Ticker

Jerin Barkwanci Daga Taskar Amsoshi (Fitowar Disamba 2023)

Barkwanci Daga Taskar Amsoshi
Idan aka lura, ayyukan gida na yi wa mace yawa. Duk namiji mai tausayi zai yi ƙoƙarin samo wa matarsa abokiyar zama 🧕🧕domin tausayawa. 👨‍🦯

Barkwanci Daga Taskar Amsoshi
Abin alfahari ne a gare ki 'yan mata su nuna suna son auren mijinki. Hakan na nuni da cewa kin auri mijin ƙwarai. 👳‍♂️

Barkwanci Daga Taskar Amsoshi
An samu wani hatsabibin mutum mai saka manyan ƙanƙara a randunan masallaci da asuba domin gwada imanin uztazai.😤

Barkwanci Daga Taskar Amsoshi
Daga zuwa hira ƙofar gidansu, sai babanta ya ɗauko Qur'ani, wai na rantse cewa auren ta zan yi.😫 Ni kuwa na ce ba ni da tsarki. 😒

Barkwanci Daga Taskar Amsoshi

Ɗazu ina addu'a a masallaci, ina faɗan laifukana a fili, kawai liman ya je ya ɗauko mini 'yan sanda. 💂‍♂️💂‍♂️😰

Post a Comment

0 Comments