𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Ba na son
shiga makewayi (toilet) na cikin ɗakina
da dare, don haka sai na ajiye wani ɗan
bokiti wanda ni da yara muke yin fitsari a ciki. Shi ne nake son jin ko
musulunci ya amince da hakan?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Babu laifi ga hakan matuƙar
dai fitsarin ba zai fantsalu ya ɓata
jiki ko tufafi ko wuraren zama ba. Domin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ya faɗa
game da waɗansu
mutum biyu da suke kwance a cikin ƙabrukansu cewa
إنَّهُمَا لَيُعَذَّبَانِ وَ مَا يُعَذَّبَانِ
فِي كَبِيرٍ، أَمَّا أَحَدُهُمَا فَكَانَ لَا يَسْتَنْزِهُ مِنَ الْبَوْلِ، وَ أَمَّا
الْآخَرُ فَكَانَ يَمْشِي بِالنَّمِيمَةِ
Lallai ne azaba ake yi musu. Amma ba ana yi
musu azaba a kan wani babban abu ba ne. Ɗayansu dai ba ya tsarkaka ne daga
fitsari. Ɗayan
kuma yawo yake yi da gulma a tsakanin jama’a. (Sahih Al-Jaami’: 2440).
Sannan kuma ya tabbata a cikin
hadisin Umaimah Bint Ruqayyah cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) yana da wani kwano kamar akushi da yake yin fitsari a cikinsa a cikin
dare
كَانَ لِلنَّبِىِّ -صلى الله عليه وسلم- قَدَحٌ
مِنْ عَيْدَانٍ تَحْتَ سَرِيرِهِ يَبُولُ فِيهِ بِاللَّيْلِ.
Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) yana da wani kwano na katako da yake yin fitsari a cikinsa,
yana ajiye shi a ƙarƙashin gado. (Sahih Abi-Daawud: 19, Sahih An-Nasaa’iy: 32).
Wannan fitsarin ne wata mace mai
suna Barakah ta zo ta shanye shi watarana. Da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi
Wa Sallam) ya nema bai gani ba kuma aka sanar da shi cewa, ai Barakah ta shanye
shi sai ya ce:
لَقَدِ احْتَظَرَتْ مِنَ النَّارِ بِحِظَارٍ
Lallai ta tsare kanta daga Wuta
da babbar kariya. (Al-Mu’ujam na Ibn Al-Muqri’: 138, masu tahqeeq na littafin sun
ce riwayar sahihiya ce).
Allaahu Akbar!
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta
WhatsApp number: 08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.