𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum malam Inada tambaya Inada ciki Kusan wata ɗaya sai kwana huɗu da suka wuce sai jini ya zoman kamar na haila Toh a tunani dai may be nasamu miscarriage ne shin zan cigaba da ibada nane koh kuma zan tsaya Har sai ya tafi, Na gode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa rahmatullah.
Mutukar dai kin tabbatar jinin ɓari ne, to wannan ba zai
hanaki sallah ko azumi ba, tunda cikin bai kai abusa masa rai ba, kuma bai fito
da siffar Ɗan
Adam ba. Wato bai wuce gudan jini ba.
Malaman Fiqhu na Mazhabin
Malikiyyah sun tafi akan cewa mace mai ciki tana iya yin haila amma idan cikin
yakai watanni uku kamar yadda yazo acikin littafin "ATTAJU WAL IKLEEL 'ALA
MUKHTASARI KHALEEL" (Juzu'i na ɗaya
shafi na 543). Da kuma AL MISKUL AZFARIY shafi na 160.
To amma naki bai kai watanni uku ɗin ba, don haka jinin
rashin lafiya ne, mutukar dai kin tabbatar kina da cikin to wannan alamar ɓarewarsa ne.
Duk da cewa Malamai sunyi saɓani game da hukuncin jinin ɓarin da bai kai watanni uku
ba, to amma wannan ita ce fatawar da tafi Qarfi. Wato za'a ɗauki wannan jinin amatsayin
jinin Istihadha kenan.
Kuma Matar dake cikin jinin
rashin lafiya, hukuncinta kamar hukincin mai yoyon fitsari ne. Idan lokacin
sallah yayi zaki je ki wanke jikinki sannan ki canza Kunzugu kiyi alwala kiyi
sallah.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.