Ticker

6/recent/ticker-posts

Mauludi A Littafin Ibn Taymiyah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Wani malamin Sunnah ya ce: Ibn Taymiyyah shi kansa ya rubuta cewa, kodayake mauludi bidi’a ne, amma waɗanda suka yi za su iya samun ladan kyakkyawan niyyarsu ta son Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Daga baya ne aka cire wannan daga cikin sabon bugun littafin! To, wai wannan maganar kuskure ne, ko kuwa da gaske akwai nuskhar da ke ɗauke da hakan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Ramatul Laah

[1] To ai malamin bai faɗi sunan littafin da Shakhul Islaam Ibn Taymiyah (Rahimahul Laah) ɗin ya faɗi hakan a cikinsa ba, balle a iya komawa gare shi don tantancewa.

[2] Dole ne a nan a san cewa, su fa Ahlus Sunnah na gaskiya ba Ibn Taymiyah ko wani malami suke bi ba. Al-Kitaab Was Sunnah suke bi, a bisa fahimtar Sahabbai da Taabi’ai da waɗanda suka bi hanyarsu da kyautatawa. Sai kuma maganganun gaskiya da suka dace da waɗannan tushen ko asullan guda uku. Allaah ya ce

{ وَمَنْ يُشَاقِقِ الرَّسُولَ مِنْ بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُ الْهُدَى وَيَتَّبِعْ غَيْرَ سَبِيلِ الْمُؤْمِنِينَ نُوَلِّهِ مَا تَوَلَّى وَنُصْلِهِ جَهَنَّمَ وَسَاءَتْ مَصِيرًا }

Kuma duk wanda ya saɓa wa Manzon nan daga bayan shiriya ta bayyana a gare shi, kuma ya bi hanyar da ba ta muminai ba, za mu bari shi da abin da ya ɗora wa kansa, kuma mu ƙona shi a cikin Jahannama, kuma ya munana da zama makoma. (Surah An-Nisaa: 115).

Don haka, bin hanyar muminai, waɗanda su ne Sahabbai da waɗanda su ke a kan tafarkinsu ita ce hanyar kariya daga shiga Wutar Jahannama a Lahira.

[3] Sannan malaman Sunnah sun yarda cewa, in ban da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) kowane malami ana samun inda ya yi daidai a cikin maganganunsa, akwai kuma inda yake yin ba daidai ba. An san wannan daga shahararriyar maganar Al-Imaam Maalik (Rahimahul Laah).

[4] Amma maganar cewa kyakkyawar niyyah tana iya samar wa musulmi da lada a kan wani mummunan aikin da ya aikata, wannan daidai ne matuƙar dai ya aikata hakan a bisa jahilci karɓaɓɓe ne ko mantuwa ko kuskure ko tilasci da makamantan hakan. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« إِنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ عَنْ أُمَّتِى الْخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ ».

Haƙiƙa! Allaah ya yafe wa alummata kuskure da mantuwa da abin da aka tilasta ta a kansa. (Sahih Al-Jaami: 1731).

[5] Sai dai kuma wannan bai mayar da abin da ya aikatan halattacce ga al’umma ba a shari’a. Kamar misali, idan wani ya sha giya a bisa jahilci ko mantuwa ko kuskure ko tilasci duk malamai sun yarda cewa ba shi da laifi. Kai! Yana ma iya samun lada idan tun farko ya yi da kyakkyawar manufa ce, kamar neman ƙarin kuzarin yi wa Allaah ibada, misali! To, amma idan wani malami ne ya aikata hakan za a iya cewa, wannan ya mayar da shan giya ya zama halal kenan? Sam! Sannan kuma sam!!

[6] Kamar haka ne: Idan da wani malami zai aikata wani aikin bidi’a a bisa jahilci ko kuskure ko mantuwa ko zamiya ko tilasci, ba za a ce ya zama mai laifi abin zargi ba har ga Allaah. Amma kuma wannan bai sauya hukuncin aikin daga bidi’a abin ƙyama ga alumma zuwa ga Sunnah kyakkyawa abin ƙauna ba.

[7] Magana a kan cewa bikin mauludi bidi’a ne abu ne sananne tabbatacce a wurin dukkan malamai, ba wai a wurin waɗanda ba su yi ba kaɗai. Har da su kansu masu aikatawa ma sun yarda da hakan. Abin da suka kafe a kansa kawai shi ne, wai bidi’a ne kyakkyawa! Kamar yadda wani Muhammad Alawiy Maaliky ya bayyana a cikin littafinsa mai suna: Haulal Ihtifaal Bil Mailudin Nabawiyis Shareef, wanda kuma Fadeelatus Shaikhul Allaamah Abdullaah Bn Sulaiman Bn Manee’ (Allaah ya biya shi da alkhairi) ya mayar wa da kyakkyawan martani a cikin littafinsa: Hiwaar Ma’al Maalikiy Fee Raddi Munkaraatihi Wa Dalaalaatih.

[8] To, amma tabbatar da cewa aiki kaza bidi’a ne kuma a lokaci guda kyakkyawa ne, wani abu ne mai wahala matuƙa, in ji malamai muhaƙƙiƙai. Domin kamar yadda Al-Imaam Maalik (Alaihi Rahmatul Laah) ya faɗa

مَنِ ابْتَدَعَ فِي الْإسْلَامِ بِدْعَةً يَرَاهَا حَسَنَةً، فَقَدْ زَعَمَ أَنَّ مُحَمَّدًا - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ - خَانَ الرِّسَالَةَ؛ لِأَنَّ اللَّهَ يَقُولُ: { الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ لَكُمْ دِينَكُمْ }، فَمَا لَمْ يَكُنْ يَوْمَئِذٍ دِينًا، فَلَا يَكُونُ الْيَوْمَ دِينًا.

Duk wanda ya ƙirƙiro wata bidia a cikin musulunci wacce yake ganin ta kyakkyawa ce, to haƙiƙa ya riya ne cewa: Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya hainci saƙon manzanci! Domin dai Allaah ya ce: {A yau na kammala muku addininku}. Don haka, duk abin da bai zama addini ba a waccan ranar, to kuwa ba zai zama addini ba a yau. (As-Shaatabiy a cikin Al-Itisaam (1/65) ya kawo shi, kuma Ibn Hazm a cikin Al-Ihkaam (6/225) ya riwaito shi da isnadinsa sahihi).

Tun da yadda bidi’a ta ke kenan, to ta yaya kuma zai yiwu ta zama kyakkyawan abu abin yabo a wurin musulmi?!

[9] Sannan kuma kusan a kowace Jumma’a sai Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya maimaita faɗin

« وَكُلَّ مُحْدَثَةٍ بِدْعَةٌ وَكُلَّ بِدْعَةٍ ضَلاَلَةٌ »

Kuma kowace ƙirƙira bidia ce, kuma kowace bidia ɓata ce! (Sahih Muslim: 2042, Sahih An-Nasaa’iy: 1589)

Ba a taɓa samun ko sau ɗaya ya rage wa wannan maganar faɗi ba, kamar ya ce: ‘… sai dai bidi’a kaza da kaza ita ba ɓata ba ce!’ Ko dai wata kalma makamanciyar hakan.

[10] Kodayake gaskiya ne an samu waɗansu malamai sun faɗi cewa bidi’ar tana iya karkasuwa gida-gida, amma kuma kamar yadda ya gabata daga Al-Imaam Maalik (Rahimahul Laah) shi ya ce

كُلُّ أَحَدٍ يُؤْخَذُ مِنْ قَوْلِه، وَيُتْرَكُ، إِلاَّ صَاحِبَ هَذَا القَبْرِ - صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ-

Kowane mutum ana samun na karɓe daga maganganunsa kuma ana samun na bari, sai dai ma’abucin wannan ƙabarin (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). (Siyaru Alaamin Nubalaa: 8/93).

A wani lafazin kuma ya ce

ما منا إلا من رد أو رد عليه إلا صاحب هذا القبر " وأشار إلى قبر النبي صلى الله عليه وسلم،

Babu wani mutum a cikinmu face ya yi martani kuma shi ma an yi masa martani, sai dai ma’abucin wannan ƙabarin. Sai ya nuna ƙabarin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). (Siyaru Alaamin Nubalaa: 10/73).

Allaah ya faɗakar da mu.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734'

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments