Ticker

Auran Yar Karamar Yarinya

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Ina fatar Allah ya kara ma Mallam Ikhlasi. Ya halatta idan mutum ya auri mace karama wadda ba ta fara jini ba ya sadu da ita? Kokuwa rainonta zai yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa a alaikumassalam,

Malamai sun cimma daidaito game da halaccin aurar ‘yar karamar yarinya, saboda ayata huɗu a suratu Addalak ta bada labarin yadda karamar yarınya za ta yi idda

وَاللَّائِي يَئِسْنَ مِنَ الْمَحِيضِ مِنْ نِسَائِكُمْ إِنِ ارْتَبْتُمْ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَاثَةُ أَشْهُرٍ وَاللَّائِي لَمْ يَحِضْنَ ۚ وَأُولَاتُ الْأَحْمَالِ أَجَلُهُنَّ أَنْ يَضَعْنَ حَمْلَهُنَّ ۚ وَمَنْ يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَلْ لَهُ مِنْ أَمْرِهِ يُسْرًا

Kuma waɗanda suka yanke ɗammãni daga haila daga mãtanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu watã uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma´abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, ( Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al´amarinsa.

Hakan sai ya nuna ingancin yi mata aure kafin ta balaga, sannan Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya auri nana Aisha tana ‘yar

shekara shida.

Malamai sun yi saɓani game da lokacin da za a fara saduwa da ita, bayan anyi auren, akwai waɗanda suka tafi akan cewa dole sai ta balaga za a mikata ga mijinta. Wasu malaman sun kayyade shi da shekara (9) saboda Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya tare da nana A’isha ne bayan ta kai shekaru tara.

Zancen da yafi zama daidai shi ne : za a duba yanayin jikin

yarinyar, in har za a iya jima’i da ita ba ta cutu ba, za a iya mikata ga mijinta, ko da shekarunta kaɗan ne, saboda mata suna bambanta wajan girman jiki gwargwadon wurin da suke rayuwa, da kuma irin abincin da suke ci, sannan sharia ba ta iyakance lokacin da ake fara jima’i da mace ba.

Don neman karin bayani duba: AlMugni 27/77 da kuma Alminhaj na Nawawy 9/206.

Allah ne mafi sani

Dr.Jamil Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/CQ9TMXMrWDx1y7sYye2znU

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments