𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Malam, hadisin
da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya shigar da Aliyu da
Fatimah da Hasan da Husayn (Radiyal Laahu Anhum) a cikin mayafi ko bargo kuma
ya ce, su ne Ahlul-Baiti, kuma bai sanya wata daga cikin matansa (Radiyal Laahu
Anhaa) a cikinsu ba, yaya matsayinsa? Domin wani ɗan
shi’ah yana ƙoƙarin kafa hujja da shi?!
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laahi Wa Barakaatuh.
Da farko dai ga waɗansu daga cikin riwayoyin
hadisin
1. Riwayar Waasilah Bn Al-Asqa’i
(Radiyal Laahu Anhu) ya ce
سَأَلْتُ عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ فِي مَنْزِلِهِ، فَقَالَتْ فَاطِمَةُ: قَدْ ذَهَبَ يَأْتِي بِرَسُولِ اللهِ - صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّم - إِذْ جَاءَ، فَدَخَلَ رَسُولُ اللهِ - صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّم - وَدَخَلْتُ، فَجَلَسَ رَسُولُ اللهِ - صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّم - عَلَى الْفِرَاشِ وَأَجْلَسَ فَاطِمَةَ عَنْ يَمِينِهِ وَعَلِيًّا عَنْ يَسَارِهِ وَحَسَنًا وَحُسَيْنًا بَيْنَ يَدَيْهِ، فَلَفَّعَ عَلَيْهِمْ بِثَوْبِهِ وَقَالَ: (إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا)، اللَّهُمَّ هَؤُلاءِ
أَهْلِي، اللَّهُمَّ أَهْلِي أَحَقُّ". قَالَ وَاثِلَةُ: فَقُلْتُ مِنْ نَاحِيَةِ الْبَيْتِ: وَأَنَا يَا رَسُولَ اللهِ مِنْ أَهْلِكَ؟ قَالَ: "وَأَنْتَ مِنْ أَهْلِي". قَالَ وَاثِلَةُ: إنَّهَا لَمِنْ أَرْجَى مَا أَرْتَجِي.
Na je neman Aliyu a gidansa, sai
Fatimah ta ce ya tafi amma zai dawo tare da Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam). Ana cikin hakan sai kuwa ya zo. Manzon Allaah (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya shiga, ni ma na shiga. Sai Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya zauna a kan shimfiɗa, ya zaunar da Fatimah a
damansa, Aliyu kuma a hagunsa. Hasan da Husain kuma a gabansa. Sai kuma ya
lulluɓa musu
mayafinsa, sannan ya karanta wannan ayar: ‘Kawai dai Allaah yana nufin ya kawar
da ƙazanta
ce daga gare ku, ku Ahlul-Bait, kuma ya tsarkake ku matuƙar tsarkakewa. ’ Kuma ya ce: ‘Ya Allaah! Waɗannan iyalin gidana ne, kuma
iyalin gidana da suka fi cancanta. ’ Waasilah ya ce: Sai na faɗa daga wani gefe na
gidan: Manzon Allaah, ni ma ina daga cikin iyalinka? Ya ce: ‘Kai ma kana daga
cikin iyalina. ’ Waasilah ya ce: ‘Wannan tana daga cikin mafi girman abin da
nake ƙauna.
’ (Ahmad (4/107) da
At-Tabariy (28494) da Ibn Hibbaan (6976) da Abu-Ya’laa (7486) da At-Tabaraaniy (2670) da Al-Baihaqiy
(2/152) da Al-Haakim (3/147) suka riwaito shi. Al-Haakim ya inganta shi, kuma
Az-Zahabiy ya dace da shi. Mai At-Tafseerul Ma’muun (6/170) ya ce: ‘Isnadinsa a kan sharadin hadisi sahihi ne. ’).
