TAMBAYA (54)❓
Assalamu alaikumalaikum. Malam barka darana yakokari;malam ina da tambaya? Tun wancan satin ya kamata In ga jinin al'adata amma shiru haryanzu, kozan iyashan maganin da za ya zo, saboda wasu hujjoji nawa, 1. banisamun isasshen abinci 2, idan nasamu ciki ina yawan ciwo, da kuma ina son wancan bani son wancan, gashi Kuma mai gidana yanzu duk bayada halin wanna, gayaranmu wasuma, komakaranta basu samun zuwa saboda mun shiga jarabawar rayuwa, to malam yaya zanyi ke nan.
AMSA❗
Waalaikumussalam, Warahmatullahi,
Wabarakatuhum.
Alhamdulillah.
Mace zata iya shan maganin
tsayarda jinin al'ada da sharuda guda biyu;
Na farko ya zama na macen bazata
cutar da kanta ba saboda hujjar ayar Qur'ani,
(وَلَا تُلْقُوا بِأَيْدِيكُمْ إِلَى التَّهْلُكَةِ ۛ
البقرة
(195) Al-Baqara
Kuma kada ku jefa kanku da
hannayenku, zuwa ga halaka
Da kuma ayar;
(وَلَا تَقْتُلُوا أَنفُسَكُمْ ۚ )
النساء
(29) An-Nisaa
Kuma kada ku kashe kãnku
Na biyu kuma idan amfani da
maganin zai cutar da mijinta, to ya zama wajibi ta nemi izininsa. Misali; idan
mace tana cikin Iddah kuma mijin yana kashe mata kudi (kafin ta kammala iddar)
to bai halatta ta sha maganin ba saboda hakan zaisa ya kashe mata kudi dayawa,
don haka sai ta nemi izininsa.
Haka kuma bazata sha ba idan tana
son tsayarda haihuwa har sai ta nemi izinin mijinnata. A shawarce ba'a buqatar
ta sha wannan maganin har sai bisa sharudan da aka zayyano a sama kuma sai
hakan ya zama dole akanta saboda haquri da shan maganin shi yafi domin maslaha
ga lafiyarta
Dangane da batun halacci ko
haramci kuwa to wannan Shaikh al-Uthaymeen yace, halasne idan ya cike wadannan
sharudan guda biyu;
Na farko ya zamana hakan bazai
illata ibadarta ba. Misali; idan watan azumi ya kusa tsayawa sai ta sha ta
yanda bazata dinga azumi ko sallah ba
Na biyu; idan zatayi amfani da
maganin tsayarda haihuwa saida izinin mijinta saboda bayyanar jinin haila kan
iya katange mijinnata da wadatuwa ga shigarta (mu'amalar aure), haka kuma idan
an sake ta hakan zaisa mijinnata ya sauke nauyinta dake kansa saboda hakan zai
janyo iddarta da wuri silar shan maganin. Ana magana ne akan sakin kome (wanda
macen zata iya komawa gidan mijin)
Don haka yar uwa, a shawarce, ki
samu maigidanki ku tattauna akan wannan ra'ayi naki. Idan ya amince falillahil
hamd amman akasin hakan saiki hakura tunda ba wajibi bane kuma a qalla hakan
zai zamo balance ga lafiyarki
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa;
Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat. whatsapp.
com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.