Hukuncin Kai Wa Kiristoci Ziyara Da Yi Masu Kyauta A Ranar Kirsimeti

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. Shin ya halasta musulmi yayiwa kirista kyauta aranar kirsimeti? Kuma Menene hukuncin musulmai wadanda suke zuwa musamman sukaiwa kiristoci ziyara aranar Kirsimeti?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Toh asali gameda yiwa arne kyauta shine  ya halasta. Amma yin musu kyauta aranar bikinsu kamar shi wannan kirsimetin to Malamai na sunnah inka duba Hashiyyar Ibnu Abidin juzu'i na 6 shafi na 754 malamai suka ce idan asali dama kasaba yin musu kyauta to seya ranar kirsimetice ta zago to baya halasta kabasu wannan kyautar a wannan ranar inkuma kabasu to ka aikata babban zunubi. Inkuwa A'a baka saba basu kyautaba kawai hakanan musammasan ka nufaci kaimusu kyautar a wannan ranar to wasu malamai sukace ka bar addinin musulinci kuma shine fatawar mafi yawan malamai dana gani, amma wasu sunce baka zama arneba amma dai ka aikata babban zunubi.

    Ibul Qayyum ya ce daidai da ganyen dabino baya halasta kabasu matukar cewa inka basun zezamanto ka taimaka musune akan wannan bikin nasu. Aduba Attaju wal iklil juzu'i na 4 shafi na 319

    asali dai halal ne musulmi yakaiwa arne ziyara musamman kuma idan yazamana cewa ziyarar tashi zaijene da zummar yin musu wa'azi da kiransu zuwaga addinin musulinci to wannan abune mekyau kwarai da gaske kuma Malamai sun halastashi. Amma mutum ya tashi musamman yakai musu ziyara don tayasu murnar kirsimeti ko wani bikinsu na kafirci to wannan kuma haramunne kuma taimakonsune akan aikinda sukeyi na saɓo .

    Allah Yasa mudace

    ✍️ Jameel A Haruna

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.