Waƙar Ɗan Tauri Basare Shanawa, Shinkafi, Jihar Zamfara Ta Makaɗa Abubakar Amadu (Kassu Zurmi) Da Kirarin Ɗan Taurin( Basare). An ɗauki Waƙar a Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna a lokacin FESTAC 77 ( a cikin shekarar 1977)
Daure Karen Gado kai nak kawo ni,
Maganin maza na Jibo ɗan Zaki,
Mahaukaci na Nabanga zulma,
Nagode Marahwa ɗan Zaki ka kyauta,
Marahwa Iro ka nuna man iko,
Uhnn! Haliku Allah ya baku arzukkkan Tswahhinku,
Gagara dako Uban ɗan Anna,
Basaren gabas ga gulbin yamma Na Abdu,
Ɗan Isaka Na Nomau,
Basare dutcin hwashin tama Na Jibo ɗan Zaki,
Katakoron Cibau Daudu,
Na Abdu masu hwaɗan kashe kunya,
Na Gajo ko daji ya ci su,
Taro abin da dud ɗaki yas samu,
Sabad da dangarama yas same shi tun da dai ita nak kawo shi,
Mutane abin ɗaki baya samuwa banza,
Basare ɗan Isaka sai ƙohwa ta buɗe,
Yan Tauri ku riƙe ni gaskiyar Allah,
Yanzu Kassu na zan matatc tcara,
Aa' kaga muji baya son mu sai ran taron kunya,
Sai wani taro ƙato ya yi ko kuma taron Daba,
Kirari:
Ar Kassu ar Kassu,
Kiɗi yakai ga babbak'u na bakin lamba,
Anna waɗan da ba'a yada ma wuta,
Aradu gahwara wuta salamu alekum,
Kowak kwana lahiya shi yas so,
Kanhwai nike mugun bance,
Ƙaya nike babban ligido,
Allobah hannu tamburan a sa maki ɓawa,
Makarin mugu bakin daji,
Ni ak Kahiri Karen Nabanga zulma,
Ni ak Karen Marahwa jikan Sambo,
Kada in ƙara ji,
Kada in ƙara gani,
Ni ak Kahiri Karen Tudun Shanawa,
Asakon dare sai mai Kura,
Daidai mai Akuya ya ɗamre,
Zucciyam mutun birni nai,
Yan Tauri kowa yasan kowa yan tcelen uwag ga,
Gagarabadan dama da hauni,
Basare na Abdu annan koran yaƙi,
A tcarci maza kau akwai ranas su,
Ranak ku sai wuta sai a tara,
In an yi gobara ɗaki ya kama,
Kirari:
Ar Kassu ni ak Kanhwai mugun bance,
Ƙaya nike babbal ligidama,
Allobah hannu tamburan a sa maki ɓawa,
Makarin mugu bakin daji,
Ni ba kama ƙareri Uban ɗan Anna,
Kiɗi yakai ga babbak'u na bakin lamba,
Anna waɗan da ba'a yada ma wuta,
Ni ak Kahirin gabag ga gulbin yamma,
Ni ak Kahiri na yamma ga gulbin gabas Uban ɗan Anna,
Ni ak Kahiri Uban Yakubu,
Ni ak Kahiri Karen Tudun Shanawa,
Ni ak Kahiri na Cibau Daudu,
Asakon dare sai mai Kura,
Daidai mai Akuya ya ɗamre,
Zucciyam mutun birni nai,
Yan Tauri kowa ya yi mai hissai,
Anne bai sha Kiɗinmu kan banza,
Basare duk abun da niyyi nuhi ya bani,
Nayi godiya ga Nabanga zulma,
Ya bani turamen lailai,
Shi kau Marahwa ɗan Zaki ya kyauta,
Kirari:
Ar Kassu ni ak Kahiri Karen Sardauna gwamnati,
Ni ak Kahiri da yardar Allah,
Kowa Allah kawa hwaɗa bashi hwaɗa,
In rana ta hita tahin hannu baya ruhin ta,
In hwaɗa ya ɓaci sai wa da Ƙane,
Sai kau baran da yaj ji yag gani yash shaida,
Ni ba kama ƙareri,
Ni ba zuwa gida ɗai ɗai,
Ni dawaya kora,
Jama'a kowash sha Kiɗi abinai yab bai,
Latton Marahwa na bad' ɗinkin swace,
Bani ɗunko wando tunas,
Sai kaji an ce Marahwa ɗan Zaki ya bani,
Jama'a dai Allah shi maida Danda ga turkenta,
Yara in hali yak kama,
Yan kallon wuri kuce min amin,
Wanda dub bai ce muna amin ba damanab bana na kashe shi,
Amin! Amin!! Amin!!!
