Da Tsohuwar Zuma...: Fasalta Narambaɗa da Shata da Ɗanƙwairo ga Matasan Yanzu
Daga
Alhaji
Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji)
Faɗar Mai Martaba Sarkin Birnin-Magaji (Ɗan Alin
Birnin-Magaji), Jihar Zamfara.
Lambar Waya: 08149388452
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Tsakure
Arewacin Nijeriya wani yanki ne a ƙasar Hausa da ya haɗa tarin fasihai ta ɓangaren makaɗa da mawaƙa. Mafi yawanci suna gwada hikimarsu cikin
harshen Hausa. Da wannan masaniyar aka nemi gwarazan
mawaƙa uku (3)
waɗanda aka yi ittifaƙin hikimominsu da zalaƙa irin tasu a awon baka, ta yi zarrar da babu
mai tababa. Bayan dogon shaƙo
wajen nazarin rayuwar mawaƙan
baka, an so a ƙara bayani ga ayyukan
da magabata suka yi kan Narambaɗa, domin mu
taya shanu ciri. An dai fahimci har yanzu akwai buƙatar a ci gaba da nazari a cikin waƙoƙin tsofaffin mawaƙan baka na Hausa, domin a yaba da ƙwazonsu, a kuma amfana da tarin hikimomin da
suka naɗe
a cikin waƙoƙinsu.
Fitilun Kalmomi: Matasa, Ɗanƙwairo, Shata, Narambaɗa
Gabatarwa
Ɗimbin
ayyukan da aka sha cin karo[1]
da su, da shirye-shiryen da hukumomin wayar da kan jama’a[2]
sun kasance abin dogaro wajen fahimtar waƙoƙin baka da mawaƙan baka na Hausa. Masana sun yi tarayya
wajen amincewa kan waƙoƙin baka da mawaƙan baka sun zama rumbu wajen adana tarihin kowace alumma. Haka nan mawaƙa suka zama tsani wajen wayar da kan
jama‟a da ilmantarwa. Dawannan
masaniyar wannan tattaunawa ta
zama
babuya tamka ga zaɓo
manyan mawaƙan
baka guda uku domin tattaunawa kan fasihanci.
A ɗan
tsakuren da za a gabatar kan Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali, an nemi ƙarin
haske kan waƙoƙin da ya gabatar daga ‘yan
uwansa da masoyansa, da kuma masu sauraren waƙoƙinsa domin bayar da gudummuwa ga
nazarin wannan mashaurin mawaƙi. Wasu waƙoƙi da aka yi tsokaci a kansu a cikin wannan maƙala, sun fara nisa a hannun manazarta,
wato ma’ana
mafi yawa daga cikin waɗanda suka yi sharhi kan waƙoƙin Narambaɗa
ba su yi
tsokaci ko sharhi a kansu ba. Mai
yiwuwa hannuwan waɗannan manazarta ba su kai gare su ba.
Wannan maƙala
ta zama tamkar cike giɓi ga ayyukan
magabata. Waɗannan
waƙoƙi za a kawo su a shafin rataye domin
nazari. Kafin tsunduma a cikin aikin zan faɗi
wane ne Narambaɗa a takaice. Sa’annan zan kawo waƙoƙi guda uku (3) waɗanda
Narambaɗa ya
rera, amma a tunaninmu suna
neman salwanta a hanun mutane saboda ba a samu ayyukan da suka ruwaito su tare da yin sharhi a kansu ba. Akwai bayanin taƙaitawa
da shafin manazarta bayan an yi makimancin
sharhi kan waƙoƙin.
Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali
Akwai Tarihin rayuwa da waƙoƙin Makaɗa
Ibrahim Narambaɗa Tubali a cikin Littafi mai suna Narambaɗa
wanda Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya wallafa. Yana da kyau ɗalibai
su karanta wannan wallafa kan Narambaɗa domin a fahimci
wane ne Narambaɗa da kuma sharhi kan waƙoƙinsa da gudummuwarsa ga harshen Hausa
ta fuskar adabi da al’ada
da kuma harshe. Littafi ne mai shafuka dari shida da biyu (602).
Akwai kuma wata maƙala da mai wannan tsokaci ya taɓa
gabatarwa kan Narambaɗa, wadda a cikinta an yi ƙarin
haske kan rayuwarsa kamar haka Birnin Magaji, I. (2019) “Makaɗa
Ibrahim Narambaɗa a Fadojin ƙasar Hausa” Takardar da aka gabatar a taron ƙasa
da ƙasa kan Makaɗa
Ibrahim Narambaɗa Tubali.
Wasu Daga Cikin Waƙoƙin IbrahimNarambaɗa
Waƙoƙin da za a gani a ƙarƙashin wannan rukuni an same su a
hannun mutane daban-daban[3].
An zaɓi waɗannan
waƙoƙin su zama misalan da za a yi tsokaci a kansu, saboda
bitar wasu ayyuka[4]
game da rayuwar Narambaɗa da waƙoƙinsa da aka yi, aka fahimci ba a
ambaci waɗannan waƙoƙin ba. Waɗannan waƙoƙi ga su kamar haka:
Waƙar Sarkin Musulmi Abubakar na Uku (III) (1938-1988)
Ita wannan Waƙar ana tunanin an gabatar da ita ga jama’a shekaru saba’in (70)
da suka wuce. An yi waƙar
ne domin gwarzanta Mai Alfarma Sarkin Musulmin Daular Usmaniyya Alhaji Abubakar
na Ukku (III). Alhaji Abubakar III shi ne Sarkin Musulmi na goma sha-bakwai,
kuma ya yi shekaru hamsin (50),
matsayinsa a cikin al’ummarsa,
ya sa. Narambaɗa
ya shiga cikin jerin Makaɗan
wannan shugaba na al’umma mai tarin daraja da ɗaukaka[5].
Waƙar Makaman Sakkwato Alhaji Sani Dingyaɗi (19??-1963)[6]
Wannan waƙa Narambaɗa
ya gabatar da ita a shekarun 1950[7].
Kasancewar sarautar makama babbar sarauta daga cikin jerin sarautun da ke
taimaka wa Sarkin Muslmi, ya sa Narambaɗa ya waƙe
mai sarautar. Shi dai Alhaji Sani Dingyaɗi an naɗa
masa wannan sarauta a shekarar 1952. Kafin naɗa
shi wannan sarauta, ya riƙa muƙamai
kamar Ajiyan Sakkwato da kuma Kansila a Majalisar Sarkin Musulmi. Alhaji Sani
Makaman Sakkwato mutumen
ƙasar
Dingyaɗi ne wadda ke ƙarƙashin Ƙaramar
Hukumar Bodinga ta jihar Sakkwato a yanzu. Matsayin wannan Sarauta a daular
Usmaniyya shi ne a
nan ana iya cewa Narambaɗa
ba karamin mawakin fada
ba ne, domin ma fi yawa daga cikin waɗanda ya waƙe
shahararrun Sarakuna ne.
Waƙar Magajin Garin Isa, Madugu Ɗan Hassan (1930-1933 da 1950-1960)[8] Wannan waƙa an gabatar da ita a shekarar 1940. Sarautar Magajin Gari babbar Sarauta ce a kowace
masarauta ta ƙasar Hausa. Wanda aka bai wa muƙamin Magaji na daga cikin masu taimaka wa Sarkin Musulmi
wajen tafiyar da masarautarsa da mulkinsa. Kuma yana riƙon masarauta idan Basarakensa ya yi tafiya,
haka nan yana daga cikin masu zaɓen Sarki idan sarautar gari ta faɗi. Sarkin Gobir Muhammadu Na’ammani shi ne ya naɗa Madugu Ɗan Hassan bayan shekaru uku sai ya cire shi daga Sarautar saboda rashin jittuwa da ta shiga
tsakaninsu. Sarkin Gobir Ahmadu Bawa I, shi
ne ya sake mayar da Ɗan Hassan kan mulki a matsayin Magajin Garin Isah.
Bunza, (2009: 34) ya bai wa Narambaɗa
matsayin makaɗin sarauta ganin irin gidajen Sarauta
da Sarakunan da ya yi wa waƙa. Marubucin ya sake tabbatar da hakan a inda ya bayyana waƙoƙin da Narambaɗa
ya yi wa Sarakunan Maraɗi
da Sarakunan ƙasar
Zazzau, duk sai da suka nemi izini daga Sarkin Gobir na Isa domin shi Narambaɗa
ya dauru ga gidan Sarautar Isa a matsayin mawaƙinsu.
3.1 Dangantakar Narambaɗa
da Shata da Ɗanƙwairo
ta Fuskokin da suka haɗa da Yawan waƙoƙi da Salailai
Rukunin Mawaƙa Fitattun ayyuka kan Shata[9] da Narambaɗa[10] da Ɗanƙwairo[11] duk sun shaidar da ba a san
iyakacin waƙoƙin da waɗannan bayin Allah suka
samar ba a rayuwarsu. Su kansu Makaɗan sun shaidar da hakan da bakinsu a lokutta daban-daban
da aka yi hira da su. A nan ba sai an je da nisa ba, ta fuskar waƙoƙi, dukkaninsu sun yi waƙoƙi da yawa.
Akwai Salailai da yawa da Mawaƙan suka yi tarayya wajen aiwatar da
su, akwai kuma inda suka bambanta. Misali:
Narambaɗa
da Ɗanƙwairo sun yi tarayya wajen yanayin
tsara Waƙarsu ta fuskar ‘yan’amshi domin
‘yan
amshinsu ana kiransu‘yan karɓa-karɓa, ma’ana Ubangida (jagoransu) yana fara rera ɗan
waƙa
yaransa suna cika masa, wato suna ida rera sauran sashen ɗan
waƙar. Idan za a kwatanta yanayin yadda ‘yan amshin Shata ke amsa masa tasa waƙar,
sai a ga cewa suna rera abin da ubangidansu ya
faɗa ne na farko, ko kuma abin da ya umurce su da amsawa. Amshin ‘yan amshin Shata, yana ɗaya
daga cikin kason ‘yan amshi na waƙoƙin baka. Misali a waƙar
Malam Babba na ƙofar Gabas, ‘yan amshin Shata suna
rera “Malam Babba na kofar Gabas” a matsayin amshin waƙar.
Salon amfani da kiɗa
da salon amfani da ‘yan amshi duk salailai ne a waƙar
baka. Wasu
mawaƙan
baka ba su da ‘yan amshi, kamar yadda wasu ba su waƙa da kiɗa
sai dai taɓi (tafi)[12]
a nan mawaƙan
sun yi tarayya a salon amfani da kiɗa
da kuma waƙa.
Akwai
salon koɗa kai wanda mawaƙan guda uku suka yi tarayya a kai. Misali, a waƙar Hajiya
Halimatu Usman Nagwaggo Katsina (Kilishi) wadda Shata ya rera kamar haka:
A.
Jagora: Da sauya waƙar Kilishi Jikkar Dikko,
Yara suna ta dukan fata,
Kiɗan
sai ka ce fitar harsashi.
‘Yan
amshi: Ranar Kilishi Jikan Dikko Jagora
Zuba
waƙa
nikai,
Ni sai zuba waƙa nikai, kama da ta
Alfazazi, Kamar ana tamsiri.
‘Yan amshi:
Ranar Kilishi Jikar Dikko
Jagora: Zuba waƙa nikai kama da ta
Alfazazi,
Kama ana Alburda
‘Yan
amshi: Rana Kilishi Jikar Dikko
(Gindin
waƙa:
Ranar Kilishi Jikkad Dikko)
Alhaji
Mamman Shata Katsina
Ita dai Kilishi (Hajiya Halimatu)
Babbar mace
ce, domin ɗiyar Sarkin Katsina, Alhaji Usman
Nagwaggo ce, ta kuma auri Sarkin Daura, Alhaji Muhammadu Bashar tun yana Wamban
Daura a shekarar 1964. Kilishi ƙanwa
ce ga Janar Hassan Usman Katsina (Ciroman Katsina). Hajiya Kilishi tana da danganta da manyan mutane da dama a
arewacin Nijeriya. A wannan waƙa
ta ce Dr. Mamman Shata ya gwarzanta kansa da Alfazazi. Waƙar
da ke biye wato Bakandamiyar Narambaɗa, Narambaɗa
ya danganta
kansa da Alfazazi. Alfazazi kamar
yadda sunan ya nuna, ba Bahaushe ba ne, ga bayaninsa nan biye kamar yadda za mu
gani.
Waƙar Ibrahim Narambaɗa
shi ma ya yi wannan kamancen kamar haka:
B.
Waƙar Sarkin Gobir na Isa Ahmadu I
Jagora:
Kullum ji nikai azanci na hudo min,
In
wani ya hi ni martaba,
Ni kau na hi wani,
Ai
kyawon mafarauci,
Ya dau kare ya yi kiwo shi yah hi
……………………………………
Jagora:
Ni ko kun gane ni na gyare turuna,
‘Yan amshi:
Sai zuba waƙa nikai kama da ta
Alfazazi,
Gwarzon
Shamaki na Malam toron Giwa, Babban Dodo ba a tamma da batun banza. (Bunza,
2009:350)
Bakandamiyar
Narambaɗa: Gindin Waƙa: Gwarzon Shamaki na Malam Toron
Giwa, babban Dodo ba tamma da batun banza
C
Ɗanƙwairo bai ambaci Alfazazi ba a cikin waƙoƙin da ya koɗa kansa da kansa ba,
amma ga nasa ƙaulin nan a waƙe. Misali:
Jagora: Batun kiɗi,
Ko
ba ku nan yi mukai,
Kun
karantar da mu,
Mun
yi kiɗan baƙi,
Mun yi wasilla,
Mun
yi ta yi,
Yanzu
ilmi mukai tunda mun sabka,
In
hwa waƙa
ta,
Don
mun san yadda za mu kulla ta,
Jagora/’Yan’amshi: In an ce mutum mai tujara ne,
Sai ya haihwa ɗa mai tujarannan,
Jagora:in an ce mutum ga shi samna ne,
Jagora/’Yan’amshi: Sai ya haihwa
samna haƙiƙanne,
Jagora: In Allah ya wa mutum ƙwazo,
Jagora/’Yan’amshi: Ya bah haihwa ɗa nai ya lalace,
Tun
da gado ne,
Jagora: Mun gani tun ga ɗiyan masara,
Jagora/’Yan’amshi: Ga abu goye kowa da gemenai,
Gindi Waƙa Shirya Kayan Faɗa mai gida Tcahe,
Ali ɗan Iro bai ɗauki reni ba[13]
A
ɗan waƙar da ke sama Musa Ɗanƙwairo ne ke bayyana kansa ta hanyar danganta fasaharsa da ta kakaninsa. Ya yi amfani da salon siffantawa inda ya kawo hoton rabon mutane a cikin al’ummarsa da ɗiyan
masara wadda bututunta tana goye da ɗiya
da yawa, amma kowane ɗan masara yana da wasu zaruruwa tamkar
gemu. Wato wannan misali na ɗiyan masara sai
aka danganta shi da mutane a matsayin al’umma ɗaya
amma kowa da halayyarsa. Misali akwai
mutanen da halayyarsu ta tujara[14]
ce, wasu kuma samnoni ne, wasu kuma lalatacci ne, wasu kuma masu ƙwazo
ne. Magabatan Musa Ɗanƙwairo tun daga kakaninsa su masu ƙwazo
ne, saboda haka da bazar magabatansa yake ta rawarsa domin ɗan-na-gada ne.
Danganta
Shaharar Shata da Narambaɗa da Abu-Zaidi AbdurRahaman Ibn Yaktalafan Ibn
Ahmad Alfazazi
An haifi Alfazazi a garin Fez ta ƙasar Morroco, a shekarar 1230AH. Waƙarsa mai suna Alwusa’i ta yabon fiyayyen Halitta Annabi
(SAW) wato Ishiriniyar Alfazazi ita ce ta fitar da shi a duniya. Ba ɓoyayyen
abu ba ne a ƙasar
Hausa, duk wani al’amari
wanda ya shafi yabon Annabin Rahama
tun daga haihuwa har zuwa yau, to ba
abin wasa ba ne. Bayanai na Annabi SAW ba su da tamka wajen ƙima
ga jama’ar
musulmi ko’ina
suke ba ma na yankin Arewacin Nijeriya
kaɗai ba. Shaharar da Ishiriniyar
Alfazazi ta yi, shi ne ya fitar da sunan mawallafinta wato Abu-Zaid ibn Ahmad. Har ya zuwa lokacin da ake rubuta wannan maƙala, ba a kammala gardama ta ilmi ba
kan wane ne ya fi shahara tsakanin
Shata da Narambaɗa da Ɗanƙwairo ba. Hasali ma, gardamar ta fi tsananta a tsakanin masoya Narambaɗa da
Shata.Wannan wataya ra‟ayi a
ilmance, ya ƙara
fito da fasihancin mawaƙan, da fitar da wasu bayanai a kan
rayuwarsu daga iyalansu da masoyansu domin nazari da tambihi daga manazarta da
masu sauraro. Shata da Narambaɗa suna ganin shahararsu a wajen waƙa da matsayin waƙoƙinsu ga jama’a, tamkar Shaharar Alfazazi ne ga duniyar musulmi da kuma karɓuwar
waƙoƙinsu ne ga jama’a tamkar
Alburda ko Ishiriniya.
Ƙarin shahara da koɗa
kai ya sake fitowa ta bakin Makaɗa
Ibrahim Narambaɗa a wata waƙa da ya
shirya mai suna Dokin Iska Ɗanhilinge.
Waƙar Ɗanhilinge a
sharhin Bunza (2009:
326),
akwai
dokin da ake kira Dokin Iska Ɗanhilinge
wanda aka sawo daga garin Filinge na jihar Maraɗi
domin yin wasan sukuwa. Dagacin Kware wadda a da ke a ƙarƙashin tsohuwar gundumar Isa amma a
yanzu gunduma ce a masarautar Shinkafi ta jahar Zamfara, shi ne ya fara mallakar wannan Doki. Sarkin Gobir
na Isa Ahmadu I ( Ahmadu Bawa 1935-1975) ya
mallaki wannan Dokin na Ɗanhilinge
a lokacin da Dagacin Kware ya yaba
da ƙwazon dokin ya aika masa da shi (Ɗanhilinge). Wannan shahara da Narambaɗa
ke bayyanawa a cikin Waƙar
Dokin Iska ba ta kai haka nan ba. Wannan waƙa da gwarzanta dokin Narambaɗa
ya shirya ta ne domin a sake bayyana
martabar Sarkin Isa Ahmadu I (Ahmadu Bawa 1935-1975), da irin ƙarfin
Ikonsa. Amma wasu ɗaliban Nazari
suna ganin akwai wannan doki kuma ya shahara
wajen tsere wa sauran dawaki a lokacin da duk aka fita wasan sukuwa. Ɗanhilinge ya shekara goma sha biyar (15) ana sukuwa da shi kuma yana samun
nasara, kusan tsakanin waɗannan shekarun ba a taɓa
samun wasar da dokin ya shiga ba,
bai yi nasarar lashe gasar ba[15].
Abin lura a nan shi ne, akwai Dokin Iska Ɗanhilinge, kuma an yi sukuwa da shi ya ciyo kyautttuka da yawa. Dokin gwarzon doki ne. Ɗanhilinge ya tsufa har ya bar sukuwa. A shekarar 1964 dokin ya mutu a hannun mahayinsa Malam Ibrahim Dattijo.
4.0 Takaitawa
Da
Narambaɗa da Shata da Ɗanƙwairo duk shahararrun mawaƙan baka ne a Arewacin Nijeriya. Masoya waƙoƙin waɗannan Makaɗa
suna da yawan gaske. Nazarin rayuwa da ƙumshiyar waɗannan
mawaƙa
zai kawo tarin ilmi ga ɗaliban adabi da
kuma masu sauraron waƙoƙin. Ƙarin
bayani kan abin da ya gabata shi ne,
waƙoƙin waɗannan
fasihai suna da tarihe-tarihe na dauloli da mutane da garuruwa da sarakuna da sana’o’i da
al’adu da halayyar jama’a. Babu wanda zai nemi tarihin ƙasar Hausa ya same shi cikkakke ba tare
da nazarin ƙumshiyar waƙoƙinsu na baka ba, domin waƙoƙin baka su ne rumbun adana tarihin kowace al‟umma.
Manazarta
1. Bunza, A. (2009) Narambaɗa,
Ibrash Islamic Publication Centre.
2. Birnin Magaji, I. (2021) “ƙasar Zamfara a Bakin Makaɗa
Alhaji Musa Ɗanƙwairo”, an gabatar da wannan Maƙala a Taron kasa da kasa na kara wa
Juna ilmi kan rayuwa da gudummuwar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun, wanda Cibiyar nazarin
harsunan Nijeriya da aikin Fassarata
Jami‟ar Bayero
ta
Kano ta Shirya.
3. Birnin Magaji, I. (2019) “Makaɗa
Ibrahim Narambaɗa a FadojinƙasarHausa” Takardarda akagabatarataronƘasadaƘasaKanMakaɗaIbrahimNarambaɗaTubalAJami‟arBayero Kano Ranar 15-17 ga Watan Satumba,
2019.
4. Ɗanjuma,
M.S. (1982) “Gudummuwar Waƙoƙi ga Rayuwar Bahaushe” Takardardaya Gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Kano: Jami‟arBayero.
5. Gusau, S. (1984) “Nazarin Zababbun Waƙoƙin Baka na Hausa” Cyclostyled Edition,
Kano Department of Nigerian Languages, BayeroUniversity.
6.
Gusau,
S.M. (1988) Waƙoƙin Makaɗan
Faɗa: SigoginsudaYanaye-yanayensu. Kundin Digiri
na Uku: Kano Jami‟ar Bayero, shafi na170-177
7. Gusau, S. (1996) Makaɗa da Mawaƙan Hausa, Bench Mark Publishers, Kano
8.
Gusau,
S. (2014) Waƙar Baka Bahaushiya, Bayero University, Kano Inaugural Lecture no 14.
9. Gusau, S. M. (2019) Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Hudu
Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun (1909-1991), Century Research and Publishers,
Kano.
10. Longman, (2003) Active Study Dictionary, Edinburg Gate
11. Sani, A. R. (2019) “Nazarin Salo a
Cikin Wasu Waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo Maradun”, Kundin Digiri na Biyu,
Usmanu Ɗanfodiyo,
Sakkwato.
12. Sheme, I da wasu
(2006) Shata Ikon Allah, Madaba‟ar Informant, Kaduna Nijeriya.
13. Tambuwal, I. (2002) “The Facinating
Emirates of Zamfara State, Matani kan Tarihin Masarautun Zamfara” da ke Jiran
Dab‟i. A Publication of Zamfara State
Council of Chiefs.
Ratayen Wasu Waƙoƙin Makaɗa Ibrahim Narambaɗa
A-
Waƙar
Sarkin Musulmi Abubakar
Jagora: Rinjayayye Dattijo na Gatau,
Abubakar
Uban Sarakuna
‘Yan
amshi: Tattaki Maza ɗan
shehu na gatau,
Abubakar
uban Sarakuna
Jagora:
Garba na Alhaji Sha da arna makaye,
‘Yan
amshi: Garba na Alhaji tura Haushi Ɗan Hassan
Jagora:
Garba na Alhaji Sha da arna makaye
‘Yan amshi:
Garba na Alhaji Sha da arna ɗan Hassan,
Jagora:
Namijinƙwazoginshimin
Magajin Rwahi
‘Yan
amshi: Garba ya biya kidi
Ya
ban doki Abu na Amadu
Jagora:
Rinjayi maza ɗan Shehu na Gatau
Abubakar
Uban Sarakuna
Jagora:
Da Bauchi da Kano da Katchina da Adamawa kai muka dibi,
‘Yan
amshi: Dama da hauni Shehu ad da su shi ag gaba shi am Mujaddadi ta tabbata Sakkwato maza suke,
‘Yan
Amshi: Tattaki
maza ɗan Shehu na Gatau Abubakar Uban
Sarakuna
Jagora:
Tattaki maza ɗan Shehu na Gatau Abubakar
UbanSarakuna
‘Yan
amshi: Tattaki maza ɗan
Shehu na Gatau Abubakar Uban Sarakuna
Jagora:
Ɗan
Shehu Uban Gazobi, Ka
yiƙwazoAllah
yayyi ma gudummuwa
‘Yan
amshi: milkin ga da Shehu yayyi ka yi shi
Jagora:
Ɗan
Shehu Uban Gazobi ka yi ƙwazo,
Allah
yayyi ma gudummuwa
‘Yan
amshi: Milkin da Mu‟azu
yayyi ka yi, shi
Jagora/‘Yan
amshi: Duk milkin da Mu‟azu yayy i ka yi
shi,
Tattaki
maza ɗan Shehu na Gatau,
Abubakar Uban Sarakuna
Jagora:
Da kai wanga mai hakon Giwadiba,
‘Yan
amshi: Ta take hakon da kayyi tawuce,
Jagora:
Da kai wanga mai hakon Giwadiba,
‘Yan
amshi: Ta take hakon da kayyi ta wuce,
Jagora:
Kai diba kissa, Kai ji munahucci,
Diba
wane in za ya gaisuwa,
‘Yan
amshi: in ya zamna, Makyarkyata yakai,
Jagora:
Ai diba Kissa,
Ka
ji munahucci diba wane in za ya gaisuwa
‘Yan
amsh: In ya zanna makyarkyata ya kai,
Bai
san muni garai ba ba an sani,
Tattaki
maza ɗan shehu na Gatau,
Abubakar
Uban Sarakuna.
Jagora:
Garba na Alhaji shada arna makaye,
‘Yan
amshi: Garba na Alhaji tura Haushi ɗan
Hassan.
Jagora:
An ce mana wane ya ci ya kihe,
‘Yan
amshi: Ya ɗangana
sai bidaw wurin gudu
(Alhaji Ummaru Mai Sa‟a, 1974)
B-
Waƙar
Magajin Garin Isa Madugu Ɗanhassan
Jagora:
Na sani tana haka,
Na
zo gaida ɗan Hassan, Allah ya baka MagajinIsa
‘Yan
amshi: Na sani tana haka,
Na
zo gaida ɗan Hassan,
Allah
ya baka MagajinIsa
Jagora:
Magaji cirin Giwa
Ba
dai da cirin Shanu ba
‘Yan
amshi: Giwa in tai girgiza,
Sai
ka ji duk dawa ta amsa
Jagora:
Magaji Atsatsageni buzu ne,
Bai
san maganas Sarki ba
‘Yan
amshi: Na sani tana haka,
Na
zo gai da Ɗan
Hassan Allah ya baka Magajin Isa
C-
Waƙar
Makaman Sakkwato Alhaji Sani Dingyaɗi
Jagora:
Makama Amintacce kake,
Kowag
gaka,
Ya san yagaka.
‘Yan
amshi: Makama Amintaccekake,
Kowag
gaka, ya san yagaka.
Jagora:
Kullum rokon Allahmukai,
‘Yan
amshi: Ya aza maka girman duniya,
Makama
amintacce kake,
Kowag
gaka ya san ya gaka
[1] Wallafaffun
Litattafai, da kundayen bincike da mukalu kan mawaƙan baka da waƙoƙin baka
[2] Shirye-shiryen
gidajen rediyo da na Talabijin na jihohin arewacin Nijeriya
[3] Sarkin Gobir na Isa na yanzu, Alhaji Nasiru Usman Ahmad II, da Alhaji
Ummaru mai Sa’a (Mai rera waƙoƙin Narambaɗa bayan da shi Narambaɗar yayi wafati), da Alhaji Attahiru Ahmad I (Ahmad Bawa).
