Ticker

Mijina Ba Ya Son Haihuwa, Yana Tilasta Mini Zubar Da Ciki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalmu alaikum malam ina da tambaya, ni ce muke tare da mijina muna zaman lafiya amma ya ce mun ba ya son haihuwa, in na samu ciki sai ya sani dole na zubar, in na ki sai ya ba ni wani abu in sha ban sani ba, sai cikin ya zube, malam meye hukuncina a wurin Ubangijina?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salamu, ƴar uwa lallai Allah ba ya hukunta wata rai da laifin da wata rai ta aikata, saboda yin hakan zalunci ne, shi ko Allah ba ya zalunci, kamar yadda ya hana a yi zalunci. Duk wani laifi da aka tilasta wa mutum ya yi shi, to idan ya yi wannan laifi saboda an fi qarfinsa, to Allah ba zai kama shi da laifin wannan aiki ba, saboda hadisin da Abu Zharril Gifáriy ya ruwaito cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: "Lallai Allah ya share wa al'ummata abin da suka yi da kuskure, da abin da suka yi da mantuwa, da abin da aka tilasta masu yin sa". Ibn Majah 2043.

Lallai shi mijin ne za a ɗora wa laifin, musamman ma idan cikin ya kai watanni huɗu an hura masa rai.

Zubar da ciki don tsoron talauci yana daga cikin manyan zunubai domin shima kisan kai ne. In dai cikin yakai wata huɗu zuwa sama. Idan cikin yakai wata huɗu to sannan an riga an busa masa rai. Idan an zubar dashi da gangan, sai an biya diyyah zuwa ga Waliyyan jaririn (wato dangin Ubansa).

Diyyar jariri shine kwatankwacin Rakuma guda biyar. Wato Ushurin diyyar Mace kenan. Kuma bayan haka za'a 'yantar da Kuyanga guda, idan babu kuyangar sai ayi azumi Sittin amatsayin kaffara.

Duk wanda suke da hannu cikin kashe jaririn duk zasu haɗu su biya diyyar. Kuma kowannensu sai ya 'Yanta Kunyanga ko kuma yayi azumi Sittin. Hujjah anan ita ce Hadisin nan na 6910 acikin Sahihul Bukhariy, kuma na 1681 acikin Sahihu Muslim. Duk sun ruwaito Hukuncin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya yanke ma matar data kwada ma wata Mai juna biyu dutse wanda yayi sanadiyyar mutuwarta da kuma jaririnta.

Amma idan cikin bai kai wata huɗu da samuwa ba, To babu diyya ko kaffara amma duk da haka dai Zunubi ne mai girma. Don Qarin bayani aduba cikin MATALIBU ULIN NUHAA (juzu'i na 6 shafi na 50).

Baya halasta a zubar da ciki bayan ya cika wata huɗu, zubar da shi a bayan ya kai wata huɗu kisan rai ne, saboda a lokacin an riga an hura masa rai, kamar yadda Bukhariy ya ruwaito a hadisi mai lamba ta 3208, Muslim kuma a hadisi mai lamba ta 2643.

Allah ne mafi sani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments