𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Shin ko ya halatta Musulmi ya
karbi abincin kirsimeti yaci?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Alalhaƙiƙa an
samu saɓanin Malamai
dangane da hukuncin musulmi yaci abincin da Ahlulkitabi (yahudawa da kiristoci)
sukayi dan saboda murnar wani biki daga cikin bukukuwansu kamar misalin irin
bikin kirsimeti.
Wato asali dai ya halatta idan
kafiri ya bawa musulmi kyauta ya karɓa,
domin hakan na iya janyo hankalinsa ya sanya shi yaji yana sha'awar musluncin,
kamar yadda aka ruwaito cewa Mαnzσn Allαh Sallallahu alaihi Wasallam yana karɓar kyautar da kafirai
suka ba shi. Haka nan asali ya halatta musulmi ya bawa kafiri kyauta musamman
ma da nufin janyo hankalinsa zuwa ga muslunci, amma bai halatta ba musulmi ya
bawa kafiri wata kyauta a ranar idin su (kafirai) ko bukukuwansu, domin yin hakan
kamar yayi taimakekeniya ne a kan shirkar da sukeyi, haka nan ba ya halatta ga
musulmi ya bawa ɗan'uwansa
musulmi wata kyauta a ranar da kafirai suke idinsu (bukukuwansu) idan ya ba shi
ne da nufin taya kafirai murna a wannan ranar da kuma girmama wannan bikin da
sukeyi.
Haka nan ba ya halatta ga musulmi
ya sayarwa da kafirai dukkan wani abinda za su yi amfani dashi na shirka awajen
bautarsu.
To sai dai Malamai sunyi saɓani game da kyautar da
kafiri ze yiwa Musulmi a ranar wani biki daga cikin bukukuwansu kamar ranar
kirsimeti. Wasu daga cikin Malamai sukace babu laifi Musulmi ya karɓi kyautar da kafiri yayi
masa a ranar kirsimeti amma da sharadin ya kasance abinda a kayi kyautar da shi
dama asali halal ne a wajen musulmi yayi amfani da shi, sukace karɓarsa ba ta nufin cewa ya
yarda da abin da sukeyi, haka nan kuma karɓar
kyautarsu ba ta nufin an temake su akan shirkarsu ba, sai dai abin lura a nan
shi ne, Malaman da sukace ya halatta a karɓi
kyautar kirsimet to suna magana ne akan abinda ba yanka ba ne, wato suna magana
ne akan kamar abincin da suka dafa ko 'ya'yan itatuwa da makamantansu.
Amma idan suka yanka wata dabba
da nufin bikin idin su (kirsimet) to bai halatta musulmi ya ci ba, duk da cewa
asali a shari'ance ya halatta a ci yankansu kuma a auri matansu, to amma a nan
ya zama haramun ne saboda sunyi yankan ne da nufin wannan bikin na su.
Sai dai kuma a gefe ɗaya akwai Malaman da
sukace haramun ne musulmi ya karɓi
dukkan wata kyauta da wani kafiri zai ba shi a ranar idinsu (kirsimet), kuma ko
da mene ne in dai an yi shi ne ko an tanadeshi saboda wannan rana ta kirsimet
to bai halatta ya karɓa
ba, waɗannan Malamai
sukace idan Musulmi ya karɓi
kyautar kafiri a ranar idinsa, to kamar yayi taimakekeniya da aikin ɓarna ne.
Sannan kuma girmamawace a garesu
da ƙarfafarsu
akan suci gaba da yi da kuma tayasu murna da farin ciki a kan ɓarnarsu.
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.