[4] . Akwai kundin Jerin tarin Makalu waɗanda aka gabatar a Jami’ar Bayero ta Kano domin tunawa da karrama
Narambaɗa. Akwai Littafin
Narambaɗa wanda Farfesa
Aliyu Muhammad Bunza ya wallafa a shekarar 2009 mai suna Narambaɗa
[5] Na samu wannan bayani a bakunan
Alhaji Lawal Isah da Malam Sanda Adamu Tsafe. Alhaji Lawal da Malam Sanda, sun
samu wannan bayani a bakin Alhaji Ummaru mai Sa’a a lokacin da suka tattauna da
shi a giɗan Rediyo
Nijeriya na Kaduna a ranar 8/11/1974. Malam Ummaru mai Sa’a shi ne halifan Marigayi Makaɗa Ibrahim Narambaɗa.
[6] Ban samu shekarar da
aka haifi Makama Alhaji Sani Dingyaɗi ba, amma na san ya
rasu a shekarar 1963.
[7] An samu bayanai kan
wannan Waƙar a hannun Sarkin Gobir na Isa Alhaji Nasiru Usman Ahmad
II a lokacin da na kai ziyarar neman bayanai. Alhaji Nasiru Usman Ahmad II jika
ne ga Sarkin Gobir na Isa, Ahmadu I (Ahmadu Bawa). Haka nan mun sake tattaunwa
da Alhaji Attahiru Ahmad I, wanda da ne ga Sarkin Gobir na Isa, Ahmadu I
(Ahmadu Bawa) a ranakun 21/9/2019 da 13/7/2021.
[8] An naɗa shi Magajin Garin Isa a 1930, bayan shekaru uku a 1933 aka sauke shi. Aka sake naɗa shi a cikin shekarun 1940 ya ci gaba har lokacin rasuwarsa.
[9] Sheme, I. da
Kankara, A. da Aliyu, M. da Yusuf, T. (2006) a littafin Shata Ikon Allah, Madaba‟ar Informant
[10] Bunza, A. (2009) Narambaɗa, Madaba‟ar Cibiyar Musulunci
ta Ibrash.
[11] Birnin Magaji, I. (2021) “Ƙasar Zamfara a Bakin Makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo”, an gabatar da wannan Maƙala a Taron kasa da kasa na kara wa Juna ilmi kan rayuwa
da gudummuwar Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun, wanda Cibiyarnazarin
Harsunan Nijeriya da aikin Fassara ta Jami‟ar Bayero ta Kano ta Shirya.
[12]MarigayiShamsuPooryayiwaAlhajiUmmaruMusa’Yar‟aduwawaƙaalokacindayakeGwamnan Katsina, kafin ya zama shugaban ƙasar Nijeriya. Akwai Waƙar Shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida wadda Garba Gashuwa ya rera da tafi. Alhaji Amadu Mailauni Bakura ya fara gabatar da waƙoƙinsa na farko-farko da tafi a shekarun 1970.
[13] Waƙar ‘Yandoton Tsafe Alhaji Aliyu (1960 – 1991), an nade wannan Waƙar a Giɗan Rediyon Rima da ke Sakkwato , 20 ga watan
Apirilu 1995, a lokacin ina aiki a Giɗan Rediyon a matsayin jami‟i mai farauto labarai.
[14] Mutum matujarci yana
nufin mafaɗaci, mai yawan satiru, da yajin magana
a maimakon magana ta ladabi da lumana. Mai tujara yana iya zama hatsabibi wanda
ba ya son zaman lafiya.
[15] An samu
wannan bayani a shirin Jiya Ba Yau Ba na Giɗan Rediyon Nijeriya na ranar 14/01/2018 da na ranar
21/1/2018, inda Malam Muhammed Magaji Sayaya ya tattauna da Mahayin Dokin Ɗanhilinge, Malam Ibrahim Dattijo Isa. Malama Ibrahim Dattijo ya warware Zare
da Abawar tarihin Dokin Iska Ɗanhilinge
da yadda aka kawo shi a giɗan
Sarkin Gobir na Isa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.