𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Aslm Mlm Barka Da Asuba Dan Allah Menene Haramcin Kwanciya Ruff Da Ciki Da Kuma Illolinta Inajin Ana Cewa Babu Kyau Toh Bansan Wata Ingantaciyar Magana Ba Akai, Gashi Ni Na Saba Da Yi, Indai Banyi Ba Bana Iya Bacci.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam warahamtullahi
Wabarkatuh
Kwanciya Rub-Da-Ciki Itace
Kwanciyar Da Ake Kwantawa Akan Ciki Fuska Na Kallon Ƙasa, Yayin da Bayan Mutum
Ke Kallon Sama. Wannan Kwanciya Haramun Ce a Musulunce Saboda Hani da Manzon
Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya yi Game da Ita. Hadisi Ya Tabbata Daga
Abi-Hurairah (ra) Yana Cewa
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِي اللّهُ عَنهُ قَالَ: رَأَى رَسُولُ اللَّهِ
صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلًا مُضْطَجِعًا عَلَى بَطْنِهِ فَقَالَ: {إِنَّ
هَذِهِ ضِجْعَةٌ لَا يُحِبُّهَا اللَّهُ}*)
(رواه الترمذي)
An Karɓo Daga Abi-Hurairah (ra) Ya ce: Lallai Manzon
Allah Sallallahu alaihi Wasallam Yaga Wani Mutum Kwance Akan Cikinsa, Sai Ya ce
Dashi: “Lallai Wannan Kwanciya Ce Da Allah Baya Sonta”.
(Tirmizi Ya Ruwaitoshi)
Har Ila Yau Hadisi Ya Tabbata
Daga Abi-Zarrin (ra) Game da Hani Akan Wannan Kwanciya.
عَنْ أَبِي ذَرٍّ قَالَ رَضِي اللّهُ عَنهُ فَال: مَرَّ بِيَ النَّبِيُّ
صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَأَنَا مُضْطَجِعٌ عَلَى بَطْنِي، فَرَكَضَنِي بِرِجْلِهِ
وَقَالَ: (إِنَّمَا هَذِهِ ضِجْعَةُ أَهْلِ النَّارِ)
(رواه إبن ماجه)
An Karɓo Daga Abi-Zarrin (ra) Ya ce: Manzon Allah
Sallallahu alaihi Wasallam Ya Wuceni Ina Kwance Akan Cikina, Sai Ya Shureni Da Ƙafarsa
Sannan Ya ce: “Wannan
Kwanciya Ce Ta Ƴan Wuta”.
(Ibn Majah Ya Ruwaitoshi)
Duk Lokacin da Mutum Zai Kwanta
Bacci Bashi da Tabbacin Ubangiji Zai Dawo Masa da Ransa Ya Cigaba da Rayuwa. Ya
Kai Ɗan'uwa
Shin Zakaso Ubangiji Ya Amshi Ranka Kana Cikin Yin Abinda Bayaso?
Idan Bazakaso Hakan Ba, To Ka
Kiyayi Kwanciya Rub-Da-Ciki Yayin da Zakayi Bacci Domin a Cikin Baccin Allah
Yana Iya Amsan Abinsa.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.