TAMBAYA (94)❓
Dan Allah meye gaskiyar wannan
addu'ar
🔥🔥 Ga wata Mai zafi. "ADDU'A SAUKAKAKKA MAI DUMBIN LADA". Manzon Allah (SAW) ya ce: Duk wanda ya karanta wannan addu'ar, koda sau guda ne a rayuwarsa, Allah zai ba shi ladar aikin Hajji 360, da ladar 'yanta Bayi 360, da ladar sadaka da dirhami 360, da ladar saukar Al-Qur'ani 360, da kuma ladar ya ye wa Bayi 360 bakin ciki da kuncin rayuwarsu.
Manzon Allah (SAW) na fadar haka
ke nan, sai ga Mala'ika Jibrilu yazo gare shi yace: Ubangiji Allah (SWT) Ya
rantse da ikonSa da mulkinSa, ga duk wanda ya karanta addu'ar nan a cikin
Al'ummarka koda kuwa sau guda ne, Allah
Zai lamunce masa abubuwa guda bakwai:
1. Zai raba shi da talauci.
2. Zai kiyaye shi daga tambayar
Munkar da Nakir.
3. Zai kiyaye shi daga kuncin
kabari.
4. Zai haramta mashi shiga wutar
Jahannama.
5. Zai kiyaye shi daga mutuwar
gatsali
6. Zai bashi damar keta siradi a
saukake.
7. Zai tsare shi daga fushin
shugaba azzalumi maras adalci.Bismillah
ﻻﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠَّﻪ ﺍﻟﺠﻠﻴﻞ ﺍﻟﺠﺒﺎﺭ
ﻻﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠَّﻪ ﺍﻟﻮﺍﺣﺪ ﺍﻟﻘﻬﺎﺭ
ﻻﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠَّﻪ ﺍﻟﻜﺮﻳﻢ ﺍﻟﺴﺘﺎﺭ
ﻻﺍﻟﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻜﺒﻴﺮ ﺍﻟﻤﺘﻌﺎﻝ
ﻻﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﺍﻟﻬﺎ ﻭﺍﺣﺪﺍ ﺭﺑﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﺍ ﺍﺣﺪﺍ ﻭﺻﻤﺪﺍ ﻭﻧﺤﻦ
ﻟﻪ ﻣﺴﻠﻤﻮﻥ
ﻻﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﺍﻟﻬﺎ ﻭﺍﺣﺪﺍ ﺭﺑﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﺍ ﺍﺣﺪﺍ ﻭﺻﻤﺪﺍ ﻭﻧﺤﻦ
ﻟﻪ ﻋﺎﺑﺪﻭﻥ
ﻻﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﺍﻟﻬﺎ ﻭﺍﺣﺪﺍ ﺭﺑﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﺍ ﺍﺣﺪﺍ ﻭﺻﻤﺪﺍ ﻭﻧﺤﻦ
ﻟﻪ ﻗﺎﻧﺘﻮﻥ
ﻻﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﺍﻟﻬﺎ ﻭﺍﺣﺪﺍ ﺭﺑﺎ ﻭﺷﺎﻫﺪﺍ ﺍﺣﺪﺍ ﻭﺻﻤﺪﺍ ﻭﻧﺤﻦ
ﻟﻪ ﺻﺎﺑﺮﻭﻥ ﻻﺍﻟﻪ ﺍﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﺤﻤﺪ ﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻟﻴﻚ ﻓﻮﺿﺖ ﺍﻣﺮﻱ ﻭﻋﻠﻴﻚ ﺗﻮﻛﻠﺖ ﻳﺎ ﺍﺭﺣﻢ ﺍﻟﺮﺍﺣﻤﻴﻦ
La ilaha illallahul jalilil
jabbar
La ilaha illallahul wahidul
qahhar
La ilaha illallahul karimus
sattar
La ilaha illallahul kabirul muta
Al
La ilaha illallahu wahdahu
lasharika lahu ilahan wahidan warabban washahidan ahdan wasamadan wanahnu lahu
muslimun.
La ilaha illallahu wahdahu
lasharika lahu ilahan wahidan rabban washahidan a hadan wasamadan wanahnu lahu
Abidun
La ilah illahu wahdahu lasharika
lahu ilahan wahidan ahdan wasamadan wanahnu lahu qanitun."
Sowa dan uwanka abinda ka sowa
kanka. Alhamdu lillah.
DAN ALLAH KAMAR YADDA WANI YA
TURO MAKA KAI MA, DAURE KA YADA WA SAURAN AL-UMMAR MUSULMI DAN SU MA, SU
KARANTA, SU SAMU 'DUMBIN LADA. Allah YA SA MU DACE, AMIINNNN.
AMSA❗
Lahaula wala quwwata illa billa
Me yas a mutane suke danganta
abin da bai tabbata daga Annabi Sallallahu alaihi wasallan ne, me yasa wanda
yayi rubutun bai kawo hadisi a karkashin addu'ar ba
Ya manta cewar yin karya ga
Annabi ba kamar yin karya bane ga kowa
Hadisi Sahihi ya tabbata a cikin
al-Bukhari cewar Annabi Sallallahu alaihi wasallam yace: "Duk wanda
yayimin karya da gangan to ya tanadi wajen zamansa a cikin wuta"
Wannan addu'ar gaba daya ba tada
asali a cikin addini, wanine kawai ya zauna yayi typing dinta don wata manufa
tashi
A cikin littafin Hisnul Muslim
akwai sahihan addu'o'in da Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar damu,
wasu daga cikinsu sune;
1) Duk wanda ya karanta;
اَللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ، خَلَقْتَنِي
وَأَنَا عَبْدُك، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ ما اسْتَطَعْت، أَعُوذُبِكَ مِنْ
شَـرِّ مَا صَنَعْتَ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ
عَلَيَّ وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِِرْ لِي فَإِنَّهُ لاَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ
إِلاَّ أَنْتَ .
Allahumma anta rabbee la ilaha
illa ant, khalaqtanee wa-ana 'abduk, wa-ana 'ala 'ahdika wawa'adika
mas-tata'ata, a'oozu bika min sharri ma sana'atu, aboo-o laka bini'matika
'alay, wa-aboo-o bizanbee, faghfir lee fa-innahu la yaghfiruz-zunooba illa
anta.
Ya Allah! Kai ne Ubangijina; babu
abin bautawa da gaskiya sai Kai. Ka halicce ni, kuma ni bawanka ne kuma ina kan
alkawarin da na yi maka (na kadaitaka da bauta) da kuma alkawarin da Ka yi mini
(na shigar da wanda bai yi shira da kai ba gidan aljanna) gwargwadon ikonak ina
neman tsarinka daga sharrin abin da na aikata. Ina tabbatar da ni'imarka gare
ni, kuma ina tabbatar da zunubi na; Ka gafarta mini, domin ba wanda yake
gafarta zunubai sai Kai.
Wanda ya karanta wannan addu'a da
maraice yana mai imani da ita, idan ya mutu a cikin daren zai shiga aljanna,
haka nan ma idan ya karanta ta da safe.
2) Babu wata addu'a da akace idan
kayi zaka samu ladan yan ta bayi 360, addu'ar da ta inganta itace wadda za'a
bala ladan yan ta bayi 10, itace;
لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْكُ
وَلَهُ الْحَمْدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ.
La ilaha illal-lahu wahdahu la
shareeka lah, lahul-mulk, walahul-hamd, wahuwa 'ala kulli shayin qadeer.
Babu abin bautawa da gaskiya sai
Allah Shi kadai, babu abokin tarayya a gare Shi. Mulki naSa Ne Shi Kadai, yabo
ma nasa ne Shi kadai, kuma Shi Mai iko ne bisa komai. (sau dari idan ya wayi
gari).
Wanda ya fada sau dari a rana
kamar ya 'yanta bayi goma ne, kuma za a rubuta masa kyakkyawan aiki dari, a
shafe masa mummunan aiki dari kuma ita addu'ar za ta zamo masa tsari daga
shaidan a tsawon wannan rana har ya kai maraice, kuma ba wanda zai yi aikin da
yafi nasa falala sai wanda ya karanta fiye da haka.
3) Acan yace idan mutum ya
karanta addu'ar Allah zai lamunce masa abubuwa guda 7 wadanda suke da alaqa da
rabuwar talauci, tambayar kabari, kuncin kabari, shiga wuta, mutuwar gatsali,
keta siradi, fushin azzalumin shugaba
Dangane da arziqi, tuni Annabi
Sallallahu alaihi wasallam ya koyar da addu'a kamar haka;
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ عِلْمًا نَافِعًا،وَرِزْقًا طَيِّبًا،وَعَمَلاً
مُتَقَبِّلاً.
Allahumma inni as'aluka 'ilman
nafi'an, wa rizqan tayyiban wa'amalan mutaqabbalan.
Ya Allah! Ina rokan Ka ilimi mai
amfani, da arziki na halal, da aiki karbabbe. (Da safe).
