TAMBAYA (50)❓
Meye matsayin sakin aure, Idan matar ce tace tanason sakin. Rashin lpyr
mijin ba wadda ake daukabace amman wadda se anyi wahala da ita
AMSA❗
Saki halas ne idan ya cike
sharuddan da shari'a ta gindaya. Dukda cewar halas ne amman shi ne aikin da
Allah yake qyama a cikin halastattun ayyukan mutane. Wannan shi ne dalilin
dayasa Shaidan yafison sakin aure fiyeda kowanne irin laifi banda shirka
Kul'i kenan. Sai ya saketa
ammanfa da sharadin xata maido masa da sadakin da ya bata saboda ita ce ta
buqaci sakin da kanta ba wai mijinba
Kamata yayi ta ci gabada haqurin
zama dashi tunda ai Allah bai saukarda cuta ba saida ya saukarda maganinta
kamar yanda hadisi sahihi ya tabbata
Ko ana dauka dinma kamar irinsu
HIV/AIDS, sickler, ciwon sanyi da sauransu, saikaga silar addu'a Allah ya dauke
cutar kamar ba'a taba yi ba
Shawarata guda 2 ce, indai ita ce
ta nemi sakin saboda tana takura to ta biyashi sadakin kawai a rabu tunda
shari'a ta halasta hakan ko kuma ta ci gabada haquri tunda ai cuta ba mutuwa
baceba. Watarana sai labari
Munga misalin hakan ya faru ga
Annabi Ayuba AS, wanda saida ya rasa komai, ga rashin lafiya ta ci karfinsa
amman da Allah ya qaddara waraka sai gashi ya bashi sauki ya kuma maido masa da
duk abubuwan da ya rasa da kuma qari
Malaman tarihi sukace lokacin da
Annabi Ayub AS yakai shekaru 70, sai ya rasa lafiyarsa da iyalansa. Ya samu
cutar fata (zata iya zama smallpox) yanda gaba daya ilahirin fatarsa ya samu
matsala in banda harshensa da kuma zuciyarsa. Bai yi qasa a gwiwa ba, ya koma
ga Allah SWT ya amsa roqonsa kamar yanda Allah SWT ya labarta mana a cikin
Suratu Anbiya:
( وَأَيُّوبَ
إِذْ نَادَىٰ رَبَّهُ أَنِّي مَسَّنِيَ الضُّرُّ وَأَنتَ أَرْحَمُ الرَّاحِمِينَ )
الأنبياء
(83) Al-Anbiyaa
Kuma da Ayyũba a sa'ad da ya yi
kiran Ubangijinsa, (ya ce:) "Lalle nĩ, cũta ta shafe ni, alhali kuwa Kai
ne Mafi rahamar masu rahama."
( فَاسْتَجَبْنَا
لَهُ فَكَشَفْنَا مَا بِهِ مِن
ضُرٍّ ۖ وَآتَيْنَاهُ أَهْلَهُ
وَمِثْلَهُم مَّعَهُمْ رَحْمَةً مِّنْ عِندِنَا وَذِكْرَىٰ لِلْعَابِدِينَ )
الأنبياء
(84) Al-Anbiyaa
Sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka
kuranye abin da ke a gare shi na cũta, kuma Muka kawo masa mutanesa da kwatank
wacinsu tare da su, sabõda rahama daga wurinMu da tunatarwa ga masu ibada.
Kuma indai har tayi imani da
Allah ai dolene ta jira zuwan jarabawa kanar yanda Allah SWT ya fada:
( أَحَسِبَ
النَّاسُ أَن يُتْرَكُوا أَن
يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لَا يُفْتَنُونَ )
العنكبوت
(2) Al-Ankaboot
Ashe, mutane sun yi zaton a bar
su su ce: "Mun yi ĩmani," alhali kuwa ba za a fitine su ba?"
Ayar gaba sai ta tabbatarda cewar
ba ita kadai bace aka taba jarabta a rayuwa, an jarabci wadanda suka gabata ma:
( وَلَقَدْ
فَتَنَّا الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ ۖ
فَلَيَعْلَمَنَّ اللَّهُ الَّذِينَ صَدَقُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْكَاذِبِينَ )
العنكبوت
(3) Al-Ankaboot
Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabaninsu, dõmin
lalle Allah Ya san waɗanda
suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata.
An jarabci Annabi Ibrahim AS
domin kafirai har wuta suka jefashi, Allah SWT ya kiyayeshi
Hakama Annabi Yunus AS ma'abocin
kifi, Allah SWT ya tseratar dashi
Ga Annabi Yaqub AS wanda ya rasa
idanuwansa silar bacewar dan sa Annabi Yusuf AS amman a karshe Allah SWT ya
warkar dashi
Annabi Ayub AS ma haka Allah SWT
ya jarabceshi da rashin lafiya saida yazamana ya rasa komai amman da ya haqura
ya koma ga Allah sai ya samu waraka
Sannan shi kansa katimul anbiya,
Manzon Allah SAW an jarabceshi da rasa yayansa. Ga kuma maraici tun tasowarsa.
Ahakan yayi haquri saboda Allah SWT yana tareda masu haquri:
( يَا
أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اسْتَعِينُوا بِالصَّبْرِ وَالصَّلَاةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ
مَعَ الصَّابِرِينَ )
البقرة
(153) Al-Baqara
Ya ku waɗanda suka yi ĩmani! Ku nẽmi
taimako da haƙuri game da salla. Lalle ne, Allah na tare da masu
haƙuri.
An karbo daga Mus'ab bin Sa'd RA
daga mahaifinsa Sa'd bin Abu Waqqas RA ya ce: Na tambayi ma'aikin Allah SAW,
wadanne mutanene akafi jarabta ? Sai Annabi SAW ya ce: "Annabawa, sai
mutane nagari sai, sai nagari. Mutum za'a gwadashi gwargwadon riqon addininsa,
idan yana da riqon addini sosai to Allah zai jarabceshi dayawa, hakama idan
yana sakwa-sakwa da addininsa to za'a jarabceshi gwargwadon hakan. Jarabawar rayuwa
(da musibu kala-kala) zasu ci gabada kewayeshi har sai ya koma yana yawo a
doron duniya ba tareda zunubi ko daya ba" (Sunan Ibn Majah 4023
Anan ina bata shawara a karo na
biyu, ta dage da yawaita addu'a, da fadin Allah SWT:
( الَّذِينَ
إِذَا أَصَابَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوا إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ )
البقرة
(156) Al-Baqara
Waɗanda
suke idan wata masĩfa ta same su, sai su ce: "Lalle ne mũ ga Allah muke,
kuma lalle ne mũ, zuwa gare Shi, muke kõmawa."
Ta yawaita haquri domin kuwa
kowanne tsananin yana tareda sauqi:
( فَإِنَّ
مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا )
الشرح
(5) Ash-Sharh
To, lalle ne tare da tsananin nan
akwai wani sauƙi.
( إِنَّ
مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا )
الشرح
(6) Ash-Sharh
Lalle ne tare da tsananin nan
akwai wani sauƙi.
A karshe ta dage da addu'ar
Istikhara don miqawa Allah SWT zabin zama dashi ko kuma rabuwa dashi. Allah
yasa mudace
Wabi hazal qadri kifaya.
Subhanakallahumma, wabi hamdika, ash-hadu anla'ilaha illa anta, astaghfiruka,
wa'atubi ilayk
Amsawa:
Usman Danliti Mato
(Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.