatullahi, Wabarakatuhum
Alhamdulillah
A al'adance
dukkan mace mai ciki ba ta jinin al'ada la'akarida musabbabin zubar jinin
al'adar yanada nasaba da rashin haduwar maniyyin namiji (sperm) da kuma
qwayayen halittar mace (ovum ko kuma egg cells) wanda idan ba'a samu haduwarsu
ba to qyanqyasar mutum (fertilization) cikin ikon Allah bazai auku ba
Idan wadannan
halittun qwayayen (egg cells) suka karada mahaifar mace (uterus) basu ga abokan
qyanqyasa ba (maniyyi da ake kirada sperm cell) sai kawai su mutu su koma jini
(wato hemoglobin mai dauke da sinadarin qwayar iron da kuma protein) wanda a
dabi'ance ake kirada jinin al'ada a shari'ance kuma jinin haida (haila) a
turance kuma catamenia ko kuma menstruation (monthly period/cycles)
Kenan fitar da
jinin al'ada ba karamar lafiya ce ga mace ba domin kuwa ta hakanne mace zata
gane cewar budurcinta yana nan bi ma'ana babu wani wanda ya sadu da ita kuma
mahaifarta (uterus) bata samu baquwar halitta ba (sperm cells) wanda a kowanne
inzali (fitar maniyyi daya tak) da akwai yayan halittu qanana (microscopic) da
idanunmu basa iya gani wanda adadinsu yakai ko kuma ya zarce guda 250,000,000
(miliyan 250) wanda a cikinsu da kyar dubunnai suke tsira a cikin dubunnan kuma
daruruwa suke galabaita a cikin daruruwan kuma baifi guda ashirin bane suke
tsira (a karshe dukkansu mutuwa suke wannan kuma cikin ikon Allah da akwai
abinda ake kirada white blood cells sune suke kashe wadancan miliyoyin
maniyyin) wanda a karshe dai guda daya ne tak yake iya qetara mahaifar mace
(uterus) ya shiga ya hadu da qwan mace (egg cells) wanda suna haduwa zasu zama
zygote daganan kuma a samu fertilization sai Allah Azzawajal ya tsara halittar
da yaga damar fitarawa mace ko namiji. A haka aka samar da kusan kowa tun daga
yayan Annabi Adam AS (Habil da Qabil) har zuwa dan Adam din da za'a haifa na
karshe. Allahu Akbar ! (Tsoron Allah Madaukakin Sarki ya zama dole)
Wannan bincike
ne da ilimin kimiyya ya tabbatar amman shekaru 1,400 baya tuni Allah Azzawajal
ya sanar da Annabi Muhammad SAW;
( ثُمَّ خَلَقْنَا النُّطْفَةَ عَلَقَةً فَخَلَقْنَا الْعَلَقَةَ مُضْغَةً فَخَلَقْنَا الْمُضْغَةَ عِظَامًا فَكَسَوْنَا الْعِظَامَ لَحْمًا ثُمَّ أَنشَأْنَاهُ خَلْقًا آخَرَ ۚ فَتَبَارَكَ اللَّهُ
أَحْسَنُ الْخَالِقِينَ )
المؤمنون (14) Al-Muminoon
Sa'an nan kuma
Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an
nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa,
sa'an nan Muka tufãtar
da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam.
Sabõda haka albarkun
Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu
halittawa.
Allah
Azzawajal shine wanda ya halicci mutum daga maniyyi kamar yanda ya fada a cikin
littafin Qur'ani mai girma;
( خَلَقَ الْإِنسَانَ مِن نُّطْفَةٍ فَإِذَا هُوَ خَصِيمٌ مُّبِينٌ )
النحل (4) An-Nahl
Ya halicci
mutum daga maniyyi, sai gã shi yanã mai husũma bayyananniya.
( ثُمَّ جَعَلْنَاهُ نُطْفَةً فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ )
المؤمنون (13) Al-Muminoon
Sa'an nan kuma
Muka sanya shi, ɗigon
maniyyi a cikin matabbata natsattsiya.
