Arrr!
Wai maganar banza da wohhi!
Na ce, sarkin Gwandu,
An yi shari'am Musulunci an aza ta,
Mallammai nat tare ta,
Su nah hana ta ci gaba,
Na ce, sarki halan ka mance, sadda ina farkon kiɗin ga,
Na ce, kwas san Ƙur'ani irina,
Duniyagga uban wa za ya tsoro?
Na ce, sarki shari'am musulunci Mallamai nah hanata,
Su nat tare ta,
Ba karuwai nat tare ba,
Ba masu marisa nat tare ba,
Ba masu kalangai nah hana ba.
Sai sarki ya dibi Gambo.
Na ce, malamai ka gane su can haka!
Su nat tare ta.
Na ce, zan ba ka dalili,
Na su nat tare ta,
Su na rarraba,
In masu izala za su ja gaba,
Masu darik'a ba su yarda,-
'Yan sha'a ba su yarda.
Na ce, in 'yan shi'a za su ja gaba,
Masu izala ba su yarda,
masu. . .
To sun rarraba, yaushe shari'ah za a yinta sarki?
Banda batun banza da wohhi!
Su shirya kansu,
Sannan shari'a in za a yinta. . .
Umar S Ahmad Chairman
30-11-2014
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.