Daga cikin Waƙar Marigayi Mai Girma Dagacin Banga, Masarautar Ƙaura Namoda, Jihar Zamfara, Sarkin Yaƙi Sale Abubakar (wanda ya yi Sarauta daga shekarar 1934 zuwa wafatinsa a shekarar 1963), Ta Makaɗa Sa'idu Faru mai taken "Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi, Gamshik'an Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi.
Jagora :
Zama Giwa ta fito kiyo tai miƙa ta zo ta sha ruwa,
Y/Amshi :
Kuji Ɗan Zomo na hwaɗin hwaɗama su Tsari, Tsara mu tai gida
Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki,
Jagora/Y/Amshi :
Daji ya ɓaci kaa a take mutum baƙi aa' akwai ciki,
Jagora :
Gurnanin Damisa ka sa mahwarauta sun ɗora ɗemuwa,
Y/Amshi :
Ga wani ya yi Kokuwa da wan ƙarfi nai,
Ya hwaɗi ya kare,
Tun ba a tantance ba shi na nishi ya lank'wanshe tsara,
Jagora /Y/Amshi :
Tun dai ba a tantance ba shi na nishi ya lank'wanshe tsara,
Jagora :
Ko jiya na iske Gamdayak'i da Tuji sun iske Jinjimi,
To sun ko murd'a gardama,
Sun iske su Bubuk'uwa ruwa,
Y/Amshi :
Dan naan niko ina gaton gab'a,
Sai nik kwaɗa gaisuwa,
Su ko sun dak'ile ni dud,
Niko nik' ƙara gaisuwa,
Dan nan Kulmen da ac cikin gurbi ya amsa gaisuwa,
Jagora :
Dan nan sai Jinjimi da yad darzaza ya suntule shi dud,
Y/Amshi :
Shi ko Tuji da ad da girman baki yak kwashe Jinjimi,
Dan nan Bubuk'uwa da tar rura tag gangame su dut,
Jagora /Y/Amshi :
Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,
Ran nan nis san duniyag ga komi nane wani mayen wani,
Y/Amshi :
Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi,
Gamshik'an Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,
Gwabron Giwa Uban Galadima Ɗan Sambo Ginshimi,
Gamshik'an Amadu na Maigandi kai aa' Uban Zagi,
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.