Ticker

6/recent/ticker-posts

Cin Hanci Kafin Samun Matsayin Aiki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Mutum ne ya samu gurbin kai wanda za a ɗauka wani aikin gwamnati, amma sai ya sanya sharaɗin cewa, wanda ya kai sunansa kuma ya samu aikin sai lallai ya ba shi waɗansu kuɗaɗe da ya yanke. Menene hukuncin irin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alaa Alihi Wa Sahbihi Wa Sallam) ya ce:

« مَنِ اسْتَعْمَلْنَاهُ عَلَى عَمَلٍ فَرَزَقْنَاهُ رِزْقًا فَمَا أَخَذَ بَعْدَ ذَلِكَ فَهُوَ غُلُولٌ ».

Duk wanda muka ɗauke shi aiki kuma muka ba shi albashinsa, to duk abin da ya ɗauka ko ya karɓa a bayan hakan sata ne. (Sahih Abi-Daawud: 2943).

Don haka bayar da cin hanci kafin samun matsayin aiki a gwamnati haram ne. Haka ma karɓar cin hancin.

Bayan wannan, bayar da dama ga wani babban mutum don ya kawo wanda ya cancanta a dauke shi a wani gurbi na wata ma’aikatar gwamnatin siyasa nau’in girmamawa ne. Don haka bai kamata wanda aka ba shi irin wannan matsayin ya zubar da girmansa, ya koma neman kuɗi daga yaron da yake ganinsa a matsayin babban wa ko uba ba a gare shi. Wannan zubar da mutunci ne, kuma ba girmansa ba ne.

Irin wannan shi ke sa ma’aikacin ya zama mara gaskiya mara riƙon amana a kan aikin nasa. Yana zama a kan kujerar ofis dole ka ga ya kama hanyar ciwa-ciwa da almandahana domin ƙoƙarin mayar da maƙudan kuɗaɗen da ya biya kafin a ba shi wannan matsayin. Don haka irin waɗannan manyan su ne ummul haba’isin cigaba da lalacewar al’ummarmu har zuwa yau.

Duk waɗannan matsalolin na tsaro irin na Boko Haram da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da sauransu da ake fama da su a yau, tushensu da abin da ya hana su mutuwa a cikinmu shi ne irin waɗannan almundahana da cin hanci da rashawa da suka yi wa ma’aikatan hukuma katutu. Duk wanda ya samu wata dama a ko’ina kuma a koyaushe ƙoƙarinsa kawai ya tafka mummnar sata kawai da gwargwadon iyawarsa kafin ya sauka ko a sauke shi!

Wannan ya janyo a yau masu kishin ƙasarmu da kishin alummarta da kishin makomar zuriyarmu suka yi ƙaranci sosai a cikinmu. Maƙiyan ƙasarmu kuma sai murna suke yi da irin wannan halin namu a ciki da wajenta. Ana biyan wasu manyan maaikata maƙudan kuɗaɗen da suka shige tunaninsu, domin su kau da ido ko su janye jiki, ko kuma ma su ba da dama a tafka mummunar ta’asa a ƙarƙashin ikonsu. Domin rufe ɓarna ana iya hallaka jama’a masu ɗimbin yawa, ko a tayar da husumar da za ta yi ajalin dubunnai. Duk kuwa da cewa akwai manya masu ikon faɗa-a-ji a cikinmu! Laa Haula Walaa Quwwata Illaa Bil Laah.

Wannan shi zai nuna girman sharrin da ke ƙunshe a cikin irin wannan almundahanar da waɗansu tsofaffin kuraye da manyan shugabannin da suka yi ritaya suke tafkawa.

Wannan zalunci ne mummuna. Bai halatta ba.

Allaah ya tsare mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments