𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Mun yi soyayya
da budurwata6 amma a ƙarshe sai ta auri wani, ni kuma na auri wata. A yanzu kuma
bana jin daɗin zama
da wacce na aura, ita ma haka. To, ko zai iya yin addu’ar Allaah ya fitar da
tsohuwar budurwarta daga gidan wancan mijin domin na aure ta?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul
Laah
1. Da farko: Lallai ya san cewa,
yana daga cikin Imani da Ƙaddara ya amince tun daga zuci har baki zuwa ga gaɓoɓinsa cewa: Duk abin da ya same shi, da ma
can ba a ƙaddara
cewa zai kuskure masa ba. Haka kuma duk abin da ya rasa shi, to da ma can ba a ƙaddara
cewa abin zai same shi ba ne. An gama rubuta komai na ƙaddara tun shekaru dubu
hamsin (50,000) kafin a halitta duniya, an ɗauke
alƙalamin
rubutun kuma takardun sun bushe.
2. Na-biyu: Bayan an ɗaura wa tsohuwar
budurwarsa aure da wani, babu sauran alaƙa a tsakaninsa da ita. Don haka haram ne
ya riƙa
hira da ita ta waya ko kuma ta wata hanyar kamar ya zauna da ita suna hira a
wani wuri, ko da me, ko don me. Kai! Ko komawa da yin bincike a kan yadda take
rayuwa a cikin gidan mijinta ma bai kamace shi ba.
3. Na-uku: Wajibi ne iyaye da
waliyyan ma’aurata su daina barin masu neman auren juna suna ƙulla
soyayya da shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu, ta yadda rabuwa zai zama musu alaƙaƙai
daga baya. Kodayake a galibi su masoyan ne suke ƙulla soyayyar a tsakaninsu ba tare da
sanin iyaye ko manya ba. Amma dai dole a hana su, a ja musu kunne a duk lokacin
da aka gano hakan, musamman ma idan an san ba za a amince da aurensu ba.
4. Na-huɗu: Lokacin da aka aura mata wani mijin, shi
kuma aka aura masa wata matar, to abin da ya kamace su shi ne haƙuri
da juriya kawai, tare da addu’ar
fatan ɗorewar zaman
lafiya da fahimtar juna a tsakanin kowannensu da abokin zaman aurensa. Sai kuma
yin tsayin daka domin gyara zaman iyalinsu a halin da suka samu kawunansu da
gwargwadon ƙarfi da iyawa.
5. Na-biyar: Babu wata addu’a a
tsakaninsu sai ta fatan alkhairi da neman Allaah ya sanya wa kowannensu albarka
a cikin rayuwarsu ta duniya da barzahu da lahira, ita ma sai in ta zama dole.
Amma neman wai Allaah ya fitar da ita daga gidan wancan mijin domin shi kuma ya
aure ta, wannan ba daidai ba ne. Domin dalilai kamar haka
(i) Ana iya shiga haƙƙin
wancan mijin da aka ɗaura
mata auren da shi, haka ma haƙƙin ’ya’yanta
idan Allaah ya sa suna da su. Rabuwarsu a irin wannan halin kuwa cutarwa ce
gare su.
(ii) Soyayyar da ake samu kafin
aure ba lallai ta zama irinta za a samu a cikin gidan auren ba. Don haka babu
tabbacin ko da ta fito ya aure ta cewa, za su samu jin daɗin zamantakewa a
tsakaninsu.
Daga ƙarshe: Abin da ya
kamata dai kawai shi ne: Ya cigaba da addu’ar Allaah ya daidaita tsakanin shi da matarsa ta gida,
ya sanya albarka da fahimtar juna a tsakaninsu. Amma kar ya kuskura tunanin
waccan tsohuwar budurwar ya dame shi, har ma wataƙila ya kai shi ga taimaka mata don ta
rabu da mijinta. Domin idan ya sanya hanunsa ko bakinsa ko shawararsa a cikin
hakan, to ya aikata mummunan haram. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ya ce
« مَنْ خَبَّبَ خَادِماً عَلَى أَهْلِهَا فَلَيْسَ مِنَّا، وَمَنْ أَفْسَدَ امْرَأَةً عَلَى زَوْجِهَا فَلَيْسَ هُوَ مِنَّا »
Duk wanda ya lalata wata baiwa a
kan masu ita ba ya tare da mu. Haka wanda ya lalata wata mace a kan mijinta shi
ma ba ya tare da mu. (Ahmad ya riwaito shi. Kuma Al-Albaaniy ya sahhaha shi a
cikin As-Saheehah: 324-325).
Amma idan ta su ta haɗa su a tsakaninta da
mijin, kuma ya sake ta don zaɓin
ransa, ba tare da sanya hannu ko bakinsa a ciki ba, to a nan yana iya neman
aurenta, a bayan ta gama idda.
Allaah ya ƙara mana shiriya.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.