𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan Zan Yi Wankan Janaba Da
Juma'a Alokaci Guda Ya Ya Zan Yi Niyyar Kowane? Zan Yi Niyyar Alokaci Guda Ne?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Idan wankan Janaba da Juma'a suka
Haɗu akan mutum,
wanka ɗaya ya isar
masa, sai ya yi niyyar wankan janaba da na Juma'a baki-daya. Saboda fadar
Annabi tsira da amincin Allah suqara tabbata agareshi:
(إنما الأعمال بالنيات وإنما لكل امرىء ما نوى)
Bukhari (1) da Muslim (1907)
Ma'ana " Dukkan ayyuka suna
tattare da niyyoyi"
Imam Annawawi ya ce acikin Majmuu
(1/368) Da'ace mai wanka zai yi niyyar wankansa na Janaba da juma'a baki-daya wannan
ya inganta"
Ibn Qudamah Allah ya yi masa
rahama yace : "idan yayi wanka ɗaya
na Juma'a da Janaba yayi masu niyya ɗaya,
ya isar masa, ba mu san wani saɓanin
malamai ba akan haka"
An tambayi Sheikh Ibn Uthaimin
Allah ya yi masa rahama: mene ne hukuncin hada wankan Juma'a da na Janaba?
Sai ya amsa da cewa: "Wannan
babu laifi, idan mutum ya kasance mai Janaba sai ya yi wanka yayi niyyar dauke
Janaba da kuma wankan juma'a babu damuwa cikin wannan, kamar yadda idan mutum
ya shiga masallaci yayi nafila raka'a da niyyar raka'o'in da ake yi kafin
kowace Sallah ta farilla da kuma raka'a biyun da ake duk lokacin da mutum ya
shiga masallaci (TAHIYYATUL MASJIDI) to babu komai akansa.
Wannan mas'ala ba ta wuce
wadannan rabe-raben guda uku (3)
1. Yin niyyar wankan Janaba kaɗai.
2. Yin niyyar wankan Janaba da
juma'a.
3. Yin niyyar wankan Juma'a kaɗai.
Idan kayi niyyar wankan Janaba ya
isar maka akan wankan juma'a idan ya kasance bayan hudowar rana ne, idan kuma
ya yi niyyarsu baki-daya Ya isar masa kuma ya samu ladarsu baki ɗaya, idan ya yi niyyar wankan
juma'a to ba ya Isar masa ga wankan Janaba, domin wankan juma'a wajibi ne ga
maras hadasi, shi kuwa wankan Janaba wajibi ne akan mai hadasi don haka babu
Makawa akan yin niyyar ɗauke
wannan hadasi.
Wani bangare na malamai sukace:
"zai yi wanka sau biyu ne" sai dai wannan zancen ba ya da madogara
Majmu'u Fatawa Ibn
Uthaimin(16/137)
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.