Wakar Garin Kwaki Ta Shek Abubakar Atiku Sanka

    Waƙar Kwaki ta Shaykh Abubakar Atiku Sanka da almajirinsa Shaykh Balarabe Jaruna Jega, an rubuta waƙar a shekarar 1942 lokacin wata yunwa da akai a ƙasar Kano.
    1. Fana fara da sunan Jalla sarki
    Tabaraka wanda shi yab bamu kwaki

    2. Yasa muka zam musulmi jalla shine
    Ya aiko du Ma'aaika mai saraki

    3. Da tauhidi da addini kawimi
    Zuwa dukkan talakka har saraki 

    4. Ilahal arshi mai kudura irada
    Alimun Wahidun sarkin saraki

    5. Fa shine yai halitta kullihinta
    Hakimun wanda yai doki da Jaki

    6. Jamadun har Mala'ikku da jinnu
    Kazaka mutum da dukkan masu baki 

    7. Abin ruwa ne fa ko na cikin kasane
    Adan ikonsa yai kura da Zaki

    8. Sannan ya bukatashemu mu duk
    Zuwa neman abin sawa a baki

    9. Fa dabbobi ciyawa anka basu
    Mutane ko ya bamu hadi da kwaki

    10. Fa dabbobi ciyawa girman sarauta
    Muna dada godiya da ya bamu kwaki
             
    Haƙiƙaninsa

    11. Fa shi dai dan sarauta ne garinsu
    Adon haka bashi yawo shifa kwaki

    12. Izan ya so fita kuma za shi yawo
    Fa sai izni fa yazo gun yan saraki

    13. Suwo izni gareshi suwo
    Shiga jirgi nufi nasa kunji kwaki 
                   
     Fitowarsa daga garinsu 

    14. Da yayi nufin kano izini ya nema
    Ya hau jirgi yana sukuwassa kwaki

    15. Yazo kano ya sauka wurin Akawu
    Acan a tasha ya sauka kusan fa kwaki

    16. Da Talakawa da masu kudin gari du
    Suna tarbansa can a tasha fa kwaki

    17. Zuwansa Kano kusan yaki yazo yi
    Ya kawo taimako a garemu kwaki

    18. Kazo nan zan gaya maka dan uwana
    Fa girman kai ka daina yiwa su rogo kwaki

    19. Izan dai dukiya ce taƙamarka
    Fa Ɗantatan mu yai caffa ga kwaki  

    20. Izan kuma dan sarauta takamarka
    Fa ga sarkin Kano ya san da kwaki

               Saukar sa a Kano

    21. A zamani na Abdullahi yazzo
    Cikin birnin kano babban saraki 

    22. Cikin hijra alif da dari da maitan
    Da sittin sai guda daya munga kwaki 

    23. A zamani na Abbas yazzo fa amma
    Azamani na Usman babu kwaki  

    24. Ya sauka tasha yana khudba fa kullum
    Kuzo ku gareni nine rogo kwaki

    25. Mutane sun rijif sunje gareshi
    Suna caffa suna gaisheshi kwaki

    26. Da dattijai da yara yan ƙanana
    Da yan mata da masu zama a jaki

    27. Inyamuri har samari manya-manya
    Anan a kano suna ladabi ga kwaki

    28. Mutan Sabon gari da Fagge na gansu
    Suna rurubi wurin gaisar da kwaki.

    Halayensa da Ɗabi’unsa

    29. Fa shidai walla saukin kai gareshi
    Fa baya ja da kowa kunji kwaki

    30. Fa domin ko talakka sayo ya cishi
    Da sauki zaya cishi halinsa kwaki

    31. Akan samai ruwa fa kadan a cishi
    Ana ma hanfudashi kadai a baki

    32. Izan kuwa anka so wahala gareshi
    Fa sai yazamo abincin yan saraki

    33. Akan teba dashi da miya ta kwanbo
    Da man shanu da nama kanci kwaki

    34. Akwai ajabi cikin gari na rogo
    Abincin yan mutanan yamma kwaki [1]

    35. Fa yayi musharaka da hadin kasammu
    Kamar Gero da Dawa harda Wake

    36. Kazalika harda shinkafa hakannan
    Kamad da Alkama Doya yi kwaki

    37. Ana waina da Alkaki dashi har
    Akanyi Wasa-wasa dana rogo kwaki

    38. Izan an rafka taushe ankasa Mai
    Da nama ya zamo sai yan saraki

    39. Izan anso fura nono akan sa
    Adama ko da sukkar anci kwaki

    40. Akanyi Tuwo dashi a gama da Gari
    A tuke sai aci da Miya fa kwaki

    41. Akanyi tuwo na shinkafa a tuke
    Asa taushe fasai shagali da kwaki

    42. Ana Dambu dashi a gama da Ganye
    Akwai shi da martabobi rogo kwaki

    43. Ya kanyi fushi izan an bata ransa
    Barin ladabi  ka motsa fushin saraki

    44. Idan ka jikashi tun baka dakata ba
    Ya kumbura wanga shi ka fusata kwaki

    45. Izan ka shashi lallai zaiyi illah
    Cikin ciki sai ya kumbura yai na Jaki

    46. Su kwaki ai saraki ne hakika
    Fa wake yin irin mulkinsa kwaki ?

    47. Adon hakanan da zamaninsa yazzo
    Faba motsi gurin sauran saraki

    48. Su Gero sun fake hakanan su Dawa
    Adan sababin zuwan Babansu kwaki

    49. Su Wake ba mujin motsinsu su du
    Su Masra sun fake sun tsorci kwaki

    50. Su Rogo su Dankali duk sunka buya
    Faba'a ganinsu don tsoronsa kwaki

    51. Su Zogale sai ka barsu makaryata ne
    Su Tafasa du kazam ladabi ga kwaki

    56. Rama ma tayi karya tun a bara
    Adan haka sai ta buya da taji kwaki

    57. Sarautar tasa ba Kadhi da Joji
    Adon yaki yazo shi Rogo kwaki

    58. Walakin dai akwai ofis gareshi
    Cikin kwano yake mulkinsa kwaki

    59. Kuli-kuli shi kadai ya tsayawa daga
    Gurin sarkinsa shine madawaki

    60. Izan an nemi sulke sai fa mansa
    Akan yafa su gishirine Dawaki

    61. Su Barkono kusan sune mabusa
    Gurin yaki sukan zuga rogo kwaki

    62. Takobi cokaline babu shakka
    Da yatsu ne kibobin Rogo kwaki

    63. Idan damarunsa dun a yaki
    Nufinsa shigi cikin kofa ta baki

    64. Izan akasa ruwa bayan hakannan
    Fa bom kenan na Garin Rogo Kwaki

    Daga:
    Muhammad Tatuhu
    Zauren Makaɗa da Mawaƙa
    Wakar Garin Kwaki Ta Shek Abubakar Atiku Sanka

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.