Kirari:
Yihuuuuuu!
Ar Kassu ance babban likita ya dawo,
Ina shirin cika shi da aiki,
Ni ag gata dawaya kora Uban ɗan Anna,
Ni ak Kahiri Musulmin yaƙi,
Ni ak Kahiri baran na Tabawa,
Ni ak Kahiri Karen Nabanga zulma,
Yan Tauri kowa yasan kowa,
Hannu baka da tsoro,
Maciji ba ayi ma zagi uban Ɗan Mowa,
Kassu albarkacin uban ɗan Anna,
Na Gajo duh hwadama tas sanni sabad dakai na Hassan da Husaini,
Ina godiya waɗan Gatawa,
Na koma godiya ga mutanen Turba,
Mun zarce sai Isa sai mun dawo,
Kirari:
Ar Kassu ni an na Abdu gako luddan Sarki,
Kowash sha dani ya ginsa,
Asakon dare sai mai Kura,
Daidai mai Akuya ya ɗamre,
Ni ah Faru ba'a hwaɗan sara ta,
Yan Tauri kowa niw wa nawa,
Koway yi man ya yi man uban ɗan Anna,
Ni ak Kahiri uban Ɗanbuzu,
Gabad da yamma an san gata,
Ni ak Kahiri na Cibau Daudu,
Ni ak Kahiri Karen Tudun Shanawa,
Karen Magaji mai Shinkahi,
Ni ak Kahiri na Malan Bello,
Shi ma Magaji ya nuna man iko,
Kassu ina godiya wurin Malan Ɗangwaggo,
Da Isah Rwahin daji,
Dangizgo yaron na Tabawa,
Mahaukaci na Jibo ɗan Zaki,
Basare ɗan Isaka masu hwaɗan kashe kunya,
Na Abdu ko daji ya ci su,
Gagarabadan dama da hauni uban Ɗan Twanka,
Basare na Gajo kaci maras sa kunya,
Dawo Karen Gado anna kai yaƙi,
Tauri ba banzaaa ba,
Ba banza ne ba yara kun ji Kiɗin ansar rai,
Kirari:
Ar Kassu ar Kassu,
Kace bismillahi La'ilahu Illallahu,
Ba Sarki sai Allah,
Ba Mala'ika awaj Jibirila,
Allah saini,
Allah saini Kassuwag ga ta gobe kassuwam mata ce,
Daji ko yaci ni ba'a ce man hoho,
Sai dai in nazo gida ace man barka,
Ni ag gata dawaya kora uban Ɗanbuzu,
Gabad da yamma an san gata,
Manya ban da cin amanab barwai,
Barwai ban da cin amanab Barwai,
Yan Tauri ku yi biya kuji daɗi,
Akwai magani ga dattab'ayye,
Kowab bi ta dattijo baya kunya daji,
Radda duk' ƙarhe yayyi man jak kama ina da jawabi ni da dattib'ayye,
Ni ak Kahiri Ƙanen Hura Yan Sanda,
Ni ak Kahiri Karen Barau na Sa'idu,
Ayyururrrrrrru!
Ayyyyihu!!
A tcarci maza kau akwai ƙaton ranas su wata rana,
Basare Sarki baya son ku sai daji ya ɓaci,
Kuwa salad dogo sai ya gama yace Alhandu,
Kuwa ba tawaye ba don gari ya ɗebe kewa,
Basare maganin maza na Hassan da Husaini,
Kirari :
Ar Kassu Ar Kassu
Ni ak Kahiri Karen Magaji mai Shinkahi,
Mu ab babbak'u mataka lamba,
Ni ak Kahiri Baturen yaƙi,
Ni ak Kahiri Nasaran yaƙi,
Ni aj Jamul ɓata ƙasa uban Yakubu,
Masu gari ku riƙe mu riƙon amanar Allah,
Nesa ta zaka kusa,
Komi ku kaso kun samu,
Na Katakare sai mai lura!
Na Katakare sai mai lura!!
Sai ran taron Daba,
Ɗan Isaka na Nomau,
Basare zakkaa awon maza na Hassan da Husaini,
Na Abdu masu hwaɗan kashe kunya,
Katakoron Cibau Daudu,
Basare na Abdu kaci mazaizai daji,
Zakkaa awon maza uban ɗan Anna,
Basare zakkaa awon maza uban ɗan Anna,
Basare maganin maza na Hassan da Husaini,
Uhmmmm!
Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.