4) Dangane da azabar kabari da
shiga wuta da mutuwar gatsali kuma sai mu ce masa muna addu'a ingantacciya daga
hadisi wadda Annabi Sallallahu alaihi wasallam yake koyarda sahabbansa kamar
yanda yake koyar dasu ayoyin Qur'ani, yace a dinga karantasu bayan Tahiya kafin
sallama, itace;
"Allahumma inni a'uzu bika
min azabil qabr, wamin azabi jahannam, wamin fitnatil mahya walmamat, wamin
fitnatil masihid dajjal"
5) Dangane da addu'ar neman tsari
daga azzalumin shugaba kuwa, Annabi Sallallahu alaihi wasallam ya koyar da
addu'ar kamar haka;
اَللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ، وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ
شُرورِهِمْ .
Allahumma inna naj'aluka fee
nuhoorihim wana'oothu bika min shuroorihim.
Ya Allah! Mu mun sanya ka a
gabansu, kuma muna neman tsarinka daga sharrace-sharracensu.
Ko kuma addu'ar da Annabi Ibrahim
(Alaihis salam) yayi a lokacin da aka jefa shi cikin wuta;
حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ.
Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel.
Allah ne mai isar mana, kuma
madalla da shi abin dogaro.
6) Neman tsari akan komai kuma
akwai addu'ar;
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ مِنْ شَرٍّ مَا خَلَقَ.
A'udhu bi-kalmati l-lahi
t-tammati min sharri ma khalaq.
Ina neman tsari da kalmomin Allah
cikakku daga sharrin abin da ya halitta (sau uku da safe uku da yamma).
Ko kuma;
بِسمِ اللهِ الَّذِي لاَ يَضُرُّ مَعَ اِسْمِهِ شَيْءٌ فِي اْلأَرْضِ
وَلاَ فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السّّمِيعُ الْعَلِيمُ. (ثلاثاً)
Bismil-lahil-lathee la yadurru
ma'as-mihi shay-on fil-ardi wala fis-sama-i wahuwas-samee'ul-'aleem.
Da sunan Allah wanda sunansa wani
abu a sama ko a kasa baya cutarwa. Shine mai Ji Masani. (sau uku).
Wanda ya fada sau uku da safe da
yamma babu abin da zai cutar da shi.
Ko kuma;
حَسْبِيَ اللَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ عَلَيْهِ تَوَكَّلْتُ وَهُوَ
رَبُّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ. (سبع مَرّات)
Hasbiyal-lahu la ilaha illa huwa,
'alayhi tawakkalt, wahuwa rabbul-'arshil-'azeem (7)
Allah ya ishe ni, babu abin
bautawa da gaskiya sai Shi. A gare Shi kadai na dogara, shi ne Ubangijin
al'arshi mai girma (sau bakwai da safe da maraice).
Wanda ya karanta ta kamar yadda
aka ce, Allah zai ishe masa duk abin da ya dame shi na al'amarin duniya da na
lahira.
7) Neman ceton Annabi Sallallahu
alaihi wasallam, sai ka lazumci;
رَضِيتُ بِاللهِ رَبَّاً وَبِالإِسْلاَمِ
دِيناً وَبِمُحَمَّدٍ نَبِيًّا. (ثلاثُ مراتٍ)
Radeetu billahi rabban
wabil-islami deenan wabiMuhammadin nabiyya.
Na yarda da Allah Ubangiji, da
Musulunci addini, da Muhammadu, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
Annabi. (sau uku).
Azkar din suna da yawa. Kuma
sunada falala mai tarin yawa kamar yanda Allah Azzawajallah ya fada;
فَاذْكُرُونِي أَذْكُرْكُمْ وَاشْكُرُواْ لِي وَلاَ تَكْفُرُونِ
Ku ambace ni zan ambace ku, ku
gode mini kada ku butulce mini"
[Bakara, aya ta 152].
Da kuma;
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا اذْكُرُوا اللَّهَ ذِكْراً كَثِيراً
Ya ku wadanda suka yi imani ku
ambaci Allah ambato mai yawa"
(Ahzab aya ta 41)
Kuma Manzon Allah, tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton
Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da
matacce ne"
(Duba Sahihul Bukhari tare da
Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208)
Muslim ya rawaito shi da lafazin;
'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a
cikinsa kamar misalin rayayye ne da matacce". (1/539)
Kuma ya ce: "Shin ba na ba
ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake
mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga
ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan
gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari.
Ya ce: Ambaton Allah Madaukaki"
(Tirmizi (5/459), da Ibn Majah
(2/1245). Duba Sahih Ibn Majah (2/316). Da Sahihul Tirmizi (3/139)
Muna roqon Allah ya rabamu da
yada abinda bai inganta daga AnnabinSa ba. Allah ya tabbatar damu akan daidai
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa
Usman Danliti Mato
(Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.