Ticker

Wane Ne Mamman A Wajen Hausawa?

Kowane harshe na duniya yana da hanyoyi da yake amfani da su wajen isar da saƙo da sarrafa zance yadda masu amfani da wannan harshen za su fahimta. Masana ilimin walwalar harshe (SOCIOLINGUISTICS) sun bayyana yadda harshe yakan sauya daga lokaci zuwa lokaci, haka daga wuri zuwa wuri, sannan daga rukunin wasu mutane zuwa wani rukunin.

Amfani da wani suna ko wata kalma mai kyakkyawar ma'ana zuwa wata ma'anar ta daban walau mai kyau ko maras kyau, yana ɓangaren ilimin HAUSAR RUKUNI (SOCIOLECT).

Sanin kowa ne, Hausawa suna matuƙar girmama sunan MUHAMMAD kasancewa suna ne na Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama. Wannan sunan ne suka sanya gudumar harshe suka mayar da shi Mamman, ko Mammada, ko Muhamman da makamantan haka.

Zan buga misalai da rukunin masu wasu sanao'i a yankin ƙaramar hukumar Sabon Gari ta Jihar Kaduna., Yadda suke amfani da wasu kalmomin rukuni domin ankarar da junansu wani abu. Ga misalin kamar haka:

1. Masu sayar da waya a PZ: Suna amfani da kalmar HAJIYA da nufin tsohuwar waya da ta sha wahala (idan an kawo ta a matsayin kwancen sabuwa).  Idan kuma ta ragargaje suna ce mata JAGWAL.

2. Masu sayar da takalma a gindin Rimi (kasuwar mata) suna amfani da kalmar ƘARFE da nufin wanda ya zo taya kaya ba domin ya saya ba.

Wannan misali ne kawai.

SUNAN MAMMAN KUMA FA?

Kamar yadda aka bayyana a baya, wannan suna ne mai matukar daraja a wajen Hausawa da ma duk wani musulmi. Duk da haka, kasancewar harshe yana da walwala, hakan bai hana Hausawa sarrafa shi da wata manufar ba, amma ko kaɗan hakan ba ya nufin izgili ko wulakanci ga sunan.

Ga wasu misalai na yadda Hausawa suka sarrafa sunan Mamman.

1. KARIN MAGANA: Hausawa suna cewa "ƁARAWON DA BA A KAMA SHI BA, SUNANSA MAMMAN"

wannan na nufin, Mamman mutumin kirki ne a asali, kuma abin yabo.

2. HAUSAR RUKUNI A SABON GARIN ZARIYA.

A) 'YAN WIWI: masu shaye-shaye a dabar Garban Ladi da Man Salis a yankin Tsauni da Tsugugi idan sabon-shigan shan WIWI ya zo suna ce masa MAMMAN.

wannan na nufin mutumin kirki ne wanda ƙafarsa take so ta zame.

B) MABARATA: Naƙasassu da suke zaune a layin Lagos Street Sabon Gari suna amfani da sunan MAMMAN ga mutumin da yake mai kuɗi amma marowaci (wanda ba ya ba su sadaka)

C) KARUWAI: Rukunin karuwai da 'yan Daudu suna amfani da kalmar MAMMAN ga wanda yake sabon-shiga a harkar.

D) 'YAN ACAƁA: Wasu daga cikin 'yan Acaɓa na ƙofar gidan Iya suna amfani da sunan MAMMAN ga mutumin da yake bayar da saƙon cefane a kai masa gida amma ba ya biyan kuɗin mashin ko kuma ba ya sa nama a cefanen.

Wannan misali ne na yadda Hausawa suke sarrafa sunan Mamman da manufa daban-daban.

Abin tambaya a nan shi ne; shin ko sarrafa wannan suna yana nufin wulaƙanta mai sunan?

A ilimin harshe, har ma a fagen addini, wannan ba zai zama wulaƙanci ga wannan suna ba, domin kowane aiki da niyyarsa. A ilimin walwalar harshe kuwa, masu amfani da harshe suna da cikakkiyar damar sarrafa harshensu yadda za su fahimta. Domin haka, ko kusa wannan ba ya nuna ƙasƙanci ga wannan suna.

Sai dai a babin ladabi, abin da ya fi dacewa, shi ne a ƙauracewa amfani da wannan suna a duk wata sadarwa ko mu'amala da take abar zargi ko maras kyau. Wannan suna ne na mafificin halitta, domin haka zai fi dacewa mu mutunta sunan kuma mu san mahallin da ya dace mu yi amfani da shi.

BA WANI NAKE KAREWA BA. FAHIMTA FUSKA.

Allah ya datar da mu da daidai.

Imrana Hamza Tsugugi
7th November, 2023

Tambaya

Post a Comment

0 Comments