Dangane da
batun jinin haila kamar yanda nayi bayani a baya cewar shi wannan cuta ne kamar
yanda Allah Azzawajal ya fada a cikin Qur'ani;
( وَيَسْأَلُونَكَ عَنِ الْمَحِيضِ ۖ قُلْ هُوَ
أَذًى
البقرة (222) Al-Baqara
Kuma suna
tambayar ka game da haila Ka ce: Shi cũta ne.
Don haka amsar
tambayarka a taqaice shine; a iya dan karamin sani na, mace bata jinin al'ada a
lokacin da take dauke da juna biyu kamar yanda dalilai a kimiyyance suka
gabata. Duk da cewar abune mai yiwuwa mace ta samu jini alhalin bata dauke da
juna biyu. Misali: Mace zata iya ganin digon jini wanda ya damfaru a jikin
mahaifa saidai wannan ba jinin al'ada bane, ana kiransa da suna "Implantation bleeding",
haka kuma macen da take jinin al'ada kuma taji kamar alamun tana dauke da ciki
to ba juna biyu bane, ana kiran abinda suna "Normal hormonal
fluctuations" (Karin bayani kuma sai a tambayi qwararrun likitocin da ake
kira da gynecologist)
Sai kuma
tambayarka ta biyu wadda kayi akan fitar wani farin ruwa a gabanta
Shi wannan
farin ruwan shine masana ilimin jima'i suke kiransa da orgasm, yana fitowa ne
sakamakon qololuwar jin dadin sha'awa yayin saduwa. Yana fitowa ne da karfi,
yana feshi, sannan kuma masana sunce fitarsa ba matsala bane kawaidai shi din
sakamako ne ya bayyana na yanda jin dadin saduwar yakai maqura sannan kuma a
cikin mata 100 (alal misali) baifi a samu mace 1 da take fitarda irin wannan
ruwan ba
Zan danyi jan
hankali anan, a duk lokacin da namiji zai kusanci iyalinsa to ya tabbatar da ya
karanta addu'ar da Annabi SAW ya koyar;
Annabi SAW
yace; Idan dayanku ya auri mace, ko ya sayi bawa mai hidima, sai ya ce;
اَللَّهُمَّ إِنِّي
أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.
Allahumma
innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min
sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh.
(Ya Allah ina
rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman
sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa.)
(Hisnul
Muslim)
Idan kuma zai
sadu da iyalinsa sai yace;
بِسْمِ اللهِ اللّهُمَّ جَنِّبْنَا الشَّيْطَانَ، وَجَنِّبِ الشَّيْطَانَ مَا رَزَقْتَنَا.
Bismil-lah,
allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.
(Da sunan
Allah. Ya Allah! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da
shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi.)
(Sahih
Al-Bukhari, Fath ul-Bari lamba ta 138 )
Sannan kuma
kafin mutum yayi inzali (releasing) sai ya karanta addu'ar da Abdullahi Ibn
Mas'ud (RA) yake karantawa; "Allahumma la taj'allish-shaidaani fimaa
razaqtanaa nasibaan"
(Ya Allah !
Kada ka bawa shaidan rabo akan abinda za ka azurtamu)
(Imam Ibn Abi
- Shayba a cikin Al-Musannaf fil Ahaadith wal - Athaar 3:402)
A cikin
littafinsa "Hasken Addu'o'i", Mufti Taqi Uthman (Rahimahullah) yace
"Daga cikin fa'idar karanta wadannan addu'o'in guda biyu, shine; a yayinda
mutum ya shagala da jin dadin tarawa da iyalinsa duk da cewar firta hakan abin
kunya ne amman addini ya koyarda mutum ya shagaltu da ambaton Allah a wannan
yanayin ya zamana ambaton Allah Azzawajal shine farko da karshen ibadar ta sa.
Abinda yake da alaqa da shauqin fata da fata ya koma ibada"
(Hasken
Addu'o'i, P. 65)
Ya Allah muna
roqon ka bamu mataye nagari, suma matan ka basu maza nagari. Allah ka tabbatar
damu akan daidai ka bamu ikon koyi da sunnar Ma'aiki SAW gwargwadon iyawarmu.
Wallahu ta'ala
a'alam
Amsawa;
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.