𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam uba ne
yasa ɗansa ya Saki
matarsa asakamakon rashin zaman lafiya da basuyi sam zaman yaki daɗi kuma ita uwargidan ita
ta kirkiri rashin zaman lafiya kuma shi mijin yayi attempting raba masu gida se
shi mahaifinsa ya hana so daga qarshe se ya ce masa tunda bashi quality na zama
da mace 2 se ya saki amarya. ita kuma amarya bayan an saketa Se tace Insha
Allah kamar yadda yasa ɗansa
ya saketa bada haqqi ba shima insha Allah se ansa an saki yarsa watarana. To shi
ne wasu suka ce sam bata kyauta ba. to don Allah malam yaya hukunci hakan shin
daidai ne ita ta faɗi
hakan haka zalika hukunci da mahaifin ya zartar shima daidai ne. Nagode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam.
Hakkin iyaye na ɗaya daga cikin manyan
hakkoki da Allah Ya yi magana, haka aure na daga cikin sunnar kowane Annabi da
Allah Ya aiko bisa doron kasa, har Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yake cewa
“ Aure sunnah ta ne kuma duk wanda ya kyamace ta ba ya tare da ni”.
Amma duk da girman wannan hakki
na iyaye Allah Bai rataya saki a hannun su ba. Gaskiya abinda uban yayi bai
halattaba, alkaline kawai yake da wannan damar amma uba bashida wannan hurumin.
Zaman lafiya wannan ai wata
jarabawace watarana saikaga ansamu zaman lafiyar.
Na biyu kuma shi ne abinda wannan
matar tafada kuskure ne amma kuskuren bashida yawa wata fuskarma bata da laifi.
Abinda yasa nace tanada laifi
tayi kuskure saboda lallai nasan anzalinceta to yakamata tayi Allah ya isa
kawai tajira taga irin hukuncin da Allah yazama dakanshi yaga dama yayi mata
amma ba ita ce yakamata tazaɓi
irin sakamakon da za'ayi mataba.
Abinda yasa nace kuma batai
kuskureba saboda babu laifi amuslunci azalinci mutum shima yanemi Allah
yasakamar amma gaskiyar magana dai baikamata tace hakaba domin ita yar wannan
mutumin bata dalaifi kuma kinzo kina rokon Allah yasa asaketa.
Sakin mutumin da aka tilasta;
Dole ne miji ya kasance mai ra’ayin kansa, idan kuma har wasu za su yi amfani
da matsayi na jini ko kusanci ko kuma karfi na mulki a bisa tilasci a sakar wa
mutum mace to ba ta saku ba, ciki har da iyaye.
Sai dai mafi kyawu a duk lokacin
da mahaifan mutum suka nuna masa ba su son wani abu, sai ya bi hanyar da ta
dace don fahimtar da su ta yadda za su amince da abin, in kuma har suka cije a
kan sai ya yi abin sai ya dubi girman darajar su da suka yi silar samar da shi
a bisa doron kasa ya yi masu biyayya don neman yardar Allah.
Don haka ina kira ga iyayen da
suka aukar da irin wannan saki da mazajen da aka sakar wa matan da ma waɗanda suka aura da
dukkanin al’ummar musulmi da mu ji tsoron Allah sannan mu tuntubi malamai, don
gaskiya akwai ganganci kuma za a rika afkawa cikin zina da gangan.
Da fatan Allah Ya shiryar da mu
bisa tafarki na kwarai.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURQQ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.