Ticker

Hukuncin Yin Taimama A Lokacin Sanyi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam shin ya halatta ayi taimama saboda sanyi kuma gashi mutum yana da janaba A jikin shi Saboda mun makara idan muka tsaya dafa ruwan zafi lokaci zai wuce kuma idan nayi amfani da ruwan sanyi zan sani rashin lafiya Saboda ina da lalura ta asthma, ko waje na fita na shaki sanyi sai ciwon ya tashi. Don Haka na samu kasa mai tsarki nayi amfani da ita, Amma da zarar hantsi ya fito nake yin wankan tsarki.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus-Salam. Hakika duk wanda Ya tashi yin Sallah kuma yana ɗauke da Janaba to dole ne sai ya tsarkaka sannan zai yi sallah, Saboda a Cikin Al-qur'ani Allah (Swt) Yana Cewa;

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا قُمْتُمْ إِلَى الصَّلَاةِ فَاغْسِلُوا وُجُوهَكُمْ وَأَيْدِيَكُمْ إِلَى الْمَرَافِقِ وَامْسَحُوا بِرُءُوسِكُمْ وَأَرْجُلَكُمْ إِلَى الْكَعْبَيْنِ ۚ وَإِنْ كُنْتُمْ جُنُبًا فَاطَّهَّرُوا ۚ وَإِنْ كُنْتُمْ مَرْضَىٰ أَوْ عَلَىٰ سَفَرٍ أَوْ جَاءَ أَحَدٌ مِنْكُمْ مِنَ الْغَائِطِ أَوْ لَامَسْتُمُ النِّسَاءَ فَلَمْ تَجِدُوا مَاءً فَتَيَمَّمُوا صَعِيدًا طَيِّبًا فَامْسَحُوا بِوُجُوهِكُمْ وَأَيْدِيكُمْ مِنْهُ ۚ مَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيَجْعَلَ عَلَيْكُمْ مِنْ حَرَجٍ وَلَٰكِنْ يُرِيدُ لِيُطَهِّرَكُمْ وَلِيُتِمَّ نِعْمَتَهُ عَلَيْكُمْ لَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni ! idan kun tãshi zuwa ga salla, to, ku wanke fuskõkinku da hannuwanku zuwa ga magincirõri, kuma ku yi shãfa ga kãnunku, kuma ku (wanke) ƙafãfunku zuwa idãnun sãwu biyu. Kuma idan kun kasance mãsu janaba, to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kõ kuwa a kan tafiya, kõ kuwa ɗaya daga gare ku ya zo daga kishi, kõ kuka yi shãfayyar junã da mãtã, sa´an nan ba ku sãmi ruwa ba to ku yi nufin wuri mai kyau, sa´an nan ku yi shãfa ga fuskõkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bã Ya nufi dõmin Ya sanya wani ƙunci a kanku, kuma amma Yanã nufi dõmin Ya cika ni´imarSa a kanku, tsammãninku kunã gõdewa. (Suratul Ma'ida aya ta 6).

An ruwaito hadisi daga Amr ibn al-Aas (rta) Yace, "Na gamu da matsalar yin Mafarki (kuma har nayi Inzali) a wani dare da ake yin masifar Sanyi kuma a karshen dare, sannan ina jin tsoro akan cewa, idan nayi wankan tsarki zan mutu, saboda haka sai nayi taimama na gabatar da sallar asuba tare da Abokanan tafiyata.

Suka gayawa Annabi Sallallahu alaihi Wasallam abinda ya faru, Sai Ya tambayeni shin ko nayi abinda abokan tafiya ta suka fadi game da Ni a cikin Janaba? Sai na gaya masa abinda ya same ni da dalilina na rashin yin tsarki. Sai na karanta masa faɗin Allah (swt)

 ۚ وَلَا تَقْتُلُوا أَنْفُسَكُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ كَانَ بِكُمْ رَحِيمًا

Kuma kada ku kashe kãnku. Lalle ne Allah Yã kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne. (Suratul Nisa'I aya 29).

Bayan na kammala sai Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yayi murmushi baice komai ba. (Imamu Abu Dawood ne, ya ruwsito shi a hadisi na 334; a cikin saheeh Albaani ya kawo shi a cikin Saheeh Abi Dawood.)

Ibn Hajar (Allah ya jikansa) Yace; "Wannan Hadisi ya yardewa wanda ke tunanin yin Amfani da ruwa zai kashe shi yin taimama, ko saboda Sanyin ruwan ko kuma wani dalili daban, kuma a cikin sa akwai yardewa mutum yayi taimama yayi sallah ga wanda baya iya yin alwala." (A duba a cikin Fatul Baar, 1/454).

Shi kuwa Shaykh ‘Abdul Azeez ibn Baaz (Allah ya jikansa) Cewa yayi, "Idan Har baka iya Daura ruwa ko kuma baka iya saye a makwaftanka a wani wuri zaka iya yin taimama Saboda Allah (Swt) Yace;

فَاتَّقُوا اللَّهَ مَا اسْتَطَعْتُمْ

Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. (Suratul Taghaabun aya ta 16) .

Saboda haka ya halatta Kiyi taimama Idan har babu yanda zaki sami Ruwan dimi.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments