Ticker

Lemon Kwakwa Da Madara, Lemon Karas, Lemon Ayaba, Lemon Zobo, Lemon Rake, Lemon Magarya, Lemon Inibi, Lemon Gwaiba, Lemon Kankana

A wannan rubutu, an kawo bayani game da yadda ake sarrafa Lemon Kwakwa Da Madara da Lemon Karas da Lemon Ayaba da Lemon Zobo da Lemon Rake da Lemon Magarya da Lemon Inibi da Lemon Gwaiba da Lemon Kankana.

Lemon Kwakwa

Kayan haɗi:

i. Filebo na kwakwa

ii. Kwakwa

iii. Madara

iv. Ruwa

v. Suga

Shi ma wannan  nau’in lemo bai bambanta da sauran ba wurin sarrafawa. Bambancin kawai shi ne na kayan ha ɗ i. Nau’in filebon da aka fi so a sanya shi ne filebon kwakwa .

Lemon Kwakwa da Madara

Kayan haɗi:

i. Kayan yaji

ii. Kwakwa

iii. Madara

iv. Ruwa

v. Suga ko zuma

Yayin samar da wannan  nau’in lemo, za a marka ɗ a kwakwa  sannan a dafa ta cikin tukunya . Bayan ta dafu , s a i a sauke a sanya kayan ƙ amshi sannan a tace. Daga nan za a zuba madara a ƙ ara suga ko zuma.

Lemon Karas

Kayan haɗi:

i. Filebo

ii. Karas

iii. Kayan ƙamshi

iv. Madara

v. Ruwa

vi. Suga ko zuma

A nan kuwa, za a kankare karas ne a wanke  sannan a yayyanka a kuma marka ɗ a. Za kuma a ƙ ara masa kayan ƙ amshi sannan a tace. Daga nan sai a sanya filebo da suga ko zuma.

Lemon Ayaba

Kayan haɗi:

i. Ayaba         

ii. Kankana                

 iii. Kayan ƙamshi      

 iv. Madara

v. Ruwa          

vi. Sitiroberi                

vii. Suga ko Zuma

Za a yanka ayaba sannan a marka ɗ a. A gefe guda kuma za a yanka kankana a fitar da bayan (ana iya cire ’ya’yan ko a bar su haka nan) ita ma a marka ɗ a. Za kuma a marka ɗ a sitiroberi. Sai a sanya kayan ƙ amshi sannan a tace su. Ana sanya suga ko zuma cikin irin wannan  nau’in lem o .

Lemon Zoɓo

Kayan haɗi:

i. Abarba                                 

ii. Citta

iii. Filebo na Abarba              

iv. Kayan ƙ amshi

v. Kukumba                           

vi. Ruwa

vii. Suga ko zuma                   

viii. Ɓ awon abarba                

ix. Zoɓo

Za a wanke  zo ɓ o a sanya a cikin tukunyar da aka ɗ ora kan wuta , sannan a sanya citta da kanamfari a ciki. S a i a bar shi ya yi ta tafasa. Za a marka ɗ a ɓ awon abarba sannan a sanya cikin ruwan da ke tafasa. Za kuma a marka ɗ a abarba da citta da kukumba. Bayan an sauke ruwan da ke tafasa sai a sanya wa ɗ annan kayayyaki da aka marka ɗ a a kuma ƙ ara kayan ƙ amshi. Daga nan sai a tace ruwa n sannan a sanya filebo. Ana shan irin wannan  lemo da suga ko zuma.

Lemon Gwaiba

Kayan haɗi:

i. Gwaiba

ii. Kayan ƙamshi

iii. Madarar ruwa

iv. Ruwa

v. Suga

Wannan nau’in lemo kuwa da gwaiba ake yi. Za a yayyanka ta sannan a marka ɗ e. Daga nan za a sanya kayan ƙ amshi a kuma tace ta.                       

Lemon Kankana

Kayan haɗi:

i. Kankana

ii. Kayan ƙamshi

iii. Ruwa

iv. Suga

v. Zuma

Yadda ake l e m o n gwaiba haka ake yin na kankana, bambancin su kawai shi ne, a nan ana amfani ne da kankana ba gwaiba ba.

Lemon Inibi

Kayan haɗi:

i. Inibi

ii. Kayan ƙamshi

iii. Na’a-Na’a

iv. Ruwa

v. Suga ko Zuma

Za a marka ɗ a inibi a ajiye gefe guda. Ita kuwa na’a-na’a tafasa ta ake yi. Daga nan s a i a ha ɗ a su gaba ɗ aya tare da kayan ƙ amshi a tace. Ana shan irin wannan  nau’in lemo da suga ko zuma.

Lemon Magarya

Kayan haɗi:

i. Kayan Ƙamshi

ii. Lemon Zaƙi

iii. Magarya

iv. Ruwa

v. Zuma Ko Suga

Za a samu ɗ any ar magarya a wanke  a marka ɗ a , s annan s a i a marka ɗ a lemon za ƙ i. Za a ha ɗ e su gaba ɗ aya tare da kayan ƙ amshi a tace. Ana shan irin wannan  nau’in lemo da suga ko zuma.

Lemon Rake

Kayan haɗi:

i. Filebo

ii. Rake

iii. Ruwa

iv. Suga

Za a fere  rake a yanka shi ƙ anana - ƙ anana sannan a marka ɗ a. Daga nan sai a a tace sannan a ƙ ara masa filebo. Idan an ga dama ana iya ƙ ara suga ko zuma. 

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments