𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Iyayena ne
suka ɗauki nauyin
karatuna har ga shi yanzu ina aiki a gidan mijina. Kowane wata ina taimaka musu
daga albashina, mijina kuma ina yi masa hidimar da ta fi haka. To menene
hukuncin wannan ɗin
a addini?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Ɗaukar nauyin karatu da iyaye suka yi miki
wannan wani haƙƙi ne na ki a kansu da suka yi ƙoƙarin saukewa kafin zuwan mijinki. Kuma
wajibi ne ki kyautata musu a yau, domin sakayya a gare su, da kuma girmamawa da
martabawa gare su a matsayinsu na iyaye, musamman ma idan suna cikin buƙatar
irin wannan taimakon.
Amma a bayan aure miji shi yake
da haƙƙi
mafi girma a kan mace fiye da iyayenta. A cikin hadisi Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗi
cewa
لَا يَصْلُحُ لِبَشَرٍ أَنْ يَسْجُدَ لِبَشَرٍ
، وَلَوْ صَلُحَ لِبَشَرٍ أَنْ يَسْجُدَ لِبَشَرٍ ، لَأَمَرْتُ الْمَرْأَةَ أَنْ تَسْجُدَ
لِزَوْجِهَا ، مِنْ عَظْمِ حَقِّهِ عَلَيْهَا وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ ، لَوْ كَانَ
مِنْ قَدَمِهِ إِلَى مَفْرَقِ رَأْسِهِ قُرْحَةٌ ، تَجْرِي بِالْقَيْحِ وَالصَّدِيدِ
، ثُمَّ اسْتَقْبَلَتْهُ فَلَحِسَتْهُ ، مَا أَدَّتْ حَقَّهُ
Ba ya kyautatuwa ga wani mutum ya
yi sujada ga wani mutum: In da zai kyautatu wani mutum ya yi sujada ga wani
mutum, da na umarci mace ce ta yi sujada ga mijinta, saboda girman haƙƙinsa
a kanta. Ina rantsuwa da Allaah wanda raina ke hannunsa! In da a ce tun daga
tafin ƙafafuwansa
har zuwa ƙoƙoluwar
kansa miji ne yana zubar da ruwan ciwo da jini, kuma sai matar ta tashi ta
sanya harshe ta lashe shi kaf, da kuwa ba ta biya haƙƙinsa ba! (Sahih
Al-Jaami’: 7725).
Bai faɗi irin wannan game da iyayen mace ba.
Kuma akwai hadisin Waathilah Bn
Asqa’i (Radiyal Laahu Anhu), daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya ce
لَيْسَ لِلْمَرْأَةِ أَنْ تَنْتَهِكَ شَيْئًا
مِنْ مَالِهَا إِلَا بِإذْنِ زَوْجِهَا
Bai halatta ga mace ta bayar da
wani abu daga dukiyarta ba sai da izinin mijinta. (As-Saheehah: 775).
Bai faɗi irin wannan ma game da iyaye ba.
Don haka dai duk da kasantuwar
iyaye suna da matsayi mai girma, amma kuma miji shi ma ba a baya ya ke ba.
Lallai mace ta san wannan kuma ta ɗauki
matakin bai wa kowane sashe haƙƙinsa ba tare da tawayewa ko naƙasa komai
ba.
Wannan shi ne adalci.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta
WhatsApp number: 08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.