2. Riwayar Umar Bn Abi-Salamah, agola
a gidan Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce
لَمَّا نَزَلَتْ هَذِهِ الآيَةُ عَلَى النَّبِىِّ -صلى الله عليه وسلم- (إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا) فِى بَيْتِ أُمِّ سَلَمَةَ فَدَعَا فَاطِمَةَ وَحَسَنًا وَحُسَيْنًا فَجَلَّلَهُمْ بِكِسَاءٍ وَعَلِىٌّ خَلْفَ ظَهْرِهِ فَجَلَّلَهُمْ بِكِسَاءٍ ثُمَّ قَالَ « اللَّهُمَّ هَؤُلاَءِ أَهْلُ بَيْتِى فَأَذْهِبْ عَنْهُمُ الرِّجْسَ وَطَهِّرْهُمْ تَطْهِيرًا ». قَالَتْ أُمُّ سَلَمَةَ وَأَنَا مَعَهُمْ يَا نَبِىَّ اللَّهِ قَالَ « أَنْتِ عَلَى مَكَانِكِ وَأَنْتِ عَلَى خَيْرٍ »
Lokacin da wannan ayar ta sauka
ga Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam): {Kawai dai Allaah
yana nufin ya kawar da ƙazanta ce daga gare ku, ku Ahlul-Bait, kuma ya tsarkake ku
matuƙar
tsarkakewa} a gidan Ummu-Salamah, sai ya kira Fatimah da Hasan da Husayn ya
lulluɓe su da mayafi,
a halin Aliyu yana bayansa, sai ya lulluɓe
su duk da mayafin, sannan ya ce: ‘Ya Allaah! Waɗannan
iyalin gidana ne, ina roƙon ka kawar da ƙazanta daga gare su, kuma ka tsarkake su
matuƙar
tsarkakewa. ’ Sai Ummu-Salamah
ta ce: ‘Ya Annabin
Allaah! Har da ni ma a tare da su?’
Ya ce: ‘Ke kina a kan
matsayinki, kuma kina a kan alkhairi. ’
(Sahih At-Tirmiziy: 2562).
Wadannan riwayoyi sun nuna cewa
1. Aliyu da Fatimah da Hasan da
Husayn (Radiyal Laahu Anhum) Ahlul-Baiti ne, wato iyalin gidan Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).
2. Riwayoyin ba su ce, su da ya
saka a cikin mayafi su ne kaɗai
iyalin gidansa (Ahlul-Baiti) ba.
3. Riwayar farko ta nuna har
Sahabi Waasilah (Radiyal Laahu Anhu) ma yana daga cikin iyalin Annabi (Sallal
Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam).
4. Riwaya ta-biyu ba ta saka
Ummu-Salamah (Radiyal Laahu Anhaa) a cikin mayafi ba, amma kuma ba ta cire ta
daga cikin Ahlul-Baiti ba.
5. Matsayin Ummu Salamah (Radiyal
Laahu Anhaa) na alkhairi shi ne dai matsayin sauran matan aurensa (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), wato Ummuhaatul Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhunna):
Manya a cikin Ahlul-Bait.
Kamar yadda ya ke a fili, wannan
hadisin ya zo ne domin fassara sashen ƙarshen aya ta 33 na cikin Suratul Ahzaab,
mai cewa
إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا
Kawai dai Allaah yana nufin ya
kawar da ƙazanta
ne daga gare ku, ku Ahlul-Bait (iyalin gidan Annabi), kuma ya tsarkake ku matuƙar
tsarkakewa. (Surah Al-Ahzaab: 33).
Amma idan aka karanto ayar tun
daga farkonta za a fahimci cewa, Ahlul-Bait su ne matan aurensa kaɗai
وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا
Kuma ku tabbata a cikin gidajenku,
kuma kar ku fita da kwalliya irin fita da kwalliya na zamanin jahiliyyar farko,
kuma ku saida sallah, ku bayar da Zakkah, kuma ku yi ɗa’a ga Allaah da Manzonsa. Kawai dai Allaah
yana nufin ya kawar da ƙazanta ce daga gare ku, ku Ahlul-Bait (iyalin gidan Annabi), kuma
ya tsarkake ku matuƙar tsarkakewa. (Surah Al-Ahzaab: 33).
Hakan kuma shi ɗin ne dai zai ƙara
bayyana sosai, idan aka faro karantun ayoyin tun daga saman wannan ayar har
zuwa wadda ta ke a bayanta
يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ مَنْ يَأْتِ مِنْكُنَّ بِفَاحِشَةٍ مُبَيِّنَةٍ يُضَاعَفْ لَهَا الْعَذَابُ ضِعْفَيْنِ وَكَانَ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرًا ٠٣ وَمَنْ يَقْنُتْ مِنْكُنَّ لِلَّهِ وَرَسُولِهِ وَتَعْمَلْ صَالِحًا نُؤْتِهَا أَجْرَهَا مَرَّتَيْنِ وَأَعْتَدْنَا لَهَا رِزْقًا كَرِيمًا ١٣ يَانِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا ٢٣ وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَى وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا ٣٣ وَاذْكُرْنَ مَا يُتْلَى فِي بُيُوتِكُنَّ مِنْ آيَاتِ اللَّهِ وَالْحِكْمَةِ إِنَّ اللَّهَ كَانَ لَطِيفًا خَبِيرًا ٤٣
Ya ku matan auren Annabi, daga
cikinku duk wadda ta zo da alfasha mabayyaniya za a riɓanya mata azaba riɓi biyu, kuma wannan mai sauƙi ne
a wurin Allaah. Kuma daga cikinku duk wadda ta yi ɗa’a ga Allaah da Manzonsa kuma ta aikata
aiki na-gari, za mu ba ta ladanta riɓi
biyu, kuma mun yi mata tattalin arziƙi na girmamawa. Ya ku matan auren Annabi!
Ku fa ba daidai ku ke da wata ɗaya
daga cikin mata ba, idan dai kun ji tsoron Allaah. Don haka kar ku lanƙwasa
murya da magana, sai wanda akwai cuta a cikin zuciyarsa ya yi tsammanin wani
abu, amma dai ku faɗi
magana daidaitacciya. Kuma ku tabbata a cikin gidajenku, kuma kar ku fita da
kwalliya irin fita da kwalliya na zamanin jahiliyyar farko, kuma ku saida
sallah, ku bayar da Zakkah, kuma ku yi ɗa’a
ga Allaah da Manzonsa. Kawai dai Allaah yana nufin ya kawar da ƙazanta
ce daga gare ku, ya ku Ahlul-Bait (iyalin gidan Annabi), kuma ya tsarkake ku
matuƙar
tsarkakewa. Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin gidajenku na ayoyin
Allaah da Hikima, haƙiƙa Allaah ya kasance Mai Tausasawa ne, Masani. (Surah Al-Ahzaab:
30-34).
Babu wanda zai karanta waɗannan ayoyin cikin lura
da adalci sannan ya yi tunanin cewa, ba matan auren Annabi (Sallal Laahu Alaihi
Wa Alihi Wa Sallam) ake nufi da Ahlul-Baiti a cikinsu ba.
Shiyasa manyan malaman Tafsir
irin su: Ibn Katheer a wurin tafsirin wannan ayar ya ce
وَهَذَا نَصٌّ فِي دُخُولِ أَزْوَاجِ النَّبِيِّ - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - فِي أَهْلِ الْبَيْتِ هَاهُنَا؛ لِأَنَّهُنَّ سَبَبُ نُزُولِ هَذِهِ الْآيَةِ، وَسَبَبُ النُّزُولِ دَاخِلٌ فِيهِ قَوْلًا وَاحِدًا، إِمَّا وَحْدَهُ عَلَى قَوْلٍ أَوْ مَعَ غَيْرِهِ عَلَى الصَّحِيحِ.
Wannan nassi ne a kan shigar
matan auren Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin Ahlul-Bait
a nan, domin su ne dalilin saukar wannan ayar. Kuma sanadin saukar aya ya shiga
cikin ma’anar ayar kai tsaye, ko dai shi kaɗai
a wata maganar, ko kuma tare da waninsa a magana sahihiya.
Sai kuma ya ambato abin da Ibn
Jareer ya kawo daga Ikrimah (Rahimahul Laah) cewa
أَنَّهُ كَانَ يُنَادِي فِي السُّوقِ: {إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا} ، نَزَلَتْ فِي
نِسَاءِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَاصَّةً.
Ya kasance yana yin shela a cikin
kasuwa cewa: {Kawai dai Allaah yana nufin ya kawar da ƙazanta daga gare ku ne,
ya ku Ahlul-Bait (iyalin gidan Annabi), kuma ya tsarkake ku matuƙar
tsarkakewa}, ta sauka a kan matan auren Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ne kaɗai.
Sai kuma ya kawo riwayar da Ibn
Abi-Haatim ya yiwo da isnadinsa har zuwa ga Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa)
a kan wannan ayar cewa
نَزَلَتْ فِي نِسَاءِ النَّبِيِّ - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - خاصة.
Ta sauka a kan matan auren Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ne a keɓance
kaɗai. (Tafseerul
Qur’aanin Azeem: 6/410).
Don haka ba abu ne mai sauƙi ba
a iya fitar da matan Auren Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) daga cikin iyalin gidansa, don lura da wannan hadisin ko waninsa, irin
yadda mabiya addini shi’ah
suka yi.
Amma masu cewa ayar tana magana a
kan waɗanda aka
sanya a cikin mayafi ne kaɗai,
ban da matan aurensa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), har kuma suke
kafa hujja da cewa:
Wakilin suna da aka yi amfani da
shi a cikin ayar a Larabcinta yana dacewa ga maza ne kaɗai ko maza tare da mata a haɗe, amma ba mata su kaɗai ba. Wato kalmar:
{ankum} da kuma {yutahhirakum}. Idan da mata ne kaɗai da kamata ya ce ne: {ankunna} da
{yutahhirakunna}!
A kan wannan malamai sun amsa da
cewa
أَنَّ
التَّذْكِيرَ بِاعْتِبَارِ لَفْظِ الْأَهْلِ كَمَا قَالَ سُبْحَانَهُ : { أَتَعْجَبِينَ مِنْ أَمْرِ الله رَحْمَتُ الله وبركاته عَلَيْكُمْ أَهْلَ البيت } [ هود : 73 ]، وَكَمَا يَقُولُ
الرَّجُلُ لِصَاحِبِهِ : كَيْفَ أَهْلُكُ؟ يُرِيدُ زَوْجَتَهُ أَوْ زَوْجَاتِهِ ، فَيَقُولُ : هُمُ
بِخَيْرٍ
An yi amfani da lamirin maza ne
saboda lura da ɗabi’ar
lafazin Al-Ahl, kamar yadda Ubangiji (Subhaanahu) ya faɗa
قَالُوْۤا اَتَعْجَبِيْنَ مِنْ اَمْرِ اللّٰهِ رَحْمَتُ اللّٰهِ وَبَرَكٰتُهٗ عَلَيْكُمْ اَهْلَ الْبَيْتِۗ اِنَّهٗ حَمِيْدٌ مَّجِيْدٌ
Suka ce: kuna mamaki ne game da
al’amarin Allaah ne, rahamar Allaah da albarkarsa su tabbata a gare ku, ya ku
Ahlul-Bait}. (Surah Huud: 73).
Kuma kamar yadda mutum ke faɗa wa abokinsa ne: Yaya
iyalinka? Yana nufin mata ko matan aurensa. Sai shi kuma ya amsa da cewa: Suna
lafiya. Ya yi amfani da lamirin maza, domin haka ɗabi’ar
lafazin ‘ahl’ ya ke a larabci. (Fat-hul Qadeer: 6/41).
Shiyasa fassarar da ta fi a nan
ita ce ta malaman da suka haɗa
dukkan nassoshin da suka zo a kan haka, kamar yadda Al-Imaam As-Shawkaaniy ya
hikaito daga gare su cewa
هَذِهِ الْآيَةُ شَامِلَةٌ لِلزَّوْجَاتِ وَلِعَلِيٍّ وَفَاطِمَةَ وَالْحَسَنِ وَالْحُسَيْنِ
Ayar ta haɗe matan auren ne da kuma su Aliyu da Fatimah
da Hassan da Husayn.
Sai kuma ya kawo dalilansu
أَمَّا الزَّوْجَاتُ فَلِكَوْنِهِنَّ الْمُرَادَاتُ فِي سِيَاقِ هَذِهِ الْآيَاتِ كَمَا قَدَّمْنَا ، وَلِكَوْنِهِنَّ السَّاكِنَاتِ فِي
بُيُوتِهِ صلى الله عليه وسلم النَّازِلَاتِ فِي مَنَازِلِهِ ، وَيُعَضِّدُ ذَلِكَ
مَا تَقَدَّمَ عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ وَغَيْرِهِ .
Amma dalilin shigar matan auren
saboda a kansu ne ayoyin suke magana, kuma da kasancewar su ne mazauna gidajen
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), masu sauka a cikin masaukinsa.
Abin da ke ƙarfafar wannan maganar kuma riwayoyin da suka gabata daga Ibn
Abbaas da waninsa daga cikin malamai.
وَأَمَّا دُخُولُ عَلِيٍّ وَفَاطِمَةَ وَالْحَسَنِ وَالْحُسَيْنِ فَلِكَوْنِهِمْ قَرَابَتَهُ وَأَهْلَ بَيْتِهِ فِي النَّسَبِ ، وَيُؤَيِّدُ ذَلِكَ
مَا ذَكَرْنَاهُ مِنَ الْأَحَادِيثِ الْمُصَرِّحَةِ بِأَنَّهُمْ سَبَبُ النُّزُولِ
Amma shigan su Aliy da Fatimah da
Al-Hasan da Al-Husayn kuwa, saboda kasantuwar su danginsa ne kuma iyalin
gidansa ne na jini. Abin da kuma ya ƙarfafi wannan, riwayoyin hadisai ne da
suka bayyana cewa su ɗin
ne sanadin saukar ayar.
فَمَنْ جَعَلَ الْآيَةَ خَاصَّةً بِأَحَدِ الْفَرِيقَيْنِ فَقَدْ أَعْمَلَ بَعْضَ مَا يَجِبُ إعْمَالُهُ وَأَهْمَلَ مَا لَا يَجُوزُ إهْمَالُهُ.
Don haka, duk wanda ya kafe a kan
cewa ayar a kan guda ɗaya
daga cikin ɓangarorin
biyu ne ta ke, to lallai ya yi amfani ne da sashen abin da ya wajaba a yi
amfani da shi, kuma ya bar abin da bai kamata a bar shi ba. (Fat-hul Qadeer:
6/43-44).
Sannan kuma ba a nan ne kaɗai Alqur’ani ya ambaci
Ahlul-Bait yana nufin matan aure ba
1. Ƙissar Annabi Ibrahim (Alaihis Salaatu Was
Salaam) a lokacin da Mala’iku
suka kawo masa albishir na samun haihuwa
قَالَتْ يَاوَيْلَتَى أَأَلِدُ وَأَنَا عَجُوزٌ وَهَذَا بَعْلِي شَيْخًا إِنَّ هَذَا لَشَيْءٌ عَجِيبٌ ٢٧ قَالُوا أَتَعْجَبِينَ مِنْ أَمْرِ اللَّهِ رَحْمَتُ اللَّهِ وَبَرَكَاتُهُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الْبَيْتِ إِنَّهُ حَمِيدٌ مَجِيد ٣٧
(Matarsa) ta ce: Kai! Yanzu ni ce
zan haihu, ahalin ni tsohuwa ce kuma ga mijina wannan tsoho ne! Lallai wannan
abu ne mai ban mamaki ƙwarai! (Mala’ikun)
suka ce: Kina mamaki a cikin al’amarin
Allaah ne, rahamar Allaah da albarkarsa su tabbata a gare ku, ya ku Ahlul-Bait.
Lallai shi (Allaah) Godajje ne Mai Daraja. (Surah Huud: 72-73).
Abin nufi da Ahlul-Bait a nan har
a harshen Mala’iku ita ce: Matar auren Annabi Ibrahim, wato Sarah mahaifiyar
Annabi Is’haaq (Alihimus Salaatu Was Salaam).
2. Ƙissar Annabi Musa (Alihis Salaatu Was
Salaam) akwai cewa
فَلَمَّا قَضَى مُوسَى الْأَجَلَ وَسَارَ بِأَهْلِهِ آنَسَ مِنْ جَانِبِ الطُّورِ نَارًا قَالَ لِأَهْلِهِ امْكُثُوا إِنِّي آنَسْتُ نَارًا لَعَلِّي آتِيكُمْ مِنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ جَذْوَةٍ مِنَ النَّارِ لَعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ
Yayin da Annabi Musa ya kammala
wa’adin kuma ya tafi tare da iyalinsa, sai ya hangi wuta daga gefen dutse. Sai
ya ce wa iyalinsa: Ku zauna a nan, domin ni na hangi hasken wuta. Me yiwuwa in
zo muku da labari daga can, ko bakin wuta domin ku ji ɗimi. (Surah Al-Qasas: 29).
A nan ma abin nufi da Ahlu ita
ce: Matar Auren Annabi Musa (Alihis Salaatu Was Salaam) ita kaɗai, a haɗuwar dukkan malamai, har
da malaman shi’ah.
Shiyasa har babban malamin shi’a
a ƙarni
na shida, wato Abu-Aliy Al-Fadlu Bn Al-Hasan At-Tabarsiy mawallafin littafin
Tafsirin Majma’ul
Bayaan wanda Daar Ihyaa’
Turaathil Arabiy na Bairut suka buga a cikin mujalladai goma, da ya zo fassara
kalmar a cikin Surah An-Naml
إِذْ قَالَ مُوسَى لِأَهْلِهِ إِنِّي آنَسْتُ نَارًا سَآتِيكُمْ مِنْهَا بِخَبَرٍ أَوْ آتِيكُمْ بِشِهَابٍ قَبَسٍ لَعَلَّكُمْ تَصْطَلُونَ
A lokacin da Annabi Musa ya gaya
wa iyalinsa cewa: Ni dai na hangi hasken wuta, zan zo muku da labari daga can, ko
kuma in zo muku da bakin wuta yula, ko kwa samu ku ji ɗimi. (Surah An-Naml: 7)
Ga abin da ya ce
{ وَإِذْ قَالَ مُوسَى لِأَهْلِهِ } أَيْ امْرَأَتِهِ ، وَهِيَ بِنْتُ
شُعَيْبٍ
{Kuma a lokacin da Annabi Musa ya
gaya wa ahalinsa} wato: Matar aurensa, kuma ita ce ɗiyar Annabi Shu’aib. (Tafseer Majma’il
Bayaan: 4/211).
Wato dai: Idan har kalmar Al-Ahl
ko Ahlul-Bait yana nufin matar aure a waɗannan
wuraren, ashe a cikin Surah Al-Ahzaab ma su ɗin
ne ake nufi, wato matan auren Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam).
Amma wannan hadisin da ya shahara
da Hadisin Al-Kisaa’u wanda muke tattaunawa a kansa, shi ne ya shigar da Aliy
da Hasan da Husayn (Radiyal Laahu Anum) a cikin Ahlul-Bait. Domin a ƙa’ida ba ka sanya jikokin da ’yarka ta haifa a wani gida
a cikin iyalin gidanka.
Wato dai wannan hadisin da
Ahlus-Sunnah suka riwaito shi, shi ne ya nuna shigar Al-Hasan da Al-Husayn
(Radiyal Laahu Anhumaa) a cikin Ahlu-Baitir Rasuul.
Amma ko kusa shi ba dalili ne a
kan fitar da matar auren Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam)
daga cikin Ahlul-Baitin ba.
Abin da mabiya addinin shi’a suka
yi a cikin wannan mas’ala, na ƙoƙarin taƙaice Ahlul-Bait a kan waɗannan manyan mutanen guda
huɗu: Aliyyu da
Fatimah da Al-Hasan da Al-Husayn (Radiyal Laahu Anhumaa) kaɗai babban kuskure ne, saboda
wannan ya ƙunshi
fitar da waɗanda ba
su ba daga cikin dangi da ’yan uwansu daga cikin Ahlul-Bait:
1. Sun fitar da ’ya’yan Aliyu
kamar su: Muhammad Bn Al-Hanafiyyah da Abubakar da Umar da Uthman da Al-Abbaas
da Ja’afar da Abdullaah da Ubaidullaah da Yahya (Rahimahumul Laah) daga cikin
Ahlul-Bait.
2. Haka kuma sun fitar daga cikin
Ahlul-Bait ɗin dai
jikokin Aliyu na wajen ’ya’yan Aliyu maza guda goma sha-biyu, da mata goma
sha-takwas ko sha-tara a bisa yadda riwayoyi suka sha bamban.
3. Haka suka fitar da ’ya’yan
Fatimah mata guda biyu: Zainab da Ummu Kulthum (Radiyal Laahu Anhunn) da kuma
dukkan ’ya’yansu daga cikin Ahlul-Bait!
4. Wanda ma ya fi duk waɗannan shi ne yadda suka
fitar da ’ya’yan Al-Hasan Bn Aliy shaƙiƙin Al-Husayn kuma yayansa (Radiyal Laahu
Anhum) daga cikin Ahlul-Bait!
5. Wanda kuma ya kere duk waɗannan shi ne yadda suka
fitar da ’ya’yan Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) shaƙiƙan
Fatima, wato Ruqayyah da Ummu-Kulthum da Zainab (Radiyal Laahu Anhunn) daga
cikin Ahlul-Bait. Haka kuma mazajen aurensu da ’ya’yansu!
A taƙaice kuma a fili ƙarara,
fassarar Ahlul-Bait a wurin shi’a
su ne: Rabi ko sashen siffar mutuntakar Fatimah, da rabi ko sahen siffar
mutuntakar Aliy, da kuma rabi ko sashen siffar mutuntakar Al-Hassan. Domin
dukkan sauran limaman shi’a
guda tara daga zuriyar Husayn ne, har zuwa Al-Hasan Al-Askariy. (Dubi ƙarin
bayani a cikin: As-Shee’ah
Wa Ahlul-Bait na Ihsaan Ilaahiy Zaheer Al-Baakistaaniy, shafi: 20).
Allaah Ta’aala nake roƙo da
Sunayensa Tsarkaka da Siffofinsa Maɗaukaka
ya shiryar da mu, kuma ya kare mu da zuriyarmu gaba-ɗaya daga dukkan hanyoyin ɓata da hallaka. Allaah ya
ƙara
tsira da aminci da albarka ga Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) da
Iyalin Gidansa da Sahabbansa da sauran Salihai.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.