Ticker

6/recent/ticker-posts

Biyayyar Mahaifi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Wan mahaifinsa ne yake ɗaukar nauyin al’amuransa tun yana ƙarami, amma ba mahaifinsa da ya haife shi ba, wanda ba ya samun komai daga wurinsa sai hantara da kyara! Yanzu dai ya gama makaranta har kuma ya samu aiki. Yayan mahaifin ya amince da neman auren da ya fara, amma shi mahaifin bai amince ba. Shi ne yake tambaya wai ko zai iya ƙin bin maganar mahaifin?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah

Haƙƙin mahaifa (uwa da uba) a kan yaya ba ƙarami ba ne. Shiyasa Allaah Taaala ya haɗa shi da haƙƙinsa, kamar a inda ya ce

وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا ، إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِنْدَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ، وَلَا تَنْهَرْهُمَا، وَقُلْ لَهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا

Kuma Ubangijinka ya hukunta cewa: Kar ku yi bauta ga kowa sai dai gare shi, kuma iyaye biyu a kai matuƙa wurin kyautata musu. Idan ɗayansu ya kai lokacin tsufa a tare da kai, ko su duka biyun, to kar ka ce musu tir! Kuma kar ka raina su, amma ka faɗa musu magana ta darajawa. (Surah Al-Israa’: 23).

Don haka, bai halatta ya bijire ko ya kangare wa mahaifinsa ba, domin wai shi mahaifin bai kula da haƙƙoƙinsa a lokacin da yaron yake ƙarami ba.

Inda kawai yake da daman saɓawa shi ne a lokacin da mahaifin ya umurce shi da saɓo. Ubangiji Ta’aala ya ce

وَإِنْ جَاهَدَاكَ عَلَى أَنْ تُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ فَلَا تُطِعْهُمَا ، وَصَاحِبْهُمَا فِي الدُّنْيَا مَعْرُوفًا ، وَاتَّبِعْ سَبِيلَ مَنْ أَنَابَ إِلَيَّ ، ثُمَّ إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُمْ بِمَا كُنْتُمْ تَعْمَلُون

Kuma idan suka yi ƙoƙari a kanka domin ka yi tarayya da ni cikin abin da ba ka da ilimin shi, to kar ka yi musu biyayya, kuma amma ka zauna da su a duniya a cikin alheri da aka sani, kuma ka bi hanyar mai mayar da alamari gare ni. Sannan a ƙarshe dai zuwa gare ni ne makomarku, sai in ba ku labarin duk abin da kuka kasance kuna aikatawa. (Surah Luqman: 15).

Don haka, idan rashin auren zai iya cutarwa ga yaron, kamar idan zai iya aukar da shi ga yin zina, to a nan ba za a yarda ya bi umurnin mahaifin ba, domin maganar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa

« لاَ طَاعَةَ فِى مَعْصِيَةِ اللَّهِ إِنَّمَا الطَّاعَةُ فِى الْمَعْرُوفِ »

Babu ɗa’a a cikin saɓon Allaah, ana yin ɗa’a ne kaɗai a cikin sanannen abin da ya dace da shari’a. (Sahih Muslim: 4871).

Har a hakan wajibi ne ya cigaba da kyautatawa gare shi, sannan kuma ya bi maganar wan mahaifin shi, matuƙar dai ya san wannan auren kariya ce gare shi daga afkawa a cikin zunubi da saɓon Allaah.

Allaah ya datar da mu ga daidai.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments