𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Wai da gaske
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi kitso a kansa? Wane irin
ne ya yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laahi Wa Barakaatuh.
Abu-Daawud da At-Tirmiziy da Ibn
Maajah sun riwaito daga Ummu-Haani’ (Radiyal Laahu Anhumaa) ta ce:
« قَدِمَ النَّبِىُّ -صلى الله عليه وسلم- إِلَى مَكَّةَ وَلَهُ أَرْبَعُ غَدَائِرَ تَعْنِى عَقَائِصَ »
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ya iso Makkah alhalin yana da kitso gado huɗu a kansa. (Sahih
Abi-Daawud: 4191).
Al-Haafiz Ibn Hajr (Rahimahul
Laah) ya ce
فَحَاصِلُ الْخَبَرِ أنَّ شَعْرَهُ طَالَ حَتَّى صَارَ ذَوَائِبَ فَضَفَرَهُ أرْبَعَ عَقَائِصَ، وَهَذَا مَحْمُولٌ عَلَى الْحَالِ الَّتِي يَبْعُدُ عَهْدُهُ بِتَعَهُّدِهِ شَعْرَهُ فِيهَا وَهِيَ حَالَةُ الشُّغْلِ بِالسَّفَرِ وَنَحْوِهِ، وَاللهُ أعْلَمُ
Abin da wannan hadisi yake nunawa
a taƙaice
shi ne, gashin kansa ya yi tsawo ne har yana sauka a gaban goshinsa, don haka
sai ya kitse shi gado huɗu.
Wannan kuma ana ɗaukar sa a kan halin da ya yi nesa da kulawa da
gashin ne, kamar a halin shagaltuwarsa da matsalar tafiya ko makamancin hakan. Kuma
Allaah ne masani. (Fat-hul Baariy: 10/360).
Ya zo a cikin littafin Injaahul
Haajah a Haashiyah na Ibn Maajah cewa
لَعَلَّهُ فَعَلَ ذَلِكَ لِدَفْعِ الْغُبَارِ . انْتَهَى
Me yiwuwa ya yi hakan ne domin
kawar da tattaruwar ƙura ga gashin. Shikenan.
A kan haka ne Al-Mubaarakafuuriy
(Rahimahul Laah) ya ce
وَهُوَ الظَّاهِرُ لِأَنَّهُ - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - كَانَ فِي السَّفَرِ
Wannan kuma ita ce fassara ta
fili, domin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya kasance a cikin
halin tafiya ne a lokacin. (Tuhfatul Ahwaziy: 5/390).
Shiyasa malamai suka ce: Wannan
duk a babin al’adar larabawan zamaninsa ne, bai fita daga cikin hakan ba. Sannan
a cikin karantarwarsa bai sanya tsawaita gashin da yawaita shi har a samu daman
kitse shi, wani aikin samun lada ba, haka ma aske shi. Ya dai yi umurni ne
kawai cewa a karrama gashin idan ya yi yawa. (Sahih Abi-Daawud: 4165).
Amma idan zamani ko wuri ya sauya
ta yadda tsawaita gashin ko yawaita shi da kitse shi ya koma al’adar mata ne a
keɓance, to bai
halatta maza su yi koyi da su a cikin hakan ba. Haka kuma idan yin hakan ya
kasance wata alama ce da waɗansu
kafirai ko fasiƙai suka bambanta da ita, kuma har waɗansu wawaye suke koyi da su, to a nan ma bai
halatta masu mutunci su yi hakan ba, don gudun yin koyi da su.
Sananniyar ƙa’ida ce tabbatacciya a cikin
addini cewa, an hana koyi da mata a cikin tufafinsu da kwalliyarsu da sauran
abubuwan da suka keɓance
su. Saboda maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa
« لَيْسَ مِنَّا مَنْ تَشَبَّهَ بِالرِّجَالِ مِنَ النِّسَاءِ، وَ لَا مَنْ
تَشَبَّهَ بِالنِّسَاءِ مِنَ الرِّجَالِ »
Mai kamantuwa da maza daga cikin
mata ba ta cikinmu, haka ma mai kamantuwa da mata daga cikin maza. (Sahih
Al-Jaami’: 5433).
Haka ma koyi da kafirai da fasiƙai
da makamantansu ma bai halatta ba, domin maganarsa (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam), cewa
« لَيْسَ مِنَّا مَنْ تَشَبَّهَ بِغَيْرِنَا، لَا تُشَبِّهُوا بِالْيَهُودِ وَ لَا بِالنَّصَارَى
»
Mai kamantuwa da waɗanda ba mu ba, ba ya
cikinmu. Kar ku kamantu da Yahudawa ko da Nasara. (Sahih Al-Jaami’: 5434).
Haka kuma maganarsa (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa
« مَنْ تَشَبَّهَ بِقَوْمٍ فَهُوَ مِنْهُمْ »
Duk wanda ya kamantu da waɗansu mutane, to kuwa yana
a cikinsu. (Sahih Al-Jaami’: 6149).
Allaah ya ƙara mana fahimta.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat. whatsapp. com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.