Ticker

Matsala Da Dangin Miji

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ina da matsala da dangin mijina, suna zargin wai na mallake ɗan’uwansu, har abin ya kai ba ma magana da su. To, ko ya halatta in nemi ya sake ni don kauce wa ƙiyayyarsu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Samun matsala da dangin miji ba shi daga cikin dalilan da suke halatta miki neman saki, domin ai ba su ke auren ki ba.

Mallake miji kuma abu ne mai kyau matuƙar dai kin yi shi ta hanyoyi na halal ne, ba na haram ba.

Hanyoyin mallake miji na halal sun haɗa da: Gyara abinci, iya kwalliya, sakin fuska da murmushi, kare masa kanki da gidansa da dukiyarsa, mutunta iyayensa da danginsa da sauran iyalinsa, zama cikin shirin biya masa buƙatarsa a sadda da yadda ya ke so, bisa dacewa da Sharia, da sauransu.

Amma hanyoyin da wasu mata ke bi don mallake miji a zamanin yau, kamar ta zuwa wurin bokaye ko amfani da magungunan da suke kira maganin mata, wannan kam haram ne, domin sihiri ne, shi kuma kafirci ne. Allaah ya kiyaye.

(Dubi littafin Maganin Mata da na rubuta a kan haka).

Hanyar da ta dace ki bi don warware wannan matsalar in shaa’al Laah ita ce

(i) Yawaita bayar da kyauta da alheri gare su da gwargwadon ikonki da ƙarfinki. Kina iya roƙon mijinki don ya taimaka miki a kan haka, idan ba ki da ƙarfi.

(ii) Idan wannan bai ci ba, sai ki sanar da mijinki halin da ake ciki don ya taimaka miki a warware matsalar, don shi ya fi ki sanin danginsa.

(iii) Idan wannan bai biya buƙata ba, sai ki kai maganar ga manyansa, waɗanda su ke jagorori a gidan, don su taimaka.

(iv) Idan duk wannan bai samar da mafita ba, kina iya ɗaukar maganar zuwa ga manyanki domin su zauna da manyan gidan mijinki a kan matsalar.

(v) Idan hakan bai samar da mafita ba to, in shaa’al Laahu Alƙalin kotun musulunci a inda ku ke ba zai rasa abin yi ba don taimaka miki.

Amma dai kafin a kai ga duk wannan, hanya mafi kyau ita ce yin haƙuri da juriya, tare da yawaita sadar da alheri gare su, musamman a lokacin da suka munana miki. Allaah Taaala ya ce

 وَلَا تَسۡتَوِی ٱلۡحَسَنَةُ وَلَا ٱلسَّیِّئَةُۚ ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِی هِیَ أَحۡسَنُ فَإِذَا ٱلَّذِی بَیۡنَكَ وَبَیۡنَهُۥ عَدَ ٰ⁠وَةࣱ كَأَنَّهُۥ وَلِیٌّ حَمِیمࣱ  ٤٣۝ وَمَا یُلَقَّىٰهَاۤ إِلَّا ٱلَّذِینَ صَبَرُوا۟ وَمَا یُلَقَّىٰهَاۤ إِلَّا ذُو حَظٍّ عَظِیمࣲ  ٥٣۝

Kyakkyawan aiki ba ya yin daidai da mummunan aiki. Ka tunkuɗe mummunan da wanda yake shi ne kyakkyawa, sai ka ga wanda ya ke akwai gaba a tsakanin kai da shi ya koma kamar wani majibinci mai matuƙar ƙauna. Amma babu mai samun wannan sai waɗanda suka yi haƙuri, kuma babu mai samun sa sai wanda ke da rabo mai girma.

(Surah Fussilat: 34-35)

Allaah ya shirye mu tare da su, kuma ya sa duk mu iya jurewa a kan bin dokokinsa.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy,

08164363661

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JoWs3feDfdyGE9yBsa1RSC

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments