𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu
Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ni ce na dawo daga unguwa sai na yi ta yi wa yarona ƙarami
wasa amma sai ya yi banza da ni, bai kula ni ba. Sai ni kuma na ce: ‘Ai ko? To, za ka gani!’ Ina nufin ni ma zan rama
idan nan gaba ya zo yi min wasa. Shi ne babansa ya hau ni da faɗa. Menene matsayin wannan
maganar da na faɗa?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.
Kalmar ‘Za ka
gani!’ a nan kalma ce mai harshen-damo: Tana ɗaukar
fassarori fiye da ɗaya.
Tana iya ɗaukar mummunar ma’ana ta
mugun addu’a ko yin baki ga yaron, kamar idan mahaifiyar ta fusata a kan abin
da yaron ya yi mata. Sanannen abu ne kuwa a addini da rayuwa cewa: Addu’ar
iyaye tana tasiri a kan ’ya’yansu.
Wataƙila
wannan fassarar ce mijinki ya hararo a lokacin da ya ji kalmar ta fito daga
gare ki.
Amma kuma
kalmar tana iya zama mai kyakkyawar ma’ana wacce babu tsoron komai a ƙarƙashinta,
kamar yadda kika yi nufi kuma kika yi bayani.
A irin wannan
halin kodayake mijinki shi ne shugaban gida, kuma daidai ne ya yi ƙoƙarin
gyara duk wani abin da ya ga zai cutar da zamantakewar gidan a kusa ko a nesa -
musamman ma a kan abin da ya shafi magajin gidan watau ɗansa, amma kuma dole ya san cewa ke ma fa
uwa ce kuma mahaifiya ga yaron, wacce kuma ba za ki yi nufin cutar da shi haka
nan siddan ba.
Ke ma kuma
kodayake ke ce uwar wannan yaron wacce ba za ki so aukuwar duk wani abin da zai
cutar da shi ba, amma kuma dole ne ki fahimci matsayin mijinki, wanda alhakin
gyara duk wata karkata ko ɓatar
da ya gani a cikin iyalinsa - har da ke matarsa - ya rataya a wuyarsa a duniya
da barzahu da lahira.
Hadisin Annabi
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) wanda Anas Bn Maalik (Radiyal Laahu
Anhu) ya riwaito ya tabbatar da cewa
إِنَ اللهَ تَعَالَى سَائِلٌ كُلَ رَاعٍ عَمَا اسْتَرْعَاهُ : أَحَفَظَ ذَلِكَ أَمْ ضَيَعَهُ ؟ حَتَى يَسْأَلَ
الرَجُلَ عَنْ أَهْلِ بَيْتِهِ
Lallai Allaah
Ta’aala mai tambayar duk wani makiyayi ne a kan abin da ya ba shi kiwo: Shin ya
kiyaye hakan ko ya tozarta shi? Har sai ya tambayi mutum a kan iyalin gidansa.
(Sahih Al-Jaami’: 1774)
A taƙaice
dai: Ƙoƙarin
fahimtar juna da bai wa kowane mai matsayi matsayinsa ba tare da rage komai ba,
shi ne maganin irin waɗannan
matsalolin a tsakanin ma’aurata, in shà Allâh.
Don haka,
iyaye su zama masu haƙuri da juriyan bin abubuwa sannu kan hankali, tare da ƙoƙarin
kyautata zato da fahimtar juna a tsakaninsu, musamman ma dayake ga ’ya’yansu a gabansu waɗanda
suke son yi wa kyakkyawar tabiyya. Su riƙa neman bayani da ƙoƙarin
tattaunawa da fahimtar junansu a kan al’amura,
kuma su riƙa
yi wa maganganu da ayyukan junansu kyakkyawar fassara kafin su kai ga yanke
hukunci, ko kafin ma su sanar da waɗansu
a waje.
Allaah ya
datar da mu gaba-ɗaya
ga abubuwan da yake so kuma yake yarda da su na zantuka da ayyuka da ƙudurori.
WALLAHU
A'ALAM.
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi
Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/CfDLSdXaGD00Wpxdfy2ofp
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.